Neja Archives - Arewa Agenda Hausa

Ambaliyar Ruwa: Mutane 11 Sun Mutu a Jihar Neja
Ambaliyar Ruwa: Mutane 11 Sun Mutu a Jihar Neja

Mummunar ambaliya ruwa ta yi sanadin mutuwar mutum 11 a jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya, tare da lalata garuruwa masu yawa faɗin ƙananan hukumomi 19 daga cikin 25 da ke jihar.

Cikin wata sanarwa da daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, Abdullahi Baba-Arah, ya fitar ya ce lamarin ya lalata gidaje fiye da 6,865, tare da gonaki 118,692, kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito.

Lamarin ya jefa fiye da mutum 41,000 cikin tsananin buƙatar tallafi.

Baya ga lalata gonakin, ambaliyar ta kuma shafi makarantu 246, lamarin da ya shafi harkokin ilimi a garuruwa 529 na jihar.

Ƙananan hukumomin da lamarin ya fi ƙamari sun haɗa da Mokwa da Katcha da Lavun da Lapai da Agaie da Shiroro da Munya da Gbako da Kontagora da Bosso da Edati da Agwara da Bida da Magama da Mashegu da Borgu da Gurara da Suleja da ƙaramar hukumar Rijau.

Rahotonni sun ce ambaliyar ta kuma shafi gadoji 18 da kwalbatoci 80, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin sufuri a wasu yankunan jihar.

The post Ambaliyar Ruwa: Mutane 11 Sun Mutu a Jihar Neja appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Mutane 30 Sun Mutu Sakamakon Fashewar Tankar Mai a Neja
Mutane 30 Sun Mutu Sakamakon Fashewar Tankar Mai a Neja

Neja – Sama da mutane 30 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon fashewar tankar mai a karamar hukumar Agaie ta jihar Neja.

An bayyana cewa tankar man ta yi karo ne da wata motar tirela dauke da matafiya da shanu daga karamar hukumar Wudil ta jihar Kano.

Tanka ta fashe, mutane sun mutu

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA) Abdullahi Baba-Arab ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a wata sanarwa, inji rahoton The Punch.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 12:30 na rana a kan titin Lapai-Agaie mai nisan kilomita 2 daga yankin Dendo a karamar hukumar Agaie.

A cewar Baba-Arab, sama da shanu 50 ne suka babbake da ransu yayin da wasu motoci guda biyu; babbar motar daukar karafuna da wata motar daukar kaya suka kone a cikin gobarar.

NSEMA ta yi bayanin iftila’in

Sanarwar ta NSEMA ta ce:

“NSEMA ta samu rahoton fashewar wata tankar mai a ranar Lahadi, 8 ga Satumba, 2024 da misalin karfe 12:30 na rana a kan titint Lapai-Agaie, kilomita 2 daga Dendo a Agaie.

“Lamarin ya faru ne a lokacin da wata tankar fetur ta yi karo da wata motar tirela da ke dauke da matafiya da shanu daga Wudil a jihar Kano da ke kan hanyar zuwa Legas.

“Sama da mutane 30 ne aka tabbatar sun mutu, tare da babbakewar shanu sama da 50 da ransu. Har yanzu tawagar NSEMA tare da haɗin gwiwar LGEMCs suna wurin da abin ya faru.”

The post Mutane 30 Sun Mutu Sakamakon Fashewar Tankar Mai a Neja appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Fasinjoji 20 Sun Mutu a Hatsarin ƙwale-kwale a Jihar Neja
Fasinjoji 20 Sun Mutu a Hatsarin ƙwale-kwale a Jihar Neja

Aƙalla mutum 24 galibinsu manoma ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka ɓace a lokacin da wani ƙwale-kwale ɗauke da fasinjoji ya kife a garin Gbajibo, a ƙaramar hukumar Mokwa da ke jihar Neja a arewa ta tsakiyar Najeriya.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi.

Rahotonni na cewa fasinjojin kwale-kwalen sun fito ne daga garuruwan Gbajibo da Ekwa da Yankeiade.

Jaridar Daily a Najeriya ta ambato shugaban ƙaramar hukumar Mokwa Jibrin Abdullahi Muregi na cewa an kuɓutar da gawarwaki 21.

Jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce suna tattara alƙaluma domin sanin haƙiƙanin adadin mutanen da lamarin ya shafa.

Hatsarin na zuwa ne kwana biyu bayan da wani kwale-kwale ya kife ɗauke da fasinjoji ciki har da mata da ƙananan yara ya kife a Yola ta jihar Adamawa, lamarin da ya haddasa asarar rayuka.

The post Fasinjoji 20 Sun Mutu a Hatsarin ƙwale-kwale a Jihar Neja appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Kifewar Kwale-Kwale: Mutane 6 Sun ɓace a Jihar Neja
Kifewar Kwale-Kwale: Mutane 6 Sun ɓace a Jihar Neja

Aƙalla fiye da fasinjoji shida ne aka bayyana cewa sun ɓace bayan da wani kwale-kwale ya kife da su a kogin Zamre a ƙaramar hukumar mulki ta Agwara da ke jahar Neja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru a ranar Litinin lokacin da matafiyan waɗanda galibinsu manoma ne ke kan hanyar tafiya daga Neja zuwa jahar Kebbi.

A halin yanzu an gano gawar mutum ɗaya daga cikin su, sannan ana ci gaba da neman sauran da suka ɓacen.

Rahotan ya ce kwale-kwalen na ɗauke da fasinjoji 20 da suka haɗa da mata da ƙananan yara, inda ya kife sakamakon tsayawar injin daidai lokacin suka kai tsakiyar kogin.

Jaridar ta ruwaito cewa Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jahar Naija ta tabbatar da aukuwar lamarin sai dai babban daraktanta, Garba Salihu, ya ce kawo yanzu ba a kai ga samun cikakkun alƙalumman waɗanda suka mutu ba.

The post Kifewar Kwale-Kwale: Mutane 6 Sun ɓace a Jihar Neja appeared first on Arewa Agenda Hausa.

‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 50 a Jihar Neja
‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 50 a Jihar Neja

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 50 a wani kauyen da ke jihar Neja a tsakiyar Najeriya.

Jaridar Nation ta Najeriya ta rawaito cewa yankin da lamarin ya faru na yawaita fuskantar hare-hare da sace-sace domin neman kudin fansa.

Sannan a cewar rahotanni ‘yan bindigar sun kuma kwashe ababen hawan mutane da dabobbinsu.

Har yanzu dai ba a tabbatar da wannan hari a hukumance ba.

Amma garkuwa da mutane domin neman kudin fansa abu ne da ya yi fice a arewacin Najeriya tun 2020, musamman Neja.

Wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa mutum 1,230 aka kashe a hare-haren ‘yan bindiga a watannin ukun farkon wannan shekarar a fadin Najeriya, sannan an sace 650.

The post ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 50 a Jihar Neja appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja ta kama Masu Garkuwa da Mutane Tare da Kuɓutar da Mutum 7
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja ta kama Masu Garkuwa da Mutane Tare da Kuɓutar da Mutum 7

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja da ke arewacin Najeriya ta ce ta kama mutum biyu da take zargi da garkuwa da mutane a yankin ƙaramar hukumar Gurara da ke jihar, tare da kuɓutar da mutum bakwai , adanda suka haɗar da maza shida da mace ɗaya.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar DSP Wasiu Abiodun ya ce an kama masu garkuwar ranar Juma’a sakamakon bayanan sirri da rundunar ta samu.

Inda nan take rundunar ta tura jami’anta zuwa yankin tare da haɗin gwiwwar jami’an sa kai.

Sanarwar ta ce jami’an ‘yan sandan sun yi musayar wuta da masu garkuwar a cikin daji, daga nan ne kuma masu garkuwar suka gudu tare da barin mutum shida da ke ɓoye a hannunsu.

The post Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja ta kama Masu Garkuwa da Mutane Tare da Kuɓutar da Mutum 7 appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Manomi Yayiwa Wata Mata Yankan Rago
Manomi Yayiwa Wata Mata Yankan Rago

Daga Hassana Magaji

Ana Zargin Wani Manomi Mai Suna Tafiya da Yiwa Wata Mata Mai Suna Hajjo Yankan Rago, Wanda Yayi Sanadiyyar Mutuwar ta Nan Take.

