Facebook Archives - Arewa Agenda Hausa

Kamfanin Meta Zai Sake Korar Ma’aikata 10,000
Kamfanin Meta Zai Sake Korar Ma’aikata 10,000

Kamfanin Meta wanda shi ne ya mallaki shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram da kuma WhatsApp, ya sanar cewa zai sake korar ma’aikata dubu goma.

Wannan shi ne karo na biyu da kamfanin ke ɗaukar matakin korar ma’aikata da dama a baya-baya nan.

Wakiliyar BBC ta ce kamfanin Meta ya kori ma’aikata dubu goma sha ɗaya a cikin watanni huɗu da suka gabata, inda a yanzu ya sanar cewa zai sake sallamar dubban ma’aikatan sauran manyan kamfanoni fasaha irinsu Amazon da Microsoft suma sun kori dubban ma’aikata.

Kamfanoni fasaha sun samu matukar ci gaba a lokacin kullen annobar corona. Sai dai fargabar da aka nuna akan durkushewar tattalin arzikn duniya ta sa mutane sun rage amfani da kayayakin fasaha abinda ya sa kamfanonin suka dauki matakin korar ma’aikata.

The post Kamfanin Meta Zai Sake Korar Ma’aikata 10,000 appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Sunayen kamfanoni 5 da Mark Zuckerberg ya Mallaka
Sunayen kamfanoni 5 da Mark Zuckerberg ya Mallaka

Bayan shekaru 17, hamshakin attajirin dan kasuwan nan na kasar Amurka, Mark Zuckerberg ya canza sunan kamfaninsa na sada zumunta na Facebook zuwa Meta.

Canjin, Mark ya bayyana, an yi shi ne don nuna hangen nesa na kamfanin da abin da yake nufi. Sai dai, ba shine karo na farko ko na biyu da zai canza suna ba, kuma abin sha’awa shine, akwai wasu kamfanoni da Meta ya mallaka.

A cikin wannan rahoton, Legit.ng ta yi tsokaci kan kamfanoni 5 da Mark Zuckerberg da kamfaninsa Meta suka mallaka wadanda suke da girman daraja a kasuwa.

Abin lura ne cewa Meta ya mallaki kamfanoni sama da 10 a karkashinsa.

Ga biyar daga ciki:

1. Beluga

Beluga, manhajar aika sako ce, da watakila za ta iya hamayya da manhajar aike da sako ta Meta idan ba da ba saye ta ba.

Meta ne ya sayi Beluga a ranar 2 ga Maris, 2011, akan kudin da ba a bayyana ba. Shekara guda kenan da kafa ta.

A wancan lokacin Beluga ta kasance tana gudanar da shirin tattara kudade na adadin da ba a bayyana ba. Zai ci gaba da kasancewa daya daga cikin nasarorin da Meta ya samu.

2. Onavo Investopedia ya kiyasta cewa kudin da aka sayi Onavo ya kai tsakanin dala miliyan 100-200.

An kafa kamfanin na nazarin gidajen yanar gizon wayar hannu mallakar Isra’ila a shekakar 2010 kuma kamfanin Mark na Meta ya samu nasarar saye shi a Oktoba 2013.

Daga baya an cire dandalin daga shagunan sauke manhajojin iOS da Android bayan fuskantar kakkausar suka kamar yadda mutane da yawa suka sanya shi a matsayin manhajar leken asiri.

3. Oculus VR

An saye shi a ranar 25 ga Maris, 2014, Oculus VR kaya ne na fasahar hange da butun-butumi da aka fi sani da ‘Virtual Reality’ da kamfanin Meta ya saye bayan saye manhajar sakonni ta WhatsApp.

An kiyasta kudin sayansa akan dala biliyan 2.0. Tun lokacin siyansa, Oculus VR ya taka rawa cikin sauri a cikin kasuwar ‘Virtual Reality’.

