Dakta Iyorchia Ayu Archives - Arewa Agenda Hausa

Kwamitin Ayyukan PDP na Neman Dalilin Zaftare N10bn Zuwa N1bn da Jam’iyyar Tayi
Kwamitin Ayyukan PDP na Neman Dalilin Zaftare N10bn Zuwa N1bn da Jam’iyyar Tayi

Rikici ya sake ballewa a jam’iyyar PDP yayin da aka nemi wasu kudade Naira biliyan 10 aka rasa inda suka shiga.

Majiyoyi sun bayyana yadda ‘yan tawagar gwamnan Ribas Wike ke kokarin kawo tsaiko ga tafiyar Atiku a 2023.

Jam’iyyun siyasa a Najeriya na ci gaba da mai da hankali ga yadda za su tallata ‘yan takararsu gabanin zaben 2023.

Awanni 48 kafin fara gangamin kamfen na PDP, rikici ya sake barkewa a jam’iyyar kan yadda aka kashe kudin foma-foman da PDP ta siyar gabanin zabukan fidda gwani.

Kwamitin ayyukan PDP ne ke tado da wannan batu na sanin bahasin kashe Naira biliyan 10, inji rahoton The Nation.

Wasu mabobin NWC sun nuna damuwa game da yadda kudin ya zaftare daga Naira biliyan 10 zuwa Naira biliyan 1.

Batutuwan da ke fitowa sun ce, PDP na shirin ba dukkan mamban NWC da ke neman bahasi N28m domin rufe musu baki kan tado da sabon rikici a jam’iyyar.

Majiyoyi sun ce, mambobin na NWC sun ki karbar N28m, inda suka nemi a bayyana gaskiyar inda sauran kudin suka shiga.

Tawagar Wike ce ta kitsa komai

Akwai kuma maganganun da ke cewa, wannan matsin lamba na zuwa ne daga tsagin gwamna Nyesom Wike, kuma ana tunanin tado da batun zai kai ga tsige shugaban PDP na kasa Dakta Iyorchia Ayu.

Dan takarar mataimakin shugaba kasa na PDP, kuma gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa ya tsorata da barazanar ‘yan tawagar Wike, ya gana da tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki don yayyafa ma rikicin ruwa.

An ce Okowa ya damu matuka da yadda tawagar gwamna Wike ke kokarin ganin an samu baraka a tafiyar kwamitin kamfen din Atiku.

Kudin foma-foman takarar PDP a zaben 2023

Idan baku manta ba, PDP ta siyar da foma-fomanta na takarar kujerun 2023 a farashi kamar haka:

1. Dan takarar shugaban kasa – N40m

2. Dan takarar gwamna – N21m

3. Dan takarar sanata – N3.5m

4. Dan takarar majalisar wakilai ta kasa – N2.5m

5. Dan takarar majalisun dokokin jihohi – N600,000

Bincike ya nuna mambobin NWC sun shiga mamaki da damuwar inda PDP ta kai wadannan makudan kudade da aka tara.

Barazanar da mambobin NWC ke yi

A cewar wasu majiyoyi, wasu mabobin NWC na barazanar za su daina halartar ganawar kwamitin da kuma tsame kansu daga maganar kamfen din jam’iyyar, kamar yadda The Nation ta samo.

Mambobin sun kuma bayyana cewa, dan takarar shugaban kasan PDP Atiku Abubakar ya ba jam’iyyar kudade Naira biliyan 1 gabanin zaben fidda gwanin da aka gudanar.

Wata majiyar da ta nemi a sakaya sunata ta ce:

“Gabanin gangamin kamfen dinmu, komai a birkice yake a jam’iyyar saboda wasu mambobin NWC sun tada jijiyar wuya game da inda N10bn suka yi na foma-foman takara.

“Suna bukatar bahasi cikin gaggawa daga jam’iyyar.

Ina tunanin fushinsu ya samo asali ne daga bayanin da ya fita cewa, kudin da aka karba ya sauka da N10bn zuwa N1bn.”

The post Kwamitin Ayyukan PDP na Neman Dalilin Zaftare N10bn Zuwa N1bn da Jam’iyyar Tayi appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Ɗan takarar Gwamna a PDP a Jahar Osun ya yi Murabus Daga Jam’iyyar
Ɗan takarar Gwamna a PDP a Jahar Osun ya yi Murabus Daga Jam’iyyar

Ɗan takarar gwamna a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP a jihar Osun ya yi murabus daga kasancewarsa mamba.

Dakta Akin Ogunbiyi, jigo a PDP reshen Osun ya bayyana haka ne a wata wasika da ya aike wa shugaban jam’iyya na ƙasa.

Ogunbiyi ya fusata tun kafin fara fafatawa a zaben fidda gwani kuma ya sanar da janye wa awanni kafin bisa wasu dalilai.

Osun- Tsohon ɗan takarar gwamna kuma babban jigo a jam’iyyar hamayya PDP reshen Osun, Dr Akin Ogunbiyi, ya tsame kansa daga cikin jam’iyyar, kamar yadda Tribune ta rahoto.

Mista Ogunbiyi, ya sanar da matakin da ya ɗauka na barin PDP a wata wasikar murabus da ya aike wa shugaban jam’iyya na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu.

A cikin wasikar ta murabus, jigon PDP ya gode wa jam’iyya da mambobinta bisa, “Damawa da shi da kuma sauran harkoki na tsawon shekaru.”

Tsohon ɗan takarar kujerar gwamnan yace:

“Dan Allah ka amince da wannan wasiƙa a matsayin murabus ɗina daga jam’iyyar PDP a hukumance daga ranar 28 ga watan Maris, 2022.”

Abubuwan da suka faru kafin haka

Idan zaku iya tunawa, awanni kaɗan kafin fafata zaɓen fidda gwamni na ɗan takarar gwamna karkashin PDP, Dakta Ogunbiyi, ya sanar da janye wa daga cikin masu tseren tikiti.

Babban jigon PDP ya bayyana matsayarsa ne a ofishin yaƙin neman zaɓensa dake Ogo Oluwa, yankin Osogbo, babban birnin jihar Osun.

Da yake faɗin dalilin janyewarsa daga tseren, ya bayyana cewa ya gano akwai wata maƙarƙashiya da aka ƙulla tun daga Hedkwatar jam’iyya ta ƙasa na yin murɗiya a zaɓen.

Bugu da ƙari, ya ce tsagin Adeleke sun shirya murɗiya, cin mutunci da kuma ta da yamutsin da ka iya jawo rasa rayukan wasu masoyansa a wurin zaɓen.

The post Ɗan takarar Gwamna a PDP a Jahar Osun ya yi Murabus Daga Jam’iyyar appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Jam’iyyar PDP ta Fitar da ‘Dan Takarar Shugabancinta
Jam’iyyar PDP ta Fitar da ‘Dan Takarar Shugabancinta

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, tsohon shugaban majalisar dattawa, Dakta Iyorchia Ayu ya zama dan takarar shugabancin jam’iyar PDP, gabanin babban taron ta na kasa na ranar 31 ga watan Oktoba.

Fitowar Ayu ya biyo bayan awanni na ci gaba da tarurrukan da masu ruwa da tsaki na PDP na Arewa ke yi a Abuja cikin awanni 72 da suka gabata.

Karin bayani na nan tafe..

The post Jam’iyyar PDP ta Fitar da ‘Dan Takarar Shugabancinta appeared first on Arewa Agenda Hausa.