Abubakar Malami Archives - Arewa Agenda Hausa

EFCC ta Roƙi Kotu da ta ƙwace Kadarorin Malami
EFCC ta Roƙi Kotu da ta ƙwace Kadarorin Malami

FCT Abuja –Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta roƙi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da ta bayar da umarnin ƙwace kadarori 57 da ake zargin suna da alaƙa da Abubakar Malami.

Kotun ta bayyana cewa tana fatan bayan an kwace kadarorin daga tsohon babban lauyan ƙasa kuma Ministan Shari’a, a mika su zuwa hannun gwamnatin tarayya.

Jaridar Punch ta wallafa cewa wannan na kunshe a cikin wata takarda da lauyoyin EFCC suka gabatar ƙarƙashin jagorancin Jibrin Okutepa (SAN) da Ekele Iheanacho (SAN).

EFCC na son a kwace kadarorin Abubakar Malami

Daily Nigerian ta wallafa cewa EFCC ta shaida wa Mai Shari’a Joyce Abdulmalik cewa waɗanda ake ƙara sun kasa gabatar da hujjoji masu ƙarfi da za su sa a soke umarnin wucin gadi na ƙwace kadarorin da kotu ta bayar tun da farko.

Shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CS/20/2026 ta haɗa da Malami, Hajia Bashir Asabe da Abiru’ Rahman Abubakar Malami, tare da wasu kamfanoni da ake zargin suna da alaƙa da kadarorin.

EFCC ta ce ta gabatar da ƙarar ne bisa sashe na 17 na dokar zamba da sauran laifuka na 2006, tana neman kotu ta tabbatar da ƙwace kadarorin da ake zargin an samo su ne daga haramtattun hanyoyi.

Lauya Okutepa ya bayyana cewa wannan shari’a ce ta ƙwace kadara ba tare da hukuncin laifi ba, yana mai cewa kotu na da ikon doka ta amince da buƙatar.

Ya ce:

“Ba a gabatar da wani dalili mai gamsarwa ba da zai hana a ƙwace kadarorin gaba ɗaya ga gwamnatin tarayya.”

Abin da binciken hukumar EFCC ya gano

A cikin rantsuwar da jami’in EFCC Daniel Adebayo ya yi, ya ce hukumar ta samu ƙorafe-ƙorafe da dama kan zargin cin hanci, amfani da mukami ba daidai ba da kuma zamba a kan tsohon ministan.

Ya ce binciken ya haɗa da duba bayanan bankuna da na Babban Bankin Najeriya, da kuma bincike daga hukumomi kamar Hukumar CAC, FIRS, CCB da AGIS na Abuja.

Haka kuma an binciki rajistar filaye a jihohin Kebbi, Sakkwato da Kano, tare da tantance kadarorin a zahiri da ƙimanta su.

A cewarsa, kudin shigar Malami daga 2015 zuwa 2023 — har da albashi, alawus da kudin tafiye-tafiye — ba su kai darajar kadarorin da ake bincike ba.

Ya bayyana cewa Malami ya samu jimillar N89,664,000 a matsayin albashi, tare da N12,158,400 na alawus bayan barin aiki, sannan ya bayyana karɓar N253,608,500 a matsayin kudin tafiye-tafiye.

Sai dai EFCC ta ce yawancin kadarorin sun zarce waɗannan kudi, kuma wasu gine-gine ba su da izinin hukumomi musamman a Kano da Kebbi, lamarin da ake zargin an yi ne domin ɓoye asalin kudin da aka yi amfani da su.

An kuma zargi cewa an sayi wasu kadarorin ta hannun wasu mutane ko kamfanoni da ke da alaƙa da Malami.

Kotun ta sanya ranar 21 ga Afrilu, 2026 domin sauraron ƙarar, yayin da shari’ar ta samo asali daga umarnin wucin gadi da Mai Shari’a Emeka Nwite ya bayar a ranar 8 ga Janairu, 2026, inda aka ƙwace kadarorin na ɗan lokaci da darajarsu ta kai kusan Naira biliyan 213.2.

The post EFCC ta Roƙi Kotu da ta ƙwace Kadarorin Malami appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Gwamnatin Najeriya na Son Hana Hawa Babura
Gwamnatin Najeriya na Son Hana Hawa Babura

Gwamnatin Najeriya ta ce tana duba yuwuwar hana amfani da babura domin dakile ayyukan masu satar mutane da ‘yan ta’adda.

