CEDEAO Archives - Arewa Agenda Hausa

Gwamnatin Najeriya na Dab da Kawo Ƙarshen Hare-Haren Ta’addanci a Arewacin Ƙasar – Malam Garba Shehu
Gwamnatin Najeriya na Dab da Kawo Ƙarshen Hare-Haren Ta’addanci a Arewacin Ƙasar – Malam Garba Shehu

Gwamnatin Najeriya ta ce tana tana dab da kawo karshen hare-haren ta’addanci a Arewacin kasar.

Mai baiwa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari shawara kan yada kabarai Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa za a hada hannu da masu ruwa da tsaki a ciki da wajen kasar don shawo kan matsalar tsaron.

Dama yau Lahadi ne ake soma taron shugabanin kungiyar ECOWAS ko kuma CEDEAO karo na 60 a Abuja.

Wannan taro zai gudana ne a daidai lokacin da yawancin kasashen na yammacin Afrika ke cikin wani yanayi na tsananin rashin tsaro, lura da yadda kungiyoyin tada kayar baya da sauran ‘yan bindiga suka addabe su.

A ‘yan kwanakin nan mahara sun kona matafiya sama da 20 a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya, kuma kafin nan wasu maharan sun kona wasu matafiyan da ke hanyarsu ta zuwa cin kasuwa a tsakiyar Mali.

Lamarin ya kara tada hankalin al’umma tare da haifar da ce-ce-ku-ce, inda ake zargin hukumomin kasashen da nuna gazawa.

A cewar Malam Shehu Garba, mataimaki na musamman ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan yada labarai, taron ya zo a dai-dai lokacin da ya dace, lura da tarin kalubala da ECOWAS ke fuskanta a kasashe daban-daban.

” Taro ne a kan gaba. Kowa ya san halin da demokradiyya ta tsinci kanta a kasashen Mali da Guinea. Ga kuma batun rashin tsaro, don ECOWAS ta fahimci cewa ‘yan tada kayar baya ketarawa suke yi iyakokin makwabtan kasashe, saboda haka babu wata kasa da za ta ware kanta ta yi wannan yaki. Dole ne a hadu a yi yaki tare,” in ji Garba Shehu.

Kan karuwar hare-hare da satar jama’a a Arewacin Najeriya, Malam Garba Shehu ya ce, ” Shugaban kasa ya tura wakilci na musamman na masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaron kasa musamman samar da bayanan sirri, kuma sun je sun tattauna da wakilai a matakin kananan hukumomi da jihohi sun dawo masa da rahoto, kuma za a ga abin da zai biyo baya.”

Kazalika ya ce a matakin kasa da kasa, taron na ECOWAS ko kuma CEDEAO zai ba da tasa gudummuwa wurin kawo karshen hare-hare a Arewacin Najeriyar.

” Wannan batu yana daya daga cikin ajanda da Shugabanni za su tattauna. Abu ne da ya damu kowa, ba a jin dadi, kuma babu wani Shugaban kasa da za a ce hankalinsa ya kwanta da wannan fitina da ake fama da ita. Saboda haka za a dauki mataki nan ba da jimawa ba za a kawo karshen hare-hare a arewacin Najeriya din-din-din.” In ji Garba Shehu.

A farkon mako kungiyar bincike kan sha’anin tsaro a Najeriya ta Beacon Consultants ta fitar da rahoton da ke cewa mahara sun kashe mutum sama da 400 a watan Nuwamba da ya gabata a arewacin Najeriyar.

Baya ga wannan rahoton ya ce sace-sacen jama’a ya karu a yankin da kusan kashi 40 cikin 100, duk da ya ce matakan dakile hare-haren na aiki a wasu yankunan kasar.

The post Gwamnatin Najeriya na Dab da Kawo Ƙarshen Hare-Haren Ta’addanci a Arewacin Ƙasar – Malam Garba Shehu appeared first on Arewa Agenda Hausa.