4. WhatsApp

Manhajar WhatsApp na daga cikin garabasar da Meta ta yi nasarar sayewa. Mark ya sayi WhatsApp ne a ranar 19 ga Fabrairu, 2014, kan makudan kudin da suka kai dala biliyan 19.0.

Dandalin na aike da sakon wayar hannu wanda aka kafa a shekarar 2009 zabi ne mai rahusa ga manhajojin aike da sakon rubutu.

An yi imanin cewa da WhatsApp ya kasance babban abokin hamayyar Meta idan da bai saye shi ba.

5. Instagram

Manhajar yada hoto da bidiyo, Instagram wani babban garabasa ne da Meta ta samu. Meta ta sayi Instagram akan kudi dala biliyan 1.0 a ranar 9 ga Afrilu, 2012.

Domin ginawa da habaka dandamali da kansa, Instagram gudana ne shi kadai daban da Meta.

Wasu masana sun kiyasta cewa Instagram yana samar da karin kudaden shiga.

The post Sunayen kamfanoni 5 da Mark Zuckerberg ya Mallaka appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Abubuwa Game da Sakonnin da yake Yaɗawa Akan Manhajar WhatsApp
Abubuwa Game da Sakonnin da yake Yaɗawa Akan Manhajar WhatsApp

A kwanan nan duk mai amfani da dandalin sada zumunta na Whatsapp to ya gamu da ɗaya daga cikin waɗannan sakonnin da zami bayani a kai.

Mutane na ta kokarin turawa abokanan su sakonnin duk da cewa basu da hujjar kare kansu cewa dokokin daga WhatsApp suke.

A wannan rubutun mun tattara muku dukkanin waɗannan jita-jita da ake yaɗawa tare da bayani mai gamsarwa kan gaskiyar lamarin.

Abuja – Duk mai bibiyar kafafen sada zumunta na Facebook, Instagram da WhatsApp, ya san cewa makon da ya gabata bai zo wa mamallakinsu, Mark Zuckerberg, da daɗi ba.

Ya rasa dala biliyan $5.9bn wanda a jimlace yakai dala biliyan $117bn a makon da ya gabata saboda matsin lambar da yake fama da ita a ɓangaren gudanarwa da kuma ɗaukewar manhajojin kamfaninsa.

A rahoton dailytrust, lamarin ya shafi yardar da masu zuba hannun jari suka wa kamfanin, inda suka rage kusan kashi 4.8% kuma suka kwashe makudan kudi daga dukiyarsa.

Dandalin Facebook kaɗai ya samu matsaloli biyu; ɗaukewar da ya yi tare da ƙawayensa Instagram da WhatsApp, abinda ya jawo asarar miliyoyin daloli.

Damuwa ta biyu kuma itace babban taron da tsohuwar manajan Facebook, Frances Haugen, ta yi ranar Talata bayan ta ɗauki matakin murabus da kuma fallasa wasu bayanai.

Haugen ta caccaki Facebook bisa , “Fifita ribar da zai samu kan mutane,” da kuma gazawa wajen tsare bayanai bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2020 a Amurka.

Sakonnin da ake yaɗawa a WhatsApp

Duk wannan abubuwan ba su kare ba, a halin yanzun dandalin WhatsApp ke fama da yaudara kala daban-daban.

Wasu daga cikin waɗannan yaudara da kuma damfara wauta ce kawai, amma wasu kuma sun jefa masu amfani da shafin cikin tantama.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasu daga cikin waɗannan jita-jitar da ake yaɗawa na yaudara, waɗanda zaku kiyaye:

1. Za’a rufe WahtsApp da karfe 6:00 na yamma

Abu na farko daga cikin jerangiyar sakonnin da mutane ke yaɗawa a Whatsapp shine kamar haka:

“Gobe da misalin ƙarfe 6:00 na yamma zasu garƙame manhajar WhatsApp kuma saika biya zaka ƙara amfani da shi, wannan doka ce.”