Ministan Shari’a kuma babban lauyan gwamnati Abubakar Malami shi ne ya sanar da haka a karshen taron majalisar tsaron kasar wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta yau Alhamis a Abuja.

A jawabin nasa ga manema labarai, ministan wanda ke tare da takwaransa na ma’aikatar cikin gida Rauf Aregbesola da kuma na ma’aikatar kula da harkokin ‘yan sanda Alhaji Maigari Dingyadi, ya ce, gwamnati na tunanin hana amfani da baburan da kuma aikin hakar ma’adanai.

Ya ce za ta yi hakan ne domin dakile hanyoyin da ‘yan ta’adda da masu satar mutane ke samun kudade da kuma jigilar kayayyakinsu.

Ministan ya bayyana cewa amfani da baburan na bai wa ‘yan ta’adda damar jigilar kudade da suke samu daga aikin hakar ma’adanai, su sayi makamai.

Sai dai kuma Malamin bai bayyana inda dokar za ta shafa ba, walau kasar baki Daya ko kuma wani bangare na kasar.

Da yake nasa jawabin ministan cikin gida Aregbesola ya ce duk da irin tarin bayanan sirrin da aka yi kafin harin da aka kai kan gidan yari na Kuje ranar 5 ga watan nan na Yuli, ‘yan ta’adda sun samu nasara saboda babu kudurin yakar su, kamar yadda ya ce.

Ya kara da cewana baw a Shugaba Buhari rahoton farko-farko na binciken da aka yi kan harin, tari da alkawarin cewa duk jami’in da aka samu da sakaci a aikinsa za a hukunta shi.

The post Gwamnatin Najeriya na Son Hana Hawa Babura appeared first on Arewa Agenda Hausa.

CPC da Suka Narke a APC su na so Mataimakin Tinubu ya Fito Daga Tsaginsu
CPC da Suka Narke a APC su na so Mataimakin Tinubu ya Fito Daga Tsaginsu

Akwai rabuwar kai tsakanin jagororin APC a kan wanda zai yi takarar mataimakin shugaban kasa.

Bangaren jam’iyyar CPC da suka narke a APC su na so mataimakin Bola Tinubu ya fito daga tsaginsu.

Yayin da ake kawo shawarar a dauki Kashim Shettima, akwai masu sha’awar Abubakar Malami.

Abuja – Lokaci ya karaso na zaben ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a zabe mai zuwa, jam’iyyar APC ta na ta lissafin abokin takarar Bola Tinubu.

Wani rahoto da ya fito daga Daily Trust a ranar Talata, 14 ga watan Yuni 2022 ya nuna cewa kai ya rabu tsakanin ‘yan bangarorin da suka taru, aka kafa APC.

Wata majiya ta shaida cewa mutanen tsagin CPC da ke jam’iyyar APC mai mulki za su tunkari shugaba Muhammadu Buhari kan batun tikitin zaben 2023.

Wadannan manya su na shirin haduwa da shugaban kasa da nufin ba shi shawarar ya fadawa Tinubu wanda zai dauka a matsayin ‘dan takarar mataimaki.

Ana kawo mutane 2 a lissafi

Sunayen da wadannan mutane za su kai fadar shugaban kasan sun kunshi Ministocin gwamnatin tarayya; Abubakar Malami da Sanata Hadi Sirika.

Malami SAN shi ne yake rike da kujerar Ministan shari’a na kasa kuma babban lauyan gwamnatin tarayya tun 2015, yana da karfi a gwamnatin nan.

Shi kuma Hadi Sirika shi ne Ministan harkokin jiragen saman Najeriya. Kafin zamansa karamin Minista, ya taba yin ‘dan majalisar wakilai da Sanatan Katsina.

Amma ana tunanin cewa shugaban kasar zai yi watsi da shawarar mutanen na sa kamar yadda ya yi a wajen zaben ‘dan takaran APC, ya ki goyon bayan kowa.

Jaridar ta rahoto majiyar ta na cewa Buhari zai bar Bola Tinubu ne ya zabi wanda zai yi aiki da shi.

Matsayar Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa ‘dan takarar shugaban kasar ya bar wuka da nama a hannun fadar shugaban kasa, a zaba masa duk wanda ya fi cancanta.