Lamarin dai Ya Aukune a Wani Gari da Ake kira Mabono dake Karamar Hukumar Bangi a Jihar Neja,Yayin Bincike Angano Cewar Mutumin Ya Yankata ne Sanadiyyar Shiga Gonan Gyadan shi da Dabbobinta Sukayi Inda Sukaci Wani Sashi na Gyadan daya Shuka.

Lamarin dai Ya Haifar da Cece Kuce Tsakanin ‘Yan Sanda Da Mutanen da Lamarin Ya Shafa Inda Dakyar da Sudin Goshi Suka Amince da Bayar da Gawan Hajjon Domin a Sallaci Gawar nata.

Har Yanxun dai ‘Yan Uwan Wanda Ake Zargi da Aikata Kisan Sunyi Dafifi a Harabar Ofishin ‘Yan Sandan Inda Suke Neman Abasu Belin Wanda ake Zargin, Yayinda Rundunar ‘Yan Sandan Sukayi Watsi da Bukatar ta su.

Tuni Angudanar da Jana’izar Marigayiyar Kamar Yadda Addinin Musulunci Ta Tanada,Sedai A dayan Bangaren ‘Yan Uwanta Nakira da Masu Ruwa da Tsaki dasu Gaggauta bi masu Hakkin Wannan Aika Aika.

The post Manomi Yayiwa Wata Mata Yankan Rago appeared first on Arewa Agenda Hausa.

An Tsinci Gawar Mace da Namiji a Cikin Kango Tsirara a Jihar Neja
An Tsinci Gawar Mace da Namiji a Cikin Kango Tsirara a Jihar Neja

Mutane sun tsinci gawarwakin wasu mutum biyu, namiji da mace tsirara a wani Kango a yankin karamar hukumar Suleja, jihar.

Neja Mutumin da ya fara ganin gawarwakin ya bayyana yadda ya gan su yayin da yaje kusa da Kangon yin bayan gida.

Wannan na zuwa ne yayin da mutane suka fara tashi daga wasu Anguwannin cikin Katsina saboda tsoron yan bindiga.

Niger- An gano gawar Wani mutumi da aka gano sunasa, Adeyemi, da wata mata da ba’a san bayananta ba a wani gini da ba’a karisa ba a Anguwan Gwari, Kwanba a ƙaramar hukumar Suleja, jihar Neja.

Wani mazaunin yankin, Ikechukwu Michael, wanda ya fara ganin gawarwakin ranar Talata, ya bayyana cewa ya je kusa da Kangon da nufin yin bayan gida, sai ya ji wani wari na tsaro wa daga ciki.

Daily Trust ta rahoto a kalamansa Mista Michael ya ce: “Na ga mutumin tsirara babu tufafi a jikinsa yayin da ita kuma budurwan na ganta rabin jiki tsirara.

Tuni fatar gawar marigayi Adeyemi ta fara salewa. Ita macen na ganta kwance kan fuskarta, da ganin haka sai na ankarar da mutane.”

Ya ƙara da cewa jim kaɗan bayan gano gawarwakin mutanen biyu, jami’an yan sanda suka iso wurin, suka kwashe su zuwa ɗakin aje gawarwaki.

Shin yan uwan mamatan basu neme su ba?

Wani wanda ya yi wa marigayi Adeyemi farin sani, Ogundipe Ayo, ya shaida wa wakilin jaridar cewa yayin da ya kira matar mamacin ta nuna masa bata san da faruwar lamarin ba.

A cewarsa, ta shaida masa cewa rabonta da Mai gida tun ranar Lahadi da yamma kuma idan ta neme shi bata samun shi.

Hukumar yan sanda reshen jihar Neja ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba a yanzu da muke kawo muku wannan rahoton.