“Muna sanar da duk masu amfani da manhajar mu, mun samu matsalan Na’ura, muna son ku taimake mu wajen isar da wannan sakon ga kowa da kowa.

Idan baka tura wannan sakon ga dukkan abokanka ba to zamu fara cajin ka kuɗaɗe.”

“Zamu rufe shafinka kuma zaka iya rasa dukkan abokanan ka, sako daga Jim Balsamic (shugaban WhatsApp). Muna bukatar kowa ya tura wannan sakon, idan ba haka ba zamu rufe shafinka cikin awanni 48.”

Sakon ya cigaba da cewa idan muka rufe maka shafi to zamu ƙara dala £25 a kuɗin da zaka rinka biya duk wata. “Muna sane da matsalar da kuke fuskanta wajen canza hoto, muna aiki ba dare ba rana domin warware matsalar, kuma zamu gyara ta cikin kankanin lokaci. Mungode da haɗin kan da kuke bamu, daga Whatsapp.”

Jita-jitar ta nuna cewa wai WhatsApp zai fara cajin mutane kudi saboda mutane sun yi musu yawa, babu ta hanyar da wannan maganar zata zama gaskiya WhatsApp yace ba zai goge shafin mutun ba dan kawai mutane sun yiwa manhajar yawa kuma ba tare da izinin mutum ba.

2. Daftarin biyan kudin manhajar WhatsApp

Bamu sani ba ko ka taba samun gayyata daga wani? idan ma sakon bai isa gareka ba, tuni wasu suka fara tura daftarin Gold ga masu amfani da dandalin.

Abinda ya kamata kusani WhatsApp ba zai taɓa tura sakonnin gayyata na Pro, Gold, Plus, Star ko wani daftari na daban ba tare da ya fitar da sanarwa ba.

3. Cutar WhatsApp (WhatsApp Biros)

Ita kuma wannan cutar bata zuwa wa mutun kai tsaye daga WhatsApp, sai dai ta hanyar sakon Email a wayar salula.

Wasu na tura wa mutanen dake amfani da dandalin WhatsApp saƙon Email ɗauke da adireshin yanar gizo-gizo, sakon na cewa an tura maka sakon murya ko kiran murya a shafinka.

Da zaran mutum ya taba wannan adireshin yanar gizo dake kunshe a sakon nan take cutar zata shiga wayarsa kai tsaye. Kai tsaye zamu iya cewa wannan ƙarya ce domin WhatsApp bai taba sakin sanarwa daga wani wuri da yake ba wajensa ba.

Babu dalilin da WhatsApp zai sanar da mutum wani abu ta hanyar amfani da abinda basu da alaƙa kamar sakon Email, zai fi kyau mutum ya yi watsi da irin wannan.

4. Jerin muhimman sakonni daga WhatsApp Tabbas kusan kowa ya samu irin waɗannan sakonni, inda ake umartarka da ka tura wa mutum 10 dake cikin lambobin wayarka.

Babu tantama waɗannan sakonnin karya ce tsagwaronta, muna baka shawara ka yi watsi da irin waɗannan bayanan.

Misalin irin wannan sakonnin da ake yaɗawa shine:

“Barka! nine DAVID D. SURETECH, wanda ya ƙirƙiri Whatsapp. Muna sanar da masu amfani da manhajar mu cewa muna da sabon shafi miliyan 53m ne kacal, waɗanda mutane zasu iya buɗewa sabo.”

“Mutane sun mana yawa, muna bukatar taimakon ku wajen warware wannan matsalar. Muna son duk waɗanda ke amfani da mu a yanzun su tura wannan sakon zuwa ga dukkan abokansu.”

“Ta haka ne kaɗai zamu gane ainihin masu amfani da WhatsApp da wanda suka daina amfani da shi… sakon ya cigaba har zuwa ƙarshe.”

Game da wannan, kamfanin WhatsApp ya yi martani da kansa:

“Babu wasu kuɗaɗe da WhatsApp zai caji masu amfani da shi, muna san ku fahimci cewa wannan jita-jita ce da bata da tushe ballantana makama.”