Majiyarmu wanda yana da kusanci da wani babban Gwamna a jam’iyyar APC ya shaida mana cewa fadar shugaban kasa ta na so ne Tinubu ya dauki Kirista.

The post CPC da Suka Narke a APC su na so Mataimakin Tinubu ya Fito Daga Tsaginsu appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Ba Daidai Bane Mika Kyari Kasar Amurka, Inji Lauyansa
Ba Daidai Bane Mika Kyari Kasar Amurka, Inji Lauyansa

Kotu ta sanya ranar da za a ji batun Abba Kyari kan yiwuwar mika shi Amurka ko ci gaba da zamansa a Najeriya.

Kasar Amurka dai a baya ta bukaci gwamnatin Najeriya ta mika Kyari domin gurfanar dashi a gaban kotu.

Wannan na zuwa ne bayan da wani bincike yace Kyari na da hannu a wata damfara da Hushpuppi ya yi a 2020.

FCT, Abuja – Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun Abuja, ya sanya ranar 29 ga watan Agusta domin yanke hukunci kan karar da ke neman tasa keyar DCP, Abba Kyari zuwa kasar Amurka domin yi masa shari’a kan wata damfara da ake zargin da hannunsa.

Ana zargin Abba Kyari da kulla harkalla da wani kasurgumin dan damfara, Abbas Roman (Huspuppi) da ke barnarsa a duniya, lamarin ya kuma ba ‘yan Najeriya da dama mamaki.

A ci gaba da jin batutuwan neman mika shi waje, alkalin ya tsayar da ranar ne bayan sauraran hujjoji akan karar da bangarorin da abin ya shafa suka bijiro dasu, rahoton Punch.

Ba daidai bane mika Kyari kasar Amurka, inji Lauyansa

Kyari wanda wani babban Lauyan Najeriya (SAN), Nureni Jimoh ya wakilci bayanansa, ya roki kotun da ta ki amincewa da bukatar mika shi Amurka bisa hujjar cewa bai aikata laifin da zai sa gwamnatin tarayya ta kai shi kasar Amurka ba da sunan hukunta shi.

Kyari ya sanar da kotun cewa fiye da shekara guda kafin a kama shi, ya rubuta wa AGF Abubakar Malami da Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP), Usman Alkali Baba wasika, inda ya sanar da su cewa ya bude sahar sadarwa da wanda ake zargin dan damfara ne, Ramon Abass.

A cikin wasiku guda biyu da aka mika a gaban kotu, Kyari ya bayyana cewa, manufar alakarsu ba komai bane face a baiwa Hushpuppi kwarin gwiwa da kuma jawo shi zuwa Najeriya inda tuni rundunarsa ke shirye don kwamushe shi.

Ban da haka, ya sanar da kotun cewa hukumomin Amurka sun taba yaba masa bisa jajircewar da yake nunawa wajen yaki da ‘yan damfarar yanar gizo, kamar yadda Channels Tv ta rawaito.

Ya kuma shaida wa kotun cewa tuhumar da ake masa na damfara da gwamnatin Amurka ta yi, ba laifi ba ne a karkashin dokar mike mutum waje, don haka bai kamata kotu ta bari a yi amfani da wannan lamari don mika shi Amurka ba.

Lauyan gwamnatin tarayya, Pius Akuta ya bukaci kotun da ta yi watsi da hujjojin wanda ake kara. Ya ce gwamnatin Amurka ta cika sharuddan karbar Kyari bisa tuhumar da ake yi masa da kuma bukatar mika shi kasar domin fuskantar shari’a.

The post Ba Daidai Bane Mika Kyari Kasar Amurka, Inji Lauyansa appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Abubuwan Alherin da na yiwa Al’ummar Jahar Kebbi – Abubakar Malami
Abubuwan Alherin da na yiwa Al’ummar Jahar Kebbi – Abubakar Malami

Dan takaran gwamnan Kebbi ya lissafa jerin abubuwan alherin da ya yiwa al’ummar jihar da yake son mulka.

Abubakar Malami yace yanzu yana kokarin mayar da mutum 500 masu kudi miloniya.

Malami, wanda shine Ministan Shari’a ya jaddada karyata rahotannin cewa ya rabawa deleget motoci.

