Kudancin Najeriya Archives - Arewa Agenda Hausa

Rundunar Sojoji Sun Kama Hadimin Gwamna Mai Daukar Nauyin ‘Yan Bindiga a Kudancin Najeriya
Rundunar Sojoji Sun Kama Hadimin Gwamna Mai Daukar Nauyin ‘Yan Bindiga a Kudancin Najeriya

Rundunar sojoji ta bankado wanda yake da hannu dumu-dumu a daukar dawainiyar ‘yan bindiga a yankin kudancin Najeriya.

An gano wani hadimin gwamna, Tochukwu Okeke alias Owo a matsayin mai daukar nauyin ‘Unknown Gunmen’ a kudanci.

Okeke yana da kungiya wadanda suke amfani da makaman kare dangi wurin kai wa ‘yan sanda, sojoji da fararen hula farmaki.

Kudancin Najeriya – Rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar damko hadimin gwamna ne wanda yake kulle-kullen rura wutar ta’addanci a kudu maso gabas.

An bankado wanda ake zargin yana da hannu akan kaiwa mutanen gari da jami’an tsaro farmaki a kudu maso gabacin Najeriya.

Hadimin gwamna ke daukar nauyin ‘Unkwown Gunmen’

PRNigeria ta tattaro bayanai akan yadda wani Tochukwu Okeke alias Owo, hadimin gwamna a kudu maso gabas ya daurewa ‘yan bindiga gindi kamar yadda rundunar division 82 na sojojin Najeriya a Enugu suka bankado.

Majiyar ta sojoji ta bayyana hakan ne inda ta bukaci a boye ta, tace hadimin yana da kungiya mai makaman kare dangi kuma suna kai hari ga ‘yan sanda, sojoji da fararen hula.

Kafin a kama wasu daga cikin shugabannin su a kuma lalata sansaninsu cikin ‘yan kwanakin nan, sun kaiwa ‘yan sanda da sojoji farmaki a Enugu ciki har da ofishin ‘yan sanda na Adani, wata matsayar sojoji dake kan titin Adani-Omoh, ofishin ‘yan sanda na Ezeagu, sansanin sojoji dake titin Orji River-Udi da wata dake kan titin Enugu Abakaliki.

Kungiyar ‘yan ta’addan wacce aka fi sani da “mugaye marasa imani” suna satar makamai a wurin jami’an tsaron da suke kaiwa farmaki.

Majiyar ta sanar da PRNigeria cewa an ragargaji daya daga cikin sansanayensu dake Akpawfu-Amangwunze dake karamar hukumar Nkanu ta yamma inda aka kwato makamai da dama da ababen hawa.

The post Rundunar Sojoji Sun Kama Hadimin Gwamna Mai Daukar Nauyin ‘Yan Bindiga a Kudancin Najeriya appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Sojoji da ‘Yan Sandan Najeriya Suna Shirin Kawo Karshen Ta’adin ‘Yan Kungiyar IPOB
Sojoji da ‘Yan Sandan Najeriya Suna Shirin Kawo Karshen Ta’adin ‘Yan Kungiyar IPOB

Sojoji da ‘Yan Sanda suna shirin dura a kan dakarun tawayen kungiyar IPOB.

An soma aika Jami’an ‘yan sanda zuwa kowace jaha da ke Kudancin Najeriya.

Shugaban kasa ya bada umarnin a ga bayan duk mai neman tada zaune-tsaye.

Ganin yadda ake fama da matsalar ‘yan tawaye a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, jami’an tsaro suna shirin tada dakarun da za su fuskanci matsalar.

Jaridar The Cable ta fahimci cewa sojojin Najeriya da ‘yan sanda za su kaddamar da wani shiri na musamman domin a samu zaman lafiya a Kudu maso gabas.

Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba jami’an tsaro umarnin suyi abin da zai kawo karshen ta’adin da wasu miyagu suke yi.

“’Yan IPOB sun dauko hayar sojoji fiye da 50, 000, sun sa a rundunar ESN, sun tara makamai da suka samu a hannun ‘yan sanda lokacin zanga-zangar #EndSARS.”

Wani jami’in tsaro ya cigaba da fallasa kungiyar, ya ce: “Suna ta shigo da makamai ta Kamaru, tare da hadin-kan ‘yan tawayen Ambazonia da ke Kudancin Kamaru.”

“Duk mako, IPOB na tura akalla maza da mata 2000 zuwa Kamaru domin a koya masu amfani da makamai” A dalilin haka ne rundunar ‘yan sanda ta fara shiri a Kudu maso gabas domin kai wa ‘yan tawayen hari.

An fara baza jami’an ka-da-ta-kwana zuwa jahohin yankin.

An kai mataimakan kwamishinonin ‘yan sanda uku da runduna ta musamman zuwa kowace jaha.

Su ma rundunar sojoji suna shiri na musamman ta yadda za su hada-kai da ‘yan sanda, domin su lallasa duk inda sojojin ‘ya ta’addan suke da nufin a kawo karshensu.

Gwamnatin Najeriya ta na sa ran shigowar wasu kayan fada kwanan nan, daga ciki har da jiragen yaki da za a kawo daga kasar Amurka da sojoji za su yi aiki da su.