5. Manhajar WhatsApp Spy

Da yuwuwar ka samu sakon sabuwar manhajar WhatsApp Spy , wadda zata baka damar shiga ka karanta abubuwan da wasu ke aikata wa a shafinsu.

A zahirin gaskiya wannan ƙarya ce tsagwaronta kuma ku ɗauki lamarin a matsayin soki burutsu ne kawai. Bayan kammala jin irin waɗannan labarai da mutane ke yaɗawa, Legit.ng ta nemo muku ingantaccen bayani daga kamfanin WhatsApp.

“Muna aiki da dukkanin karfinmu wajen rage saƙonnin karerayi dake shiga na’urar mu. Zami ƙirƙiri wuri da zai bada fifiko ga maganar da mutane ke yi da yan uwansu…”

“Matukar an turo maka irin wanna sakon to muna baka shawara ka datse ma’amala da wanda ya turo maka shi kuma ka goge sakon.”

“Domin guje wa cutar da abokanka, kada ka kuskura ka tura wa wani wannan sakon, ka gagguta kai rahoton shi sashin Spam.”

The post Abubuwa Game da Sakonnin da yake Yaɗawa Akan Manhajar WhatsApp  appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Lakaɗa wa ɗaliba Duka: An Dakatar da Shugaban Islamiyya a Jahar Kwara
Lakaɗa wa ɗaliba Duka: An Dakatar da Shugaban Islamiyya a Jahar Kwara

Gwamnatin jahar Kwara a Najeriya ta dakatar da shugaban wata makarantar arabiyya da wani bidiyo ya nuna an kewaye ɗaliba ana lakada mata duka saboda saɓa dokar makarantar.

Wata sanarwa da gwamnatin jahar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce an dakatar da shugaban makarantar ne bayan wata tawagar gwamnati da ta kunshi kwamishinan ilimi da mai ba gwamna shawara kan harakokin addinin Islama sun ziyarci Islamiyyar.

Bidiyon da gwamnatin ta wallafa a Facebook ya nuna yadda wasu maza suka sa ɗaliba tsakiya suna lakada mata duka.

Gwamnatin jahar Kwata ta ce ta naɗa kwamitin binciken al’amarin da ya ƙunshi malaman addini da jami’an gwamnati.

Sanarwar dai ba ta bayyana dalilin da ya haddasa yi wa ɗalibar duka ba da kuma lokacin da al’amarin ya faru.

The post Lakaɗa wa ɗaliba Duka: An Dakatar da Shugaban Islamiyya a Jahar Kwara  appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Mai Shafukan Sada Zumunta, Zuckerberg ya Bayyana Abinda ya Dame shi ya yin da Kafofin Suka Tsaya na Tsawon Sa’o’i 7
Mai Shafukan Sada Zumunta, Zuckerberg ya Bayyana Abinda ya Dame shi ya yin da Kafofin Suka Tsaya na Tsawon Sa’o’i 7

Wanda ya kirkiri kamfanin Facebook ya bayyana halin da ya shiga yayin da hajarsa ta daina aiki.

Ya bayyana cewa, asarar da ya tafka bata dame shi, kawai mutanen da suka dogara da kafafen ne suka dame shi.

Ya kuma bayyana cewa, masu yada zarge-zarge su daina yada karya cikin al’umma domin ba gaskiya suke fadi ba.

California, Amurka – Mark Zuckerberg, ya ce bai damu da kudin da ya rasa ba ko kuma yawan masu amfani da suka yi hijira zuwa wasu kafofin sada zumunta yayin da hajojinsa suka daina aiki na tsawon sa’o’i bakwai a ranar Litinin, 4 ga Oktoba.

Zuckerberg, mai kamfanin Facebook wanda ya bayyana matsayinsa a shafin Facebook a ranar Talata, 6 ga Oktoba ya ce ya fi damuwa da wadanda ke dogaro da hajojinsa don cudanya da abokai da dangi.