Birnin-Kebbi – Antoni Janar na tarayya kuma dan takaran kujerar gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Malami, ya ce ta dalilinsa mutum sama da 500 sun zama miloniya a jihar.

Malami ya bayyana hakan ne a gidansa dake Birnin Kebbi yayinda ya karbi bakuncin kungiyar magoya bayansa makon da ya gabata, rahoton PremiumTimes.

Ya kara da cewa ya samawa matasa sama da 700 ayyuka.

A cewarsa:

“Mun samu nasarar samawa mutum 700 ayyukan yi. Mun gina rijiyar burtatsai sama da 200 a fadin jihar, muna taimakawa jihar wajen mayar da mutane 500 miloniya a jihar.”

“Mun taimakawa sama da mutum 6000 wadanda suka samu tallafin COVID-19 kowanne N550,000.”

The post Abubuwan Alherin da na yiwa Al’ummar Jahar Kebbi – Abubakar Malami appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Shugaba Buhari ya Umarci Dukkan Ministocinsa da ke Niyyar Takara a Zaben 2023 da su yi Murabus
Shugaba Buhari ya Umarci Dukkan Ministocinsa da ke Niyyar Takara a Zaben 2023 da su yi Murabus

Daga karshe Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci dukkan ministocinsa da ke da niyyar takara a zaben 2023 su ajiye aikinsu.

Lai Mohammed, Ministan Labarai da Al’adu ne ya sanar da hakan bayan taron FEC da Shugaba Buhari ya jagoranta a yau Laraba.

Mohammed ya ce Shugaba Buhari ya bawa ministocin wa’adin kwana biyar daga yau su mika murabus dinsu wato kafin ko ranar 16 ga watan Mayu.

FCT, Abuja – Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci dukkan ministocinsa da ke son yin takara a zaben 2023 da ke tafe su mika takardan murabus dinsu kafin ko ranar Litinin 16 ga watan Mayun 2022, Channels Television ta rahoto.

Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed ne ya sanar da hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Villa a Abuja.

Daga cikin ministocin da suka ayyana niyyarsu na takara akwai Rotimi Amaechi (Sufuri), Chris Ngige (Kwadago), Abubakar Malami (Shari’a), Godswill Akpabio (Neja Delta).

Shima hadimin shugaban kasa Tolu Ogunlesi ya tabbatar da umurnin na shugaban kasa ga ministoci masu son yin takara kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya ce:

“Yanzun nan: Dukkan ministocin fadar Shugaba Buhari da ke son yin takara za su yi murabus kafin ko ranar 16 ga watan Mayun 2022.”

The post Shugaba Buhari ya Umarci Dukkan Ministocinsa da ke Niyyar Takara a Zaben 2023 da su yi Murabus appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta Iya Saka Dokar Ta-ɓaci a Anambra Saboda Zaɓe
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta Iya Saka Dokar Ta-ɓaci a Anambra Saboda Zaɓe

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta iya saka dokar ta-ɓaci a Jahar Anambra da ke kudancin ƙasar domin tsaurara tsaro yayin gudanar da zaɓen gwamna a watan Nuwamba.

Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ranar Laraba wanda Shugaba Buhari ya jagoranta.

Malami ya ce gwamnati za ta yi dukkan mai yiwuwa domin ta tabbatar da tsaron lafiyar mutane da dukiyoyinsu “idan gwamnatin jahar ta gaza yin hakan”.

“Idan aka samu tabbacin cewa gwamnatin jaha (Anambra) ba za ta iya kare rayukan mutane ba ta hanyar tabbatar da doka da oda gwamnatin tarayya za ta ɗauki mataki kuma za mu iya saka dokar ta-ɓaci,” a cewarsa kamar yadda Channels TV ta rawaito.

Matakin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun rahotannin kashe-kashe a Anambra da kuma yankin kudu maso gabashin Najeriya.

An kashe mutum fiye da 10 a ‘yan makonnin da suka wuce a Anambra. Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta saka 6 ga watan Nuwamba domin gudanar da zaɓen gwamna a jahar.

The post Gwamnatin Tarayya ta ce za ta Iya Saka Dokar Ta-ɓaci a Anambra Saboda Zaɓe appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Gwamnatin Tarayya ta yi Nasarar Ragargazar ‘Yan Boko Haram da ‘Yan Bindiga – Abubakar Malami
Gwamnatin Tarayya ta yi Nasarar Ragargazar ‘Yan Boko Haram da ‘Yan Bindiga – Abubakar Malami

Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya ce an karya lagwan ‘yan ta’adda a Nigeria.