The post An Tsinci Gawar Mace da Namiji a Cikin Kango Tsirara a Jihar Neja appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Miji ya Shigar da ƙarar Surukansa a Kotu Kan Zargin Sun yi Garkuwa da Matarsa
Miji ya Shigar da ƙarar Surukansa a Kotu Kan Zargin Sun yi Garkuwa da Matarsa

Abu kamar wasan kwaikwayo, wani mutumi ya kai ƙarar Surukansa kan zargin sun yi garkuwa da matarsa woto diyarsu a Suleja, jihar Neja.

Mai shigar da ƙara a Kotu daga hukumar yan sanda ya gaya wa Alƙali cewa mutanen biyu sun je har gidan diyarsu sun tafi da ita.

Wannan na zuwa ne a lokacin mutane suka tsinci gawar mutum biyu mace da namiji a Kango duk a yankin na Suleja.

Niger- An gurfanar da iyayen wata matar aure da ke zaune a Kwankwashe, yankin ƙaramar hukumar Suleja, jihar Neja a gaban Kotun Majistire da ke zamanta a Madalla.

Jaridar Daily Trust ta ruwiato cewa hukumar yan sanda ta gurfanar da iyayen matan a Kotu ne bisa zargin sun sace ɗiyar su daga gidan Aurenta.

Mai shigar da ƙara, ASP John Ateni, ya faɗa wa Kotun cewa mutumin da ake zargi, Godgift Ekwedi, da matarsa, Eshima Ekwedi, sun dira gidan ɗiyar su da ke yankin Rafin Sanyi a Suleja, suka yi awon gaba da ita ba tare da izinin mijinta ba.

Bugu da ƙari a cewar mai shigar da karar, sun kwashe kayayyaki a gidan auren ɗiyar ta su wanda a kiyasi sun kai darajar Miliyan biyu da rabi, daga bisani suka cigaba da amfani da kayan.

Wane mataki Kotu ta ɗauka?

Waɗan da ake zargin sun musanta dukkan tuhume-tuhumen da aka ɗora kansu kuma suka nemi Kotu ta ba da belin su.

Alƙalin Kotun, Mai shari’a Ruth Ibrahim, ta bai wa waɗan da ake ƙara beli bisa sharaɗin kawo wanda zai tsaya musu kuma tilas ya zama mazaunin Madalla.

Bayan sauraron ɓangarorin biyu, Alkalin Kotun ta sanar da ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 5 ga watan Satumba, 2022.

The post Miji ya Shigar da ƙarar Surukansa a Kotu Kan Zargin Sun yi Garkuwa da Matarsa appeared first on Arewa Agenda Hausa.

‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki a Yankin Jihar Neja
‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki a Yankin Jihar Neja

Rahoto daga majiya mai tushe ya bayyana yadda ‘yan bindiga suka farmaki wani kauye a yankin jihar Neja.

An ga mazauna yankin da lamarin ya shafa suna gudun tsira, tare da boye shanunsu daga sacewar ‘yan bindiga.

Ana yawan samun hare-hare a yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya, lamarin da ya raba jama’a da gidajensu.

Kontagora, jihar Neja – A safiyar yau Alhamis ne ‘yan ta’adda suka mamaye wasu al’ummomin yankin Kamapani Waya a karamar hukumar Kontagora a jihar Neja.

Wakilin The Nation, wanda ke kan hanyar zuwa Kontagora daga Minna a motar haya, ya koma da baya bayan ya bar yankin Kampani Waya.

Wasu motoci ne suka sanar da direban motar cewa, akwai ‘yan bindiga da ke barna kan mutanen kauyen.

Rahoton jaridar ya ce, mutanen da ke motar sai da suka koma Kampani Waya kana suka zauna a can na kusan mintuna 40.

An ga mutanen kauyen cikin shiri yayin da wasu ke kira ga mata da yara su je su buya. Hakazalika, wasu sun kwashe shanunsu domin boyesu.

Duk motocin da suka taho daga Minna sai da suka tsaya don gudun shiga cikin tashin hankalin da ‘yan bindigan ka iya jefa su.

A bangare guda, jaridar ta yada bidiyon lokacin da motoci ke barin hanyar bayan samun labarin ‘yadda ‘yan ta’addan ke barna a yankin na jihar Neja.

The post ‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki a Yankin Jihar Neja appeared first on Arewa Agenda Hausa.