Ya rubuta:

“Mun shafe awanni 24 da suka gabata muna bincike kan yadda za mu iya karfafa tsarinmu kan irin wannan gazawar. Wannan kuma tunatarwa ce ga yadda aikin mu yake da mahimmanci ga mutane.”

Hakanan, Zuckerberg ya ce zarge-zargen da ake yada wa na masu satar bayanai kan ayyukan Facebook ba gaskiya ba ne kuma ba su shafi Facebook da ‘yan uwanta WhatsApp da Instagram ba.

Hakanan, Zuckerberg ya ce zarge-zargen da ake yada wa na masu satar bayanai kan ayyukan Facebook ba gaskiya ba ne kuma ba su shafi Facebook da ‘yan uwanta WhatsApp da Instagram ba.

A kalamansa:

“A zuciyar irin wadannan zarge-zargen shine muna fifita ra’ayin riba akan aminci da walwala. Wannan ba gaskiya bane.”

A rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu, Al Jazeera ta ba da rahoton cewa hadarin da Facebook ya shiga ya nuna illar dogaro da kafafen sada zumunta a matsayin hanya guda ta zamantakewa.

Mutane da dama sun shiga damuwa da rashin amfanin kafafen uku na sada zumunta na tsawon awanni bakwai.

The post Mai Shafukan Sada Zumunta, Zuckerberg ya Bayyana Abinda ya Dame shi ya yin da Kafofin Suka Tsaya na Tsawon Sa’o’i 7 appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Katsewar Shafukan: Asarar da Mai Kamfanin Shafin Sada Zumunta, Mark Zuckerberg ya Tafka
Katsewar Shafukan: Asarar da Mai Kamfanin Shafin Sada Zumunta, Mark Zuckerberg ya Tafka

Hanayen jarin Facebook ya faɗi da kashi 5.5 cikin 100, yayinda mai kamfanin, Mark Zuckerberg ya tafka asarar kusan dala biliyan 7 sakamakon katsewar shafin sada zumuntar a jiya Litinin.

Wannan katsewar ta shafi sauran shafuka mallakin Zuckerberg irinsu WhatsApp da Instagram.

Kamfanin mai karfin tattalin arziki a duniya ya rasa dimbin bilyoyin daloli tun bayan katsewarsa da misalin 4:42pm na yamma agogon Najeriya.

A cewar kididdigar NetBlocks, katsewar ta haifar da asarar dala miliyan 160 a kowacce sa’a guda.

Mutane sama da biliyan 2.9 ke amfani da shafin Facebook a faɗin duniya.

The post Katsewar Shafukan: Asarar da Mai Kamfanin Shafin Sada Zumunta, Mark Zuckerberg ya Tafka appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Shugaban Jami’ar UMYUK da ke Katsina, Farfesa Sunusi Mamman ya yi Barazanar Hana Budurwarsa Kammala Jami’ar
Shugaban Jami’ar UMYUK da ke Katsina, Farfesa Sunusi Mamman ya yi Barazanar Hana Budurwarsa Kammala Jami’ar

Shugaban jami’ar Umaru Musa Yar’Adua da ke jahar Katsina, Farfesa Sunusi Mamman ya yi barazanar hana budurwar sa kammala jami’ar.

Ya bukaci kada ta nuna ta san sa yayin da ake bincike akan sa bisa zargin amfani da matsayin sa wurin harkokin da basu dace ba da daliban sa mata.

A wani sako da ya yi wa wata budurwarsa, Aisha Tahir, ta WhatsApp ya ce matsawar tana so ta gama makarantar ta rufe bakin ta.

Jahar Katsina – Shugaban jami’ar Umaru Musa Yar’Adua da ke Jihar Katsina, Farfesa Sanusi Mamman ya yi barzanar korar budurwarsa daga jami’ar idan har ta nuna ta san shi, Daily Nigerian ta rawaito.