Malami ya yi wannan jawabin ne yayin zantawa da manema labarai a New York.

AGF din ya ce kama masu daukan nauyin ta’addanci da aka yi ne ya haifar da nasarorin.

New York – Attoni Janar na Nigeria, AGF, kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya yi ikirarin cewa an yi nasarar ragargazan ‘yan Boko Haram da ‘yan bindiga kwarai da gaske, rahoton NewsWireNGR.

Malami ya bayyana hakan ne a birnin New York ta Amurka yayin da ya ke zantawa da manema labarai. Ya kuma yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya ta yi nasarar wurin ‘binciko da gano wasu manyan mutane’ da ake zargi da daukan nauyin ‘yan ta’adda a kasar.

A cewar babban jami’in doka na kasar, batun daukan nauyin ta’addanci lamari ne da ake aiki a kansa kuma baya son ya yi magana kan abin da ba a kammala bincike a kansa ba.

Sai dai ya ce:

“Abu daya da zan iya tabbatarwa shine, duba da irin kamen da aka yi, an karya lagwan masu daukan nauyin ta’addanci da ‘yan ta’adda don haka za a samu cigaba a bangaren dakile ‘yan ta’adda.

“Kana iya gani karara cewa muna samun nasarori kan yaki da Boko Haram, wanda ke nuna cewa ana karya lagwan ‘yan ta’addan.”

Ya cigaba da cewa:

“Tuni an karya lagwan ‘yan ta’addan Boko Haram sosai kuma kana iya ganin abin da ke faruwa a yankin Arewa maso Yamma da ya shafi ‘yan bindiga.

“Suma ‘yan bindigan an karya lagwan su sosai. Dukkan wannan sakamako ne na abin da muka yi.”

The post Gwamnatin Tarayya ta yi Nasarar Ragargazar ‘Yan Boko Haram da ‘Yan Bindiga – Abubakar Malami appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Gwamnatin Tarayya za ta kwato fam 200m da Aka Sace Aka Boye a Kasar Amurka
Gwamnatin Tarayya za ta kwato fam 200m da Aka Sace Aka Boye a Kasar Amurka

Gwamnatin tarayya ta bayyana yunkurinta na kwato wasu kudaden da aka sace su mallakin kasar.

Wannan na zuwa ne yayin da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya ya ke tattaunawa a wani taro a Amurka.

Ya bayyana cewa, gwamnati na shirya wasu hanyoyi don tabbatar da kwato kudaden kasar nan cikin sauki.

New York, US – Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kwato fam miliyan 200 da aka sace aka boye a Amurka, yayin da gwamnatin ke shirin fara kwato kadarori mallakin kasar.

Yunkurin ya fito ne ta bakin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami wanda ke magana a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya a New York ta kasar Amurka.

Channels Tv ta tattaro cewa, da yake magana kan yaki da cin hanci da rashawa da kwararar kudade a kasar, Malami ya ce:

duba yiwuwar dawo da fam miliyan 200 da wasu kari amma to, hakan ba yana nufin babu wasu kadarorin da ake alaka da su ba, dangane da sauran kasashen duniya da suka hada da Ireland.

“Muna bibiyar kadarori da yawa a duk fadin duniya sannan muna da niyyar shirya karin tarurrukan da suka shafi dawo da kudade a Burtaniya wanda ke da alaka da wasu mutane.”

AGF ya ce ba zai so ya kara bayyana dabarun da gwamnatin tarayya za ta bi wajen dawo da kudade ba, amma ya lura cewa:

“Gwamnati na kokarin tattara karfin duniya da ke da alaka da matakai da hanyoyi, dangane da saukake lamurra ga kasashe wajen dawo da kadarori cikin sauki.”

Ya kara da cewa gwamnati ta himmatu ga yakin da take yi da cin hanci da rashawa kuma ta hanyar fadada shimfida tarkon ta ga wadanda ke boye da kudaden da aka sace ko aka tsallakar.