A yau kun ji yadda mutanen Kungiyar IPOB suka yi sanadiyyar da wasu suka rasa motocin man-ja da suka dauko kaya daga garin Nsukka, za a kawo jahar Kano.

Shugaban kungiyar Galadima Road Transport ya bayyana cewa su na zargin ‘Yan ta’addan IPOB ne suke kai hari, suka barnatar dukiyar da su ka dauko daga Kudu.

The post Sojoji da ‘Yan Sandan Najeriya Suna Shirin Kawo Karshen Ta’adin ‘Yan Kungiyar IPOB appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Gwamnatin Jahar Kano ta Fadi Yankin da ya Dace a Fitar da Shugaban Kasa a 2023
Gwamnatin Jahar Kano ta  Fadi Yankin da ya Dace a Fitar da Shugaban Kasa a 2023

Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan Kano ya ce yana goyon bayan a mika mulki ga kudancin Nigeria a 2023.

Gwamnan ya ce duk da cewa tsarin karba-karba baya cikin kudin tsarin mulki, tsari ne da ke taimakawa a ci zabe.

Ganduje ya kuma ce yana kyautata zaton APC za ta sake cin zaben mulkin kasar a 2023 domin cigaban da aka samu a tsaro da tattalin arziki a karkashin mulkin Buhari.

Gabanin babban zaben da ke tafe a 2023, Gwamnan Jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya kamata a bawa kudancin Nigeria tikitin takarar kujerar shugaban kasa.

Ganduje ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today a Channels Television da aka haska a ranar Juma’a.

“Kudancin Nigeria ya dace a bawa takara amma ya kamata a samu hadin kai tsakaninsu,” ya ce a yayin da ya ke amsa tambayar game da yankin da ya dace ta fitar da shugaban kasa a 2023.

“Kudancin Nigeria ya dace a bawa takara amma ya kamata a samu hadin kai tsakaninsu,” ya ce a yayin da ya ke amsa tambayar game da yankin da ya dace ta fitar da shugaban kasa a 2023.

“Karba-karba duk da cewa bata cikin kundin tsarin mulkin jamhuriyar tarayyar Nigeria tsari ne na cin zabe.”

Da aka masa tambaya shin ko APC ta tabuka abin a zo a gani tun bayan lashe zabe da ta yi a 2015, ya amsa da cewa eh.

Ya ce jam’iyyar APC a karkashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ta inganta tsaro sannan tana gyara tattalin arzikin kasar.

Ganduje ya ce yana kyautata zaton jam’iyyar mai mulki za ta yi nasara a babban zaben 2023 da ke tafe ta cigaba da jagorancin kasar.

Amma ya ce akwai bukatar jam’iyyar ta yi shiri mai kyau tare da bincike kan hanyoyin da suka fi dacewa domin sake cin zabe a kasar.

The post Gwamnatin Jahar Kano ta  Fadi Yankin da ya Dace a Fitar da Shugaban Kasa a 2023 appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Ina Kira da a yi Watsi da Kaiwa da Kawowa na Makiyaya Daga Sassan Arewa Zuwa Kudancin Najeriya – Gwamnan Kano
Ina Kira da a yi Watsi da Kaiwa da Kawowa na Makiyaya Daga Sassan Arewa Zuwa Kudancin Najeriya – Gwamnan Kano

Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano ya bukaci a sanya dokar hana yawon shanu daga arewa zuwa kudu.

Ya ce za su samar da matsuguni ga makiyaya a dajin Samsosua da ke tsakanin jahar Kano da Katsina.

Ya ce hakan ne kawai zai iya sa a shawo kan matsalar rikicin manoma da makiyaya a fadin kasar na Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ya dace a saka dokar da za ta hana kai shanu daga arewa zuwa kudu, The Cable ta wallafa.

A yayin zantawa da manema labarai bayan haduwarsa da gwamnonin APC tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura, jahar Katsina, Ganduje ya ce idan har ba a hana yawon shanu ba, babu ranar kawo karshen manoma da makiyaya.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta shirya samar da wurin zama ga makiyayan a dajin da ke tsakanin iyakar Kano da Katsina.

Ya ce matsugunin zai kasance da gidaje, tafki, cibiyar dabbobi ta zamani da asibitocin dabbobi.

“Zamu gina matsugunin a dajin Samsosua, iyakarmu da Katsina kuma mun yi nasarar shawo kan illar ‘yan bindiga a yankin,” Ganduje yace.

“Za mu gina gidaje, tafkuna, cibiyar dabbobi, asibitin dabbobi kuma tuni muka fara ginawa makiyayan gidaje.

“Ina kira a kan a yi watsi da kaiwa da kawowa ko kuma yawon makiyaya daga sassan arewa zuwa tsakiyar kasar nan ko kudancin Najeriya.

“A saka dokar haramcin hakan ko kuma ba za mu iya shawo kan rikici tsakanin makiyaya da manoma ba kuma ba za mu iya hana satar shanu ba da ya addabe mu.”

The post Ina Kira da a yi Watsi da Kaiwa da Kawowa na Makiyaya Daga Sassan Arewa Zuwa Kudancin Najeriya – Gwamnan Kano appeared first on Arewa Agenda Hausa.