Ana zargin Mamman, wanda yanzu haka farfesa ne a bangaren ilimi na musamman, da laifuka masu yawa tun daga wadaka da dukiyar makarantar zuwa yin harkokin da basu dace ba da wasu dalibansa.

An zarge shi da gyara wa daliban sa da suka koma ‘yan matan sa sakamakon jarabawar su da sauran su.

Yakan sa a dauke wuta idan zai kai wa ‘yan matan sa ziyara a makwancin su na makarantar

Ana zargin VC din da bayar da umarnin a dauke wuta a gaba daya makwancin dalibai mata idan zai kai wa budurwar sa ziyara.

Bayan korafin jama’a ya yawaita, har da na tsofaffin daliban sa, Daily Nigerian ta tattaro bayanai akan yadda hukumar makarantar ta shirya wata kungiya da zata yi bincike akan wannan zargin da ake ma sa.

Sai dai kungiyar ta gayyaci wasu daga cikin daliban sa don su bayar da shaida akan sa, daga nan ne Mamman ya rude ya fara kiran tsofaffin ‘yan matan sa yana razana su akan kada su tona masa asiri.

Aisha Tahir, daya daga cikin ‘yan matan sa ta tattauna da Daily Nigerian ta wayar salula inda ta ce VC din ya yi barazanar hana ta kammala makarantar matsawar ta fallasa ma sa asiri.

Ya ce kada ta kuskura ta nuna ta san shi

Kamar yadda ta bayyana ya tura mata sako ta WhatsApp:

“Ki dage akan cewa mahaifin ki ne ya biya miki kudin dakin da kike zama a makaranta. Idan ki ka yi wani kuskure, za ki rasa digirin ki.

“Ki sanar da su cewa sunan da ake kiran ki, ‘First Lady’ dama tsohon suna ne kuma baki sanni ba gaba daya.”

Aisha daliba ce ‘yar aji 4 a jami’ar inda take karanta Geography Education. Dalibai ne su ka sa mata suna First Lady. Ta ce razanar da ita da VC din ya yi ne yasa ta ce sai ta tona ma sa asiri.

A cewarta, VC din ya nemi auren ta don har Malumfashi ya je wurin iyayen ta ya nemi auren ta da kudi N110,000 a matsayin kudin na-gani-ina-so da kuma sadaki.

Ta ce:

“Da farko ya neme ni ta Facebook ne inda ya bukaci in ba shi lambar waya ta. Ban gane shi ba, na zaci kawai wani ne daban, sai ya ce min shi malami na ne ya tura min hoton sa.

“Bayan nan ne mu ka fara magana, sai dai daga baya ya fara korafi akan yadda na sanar da mutane soyayyar mu.

“Na yi kokarin gamsar da shi cewa batun aure babu sirri kuma ko ban bayyana ba, ‘yan uwa na da ya samu a Malumfashi za su bayyana.

“Daga nan ne muka rabu. Ya dakatar da lambata daga kiran sa sannan muka dena magana gaba daya har sai yanzu da maganar nan ta taso.

“Mahaifi na ya fara kira ya bukaci in yi karya a gaban hukumar makarantar dake bincike akan sa.Ya tsoratar da shi akan cewa in har na fadi gaskiya ba zan gama jami’ar nan ba.”

An yi kokarin jin ta bakin VC din amma lambarsa ba ta zuwa kuma bai bayar da amsar sakon da Daily Nigerian ta tura ma sa ba dangane da zargin.

The post Shugaban Jami’ar UMYUK da ke Katsina, Farfesa Sunusi Mamman ya yi Barazanar Hana Budurwarsa Kammala Jami’ar appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Aliko Dangote ya Koma na 117 a Jerin Manyan Attajiran Duniya
Aliko Dangote ya Koma na 117 a Jerin Manyan Attajiran Duniya

Babban attajirin nan na Najeriya da Africa, Aliko Dangote, ya koma na 117 a jerin manyan attajiran duniya da aka fitar.