Majalisa ta nemi a bata rahoto kan kadarorin Janar Abacha da hankali zai dauka

Majalisar wakilai a ranar Litinin 20 ga watan Satumba ta nemi Kwamitin Aiwatarwa ta Shugaban Kasa (PIC) kan kadarorin da filaye mallakar gwamnati da su gabatar da rahotannin dukkan kadarorin da aka kwace daga tsoffin shugabannin Najeriya.

‘Yan majalisar sun fi mayar da hankali musamman kan Janar Sani Abacha wanda Gwamnatin Najeriya ta kwato kaddarori da kudade da dama daga turai da aka ce mallakinsa ne, Daily Nigerian ta rawaito.

Dan majalisar wakilai Ademorin Kuye, shugaban kwamitin wucin gadi kan kadarorin da aka yi watsi da su ya ce majalisar tana bukatar rahoton dukkan kadarorin da aka kwato daga hannun shugabanni, musamman Janar Abacha.

Ya fadi haka ne lokacin da Babban Sakataren PIC ya bayyana a kwamitin a babban birnin tarayya Abuja.

The post Gwamnatin Tarayya za ta kwato fam 200m da Aka Sace Aka Boye a Kasar Amurka appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Kutsen DSS a Gidan Igboho: Kotun Jahar Ibadan ta Yarda da Bidiyoyin Shaida da Aka Mika Gaban ta
Kutsen DSS a Gidan Igboho: Kotun Jahar Ibadan ta Yarda da Bidiyoyin Shaida da Aka Mika Gaban ta

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Ibadan ta aminta da bidiyoyin da lauyan Igboho ya mika na kutsen DSS a gidansa.

Har ila yau, kotun ta amince da cewa bidiyon da DSS ta mika ta lalata shi, lamarin da yasa ta fara kare kan ta.

Sai dai kuma lauyoyin Malami da na DSS sun ce ya zama dole a je a gwada jinin da aka gani a bidiyon don tabbatar da cewa na mutum ne ko dabba.

Ibadan – Wata babbar kotun da ke zama a Ibadan a ranar Talata ta yarda da bidiyoyin shaida da aka mika gaban ta kan zargin kutsen da jami’an tsaron farin kaya suka yi a gidan Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho a ranar 1 ga watan Yuli.

Kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa, lauyan Igboho, Yomi Aliyu, SAN, ya mika kara tare da bukatar a biya shi diyyar biliyan N500 daga wurin antoni janar na tarayya, Abubakar Malami, SSS da kuma daraktan DSS na jahar Oyo a kan kutse.

Tun farko Aliyu ya sanar da kotun cewa, an kutsa gidan wanda ya ke karewa da motocinsa kuma an ragargaza tare da kashe wasu mutum biyu.

A zaman ranar Talata, Mai shari’a Ladiran Akintola, ya yarda da shaidun da aka mika gabansa bayan Aliyu ya bayyana asalin dalilin da yasa suka gurfana a gaban kotu, Daily Nigerian ta wallafa.

Akintola ya sake yadda da bidiyon da lauyan DSS ya mika, T. A. Nurudeen, inda Igboho ke barazanar kafar jamhuriyar Oduduwa, balle wa daga Najeriya da kuma kiran Yarabawa da su kare kan su da layu da bindigogi.

Kotun ta bukaci a saka bidiyoyin biyu a bayyane a kotu kamar yadda lauyan Igboho da na SSS suka bukata.

A yayin jawabi ga kotun bayan an saka bidiyoyin, lauyan AGF, Abdullah Abubakar, ya ce ba bu shaida a gaban kotu kan cewa jinin da aka gani a bidiyon ko na mutum ne.

Abubakar ya kara da cewa, babu wani abu a bidiyon da ya nuna cewa gidan da aka kutsa na Igboho ne ko kuma kutsen ya na da alaka da AGF. Don haka ya yi kira ga kotun da ta yi watsi da duk wata shaida tare da korar karar da aka shigar.

Lauyan SSS, Nurudeen, ya ce tabbas ya zama wajibi likitoci masana halittar jini su tabbatar da cewa wannan jinin na mutum ne ba na mage ba.

Akintola ya dage sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Satumba domin yanke hukunci.

The post Kutsen DSS a Gidan Igboho: Kotun Jahar Ibadan ta Yarda da Bidiyoyin Shaida da Aka Mika Gaban ta appeared first on Arewa Agenda Hausa.