Rahoton wanda jaridar Bloomberg ta fitar ya nuna cewa Dangote ya mallaki dala biliyan $17.8bn.

Elon Musk, shine attajirin da yafi kowa kuɗi a duniya kamar yadda rahoton ya nuna da dala biliyan $194bn.

Kano – Sabon rahoton manyan attajiran duniya da jaridar Bloomberg ta fitar ya nuna cewa attajirin mai kuɗin Najeriya, Aliko Dangote ya koma na 117.

Kafin fitar da rahotonta, jaridar Bloomberg tana bincike da tattara bayani tare da lissafa dukiyar da kowane mai kuɗi ya mallaka.

BBC Hausa ta ruwaito cewa Bloomberg na yawaita fitar da rahoto game manyan mafiya arziki a duniya.

A wannan karan rahoton ya bayyana cewa Aliko Dangote, shugaban kamfanin ‘Dangote Group’ ya mallaki dukiyar da takai dalar Amurka biliyan $17.8bn.

Wanene yafi kowa arziki a duniya?

Wanda yafi kowa kuɗi a duniya a cewar rahoton shine Elon Musk, haifaffen ƙasar Africa ta kudu, wanda ya mallaki dalar Amurka biliyan $194bn.

Mutumin da yazo na biyu shine shugaban kamfanin Amazon kuma mamallakinsa, Jeff Bezoz, wanda yake da arzikin dala biliyan $194bn.

Attajiri na uku mafi kuɗi a duniya shine Bernard Arnault, ɗan kasar Faransa wanda ya mallaki dala biliyan $174bn.

A baya dai shugaban kamfanin Microsoft, Bill Gates, shike rike da matsayi na uku amma yanzun an kere shi.

Punch ta ruwaito cewa ana ganin dai kuɗin Bill Gates ya ragu ne sanadiyyar rabuwar da ya yi da matarsa Melinda Gates a yan kwanakin baya.

Mamallakin shafin sada zumunta wato Facebook, Mark Zuckerberg, shine na biyar a jerin masu kuɗin duniya inda yake da dukiyar da takai dala biliyan $135bn.

The post Aliko Dangote ya Koma na 117 a Jerin Manyan Attajiran Duniya appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Da Zarar Twitter ta yi Rijista da NBC da CAC Zamu Janye Dakatarwar – Gwamnatin Tarayya
Da Zarar Twitter ta yi Rijista da NBC da CAC Zamu Janye Dakatarwar – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce bata hana yan kasa amfani da Manhajar Twitter ba.

Gwamnatin ta ce duk da dakatarwar, yan Nigeria na cigaba da shiga Twitter da VPN.

Gwamnatin ta ce za ta janye dakatarwar da ta yi wa Twitter da zarar ta yi rajista da NBC da CAC.

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta fada wa babban kotun tarayya a Legas cewa bata hana yan Nigeria amfani da dandalin sada zumunta na Twitter ba, tana mai cewa har yanzu yan Nigeria da dama suna amfani da shi a kullum, rahoton The Punch.

Attoni Janar na kasa, Abubakar Malami, da gwamnatin tarayya ta bayyana hakan ne yayin bada amsa kan wani kara da lauya mai rajjin kare hakkin bil adama, Inihebe Effiong ya shigar game da batun na hana amfani da Twitter.

A ranar 4 ga watan Yunin shekarar 2021 ne gwamnatin Nigeria ta dakatar da ayyukan Twitter kimanin kwanaki biyu bayan Twitter ta goge wani rubutu da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a dandalin.

Sai dai, yan Nigeria da dama na amfani da manhajar VPN mai badda-kama domin amfani da manhajar na Twitter duk da dakatarwar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Malami, ciki wata sanarwa da ya fitar ya yi barazanar tuhumar yan Nigeria da ke cigaba da amfani da manhajar yayin da NBC ta umurci dukkan gidajen rediyo da talabijin su dena daukan labarai daga Twitter.

Lauyan mai rajjin kare hakkin bil adama, Effiong, ya yi karar Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, Malami, da gwamnatin tarayya bisa dakatar da Twitter.

A cikin karar Effiong ya nemi kotu ta hana gwamnati dakatar da amfani da manhajar ko hana mutane amfani da wasu dandalin sada zumuntar da wasu bukatu takwas da ya ce keta hakkin bil adama ne.

Dakatar da Twitter ta take hakkin bil adama bane Sai dai, Mr Ilop Lawrece a madadin gwamnatin tarayya da AGF ya ce dakatar da Twitter ba take hakkin bil adama bane domin har yanzu yan Nigeria na cigaba da amfani da Twitter.

Ya kuma ce yan Nigeria na da damar bayyana ra’ayoyinsu da sukar gwamnati idan bukatar hakan ya tashi a wasu kafafen kamar WhatsApp, Facebook, Tiktok da wasu sauran.

Gwamnatin tarayyar ta kuma ce yan Nigeria su dena fushi da ita domin ba laifinta bane domin Twitter ta ki bin dokokin kasa.

Gwamnatin ta fadawa kotu cewa za ta janye dakatarwa da ta yi wa Twitter da zarar kamfanin ta yi rajista da NBC da CAC.

The post Da Zarar Twitter ta yi Rijista da NBC da CAC Zamu Janye Dakatarwar – Gwamnatin Tarayya appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Donald Trump: Tsohon Shugaban Kasar Amurka ya Dawo Kan Kafofin Sada Zumunta
Donald Trump: Tsohon Shugaban Kasar Amurka ya Dawo Kan Kafofin Sada Zumunta

Bayan gargame asusun tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump, an sake bude masa.

Tsohon shugaban kasan ya dawo kan kafofin sada zumunta a matsayin tsohon shugaba.

Faceboo, Twitter, Instagram, Reddit, Snapchat da sauransu ne a baya suka gargame asusun Donald Trump ya cire tsohuwar asusun Gab din sa saboda dawowar da ya yi ta kafofin sada zumunta sakamakon gogewar da manyan kamfanonin fasaha na Silicon Valley suka yi.

A sakonsa na farko zuwa shafin tun ranar 8 ga Janairu, Trump ya daura martanin lauyansa kan bukatun da ya bayar da shaida a sauraren tsige shi karo na biyu mako mai zuwa.

Trump ya koma ga sakin bayanan ne daga Ofishin tsohon shugaban kasar bayan da Facebook, Twitter, Instagram, Reddit, Snapchat, Twitch, Shopify, Stripe, da YouTube, da sauransu suka datse.

Duk da yake dawowarsa ga shafukan sada zumunta kawai ya sake rubuta wasikar lauyoyin nasa ne, kalmomin suna dauke da halayyar tsohon shugaban, kamar yadda jaridar Independent ta ruwaito.

Lauyoyin David Schoen da Bruce Castor Jr sun rubuta cewa “Muna nan kan karbar sabuwar dangantakar ku ta jama’a.”

“Wasikarku kawai ta tabbatar da abin da kowa ya sani ne: ba za ku iya tabbatar da zargin da kuke yi wa Shugaban Amurka na 45, wanda yanzu dan kasa ne mai zaman kansa.

“Amfani da Kundin Tsarin Mulkin mu wajen kawo karar da ake zargin tsige shi yana da matukar mahimmanci a yi kokarin yin wadannan wasannin.”

Lauyoyin Trump suna amsa jawabi ne daga dan majalisa Jamie Raskin cewa tsohon shugaban ya bayyana a gaba ko a lokacin shari’ar, kan batun yi masa tambayoyi, yana mai nuna shaidar tsoffin shugabanni Gerald Ford da Bill Clinton a lokacin da suke kan mulki.

The post Donald Trump: Tsohon Shugaban Kasar Amurka ya Dawo Kan Kafofin Sada Zumunta appeared first on Arewa Agenda Hausa.