Ba Daidai Bane Mika Kyari Kasar Amurka, Inji Lauyansa

Kotu ta sanya ranar da za a ji batun Abba Kyari kan yiwuwar mika shi Amurka ko ci gaba da zamansa a Najeriya.

Kasar Amurka dai a baya ta bukaci gwamnatin Najeriya ta mika Kyari domin gurfanar dashi a gaban kotu.

Wannan na zuwa ne bayan da wani bincike yace Kyari na da hannu a wata damfara da Hushpuppi ya yi a 2020.

FCT, Abuja – Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun Abuja, ya sanya ranar 29 ga watan Agusta domin yanke hukunci kan karar da ke neman tasa keyar DCP, Abba Kyari zuwa kasar Amurka domin yi masa shari’a kan wata damfara da ake zargin da hannunsa.

Ana zargin Abba Kyari da kulla harkalla da wani kasurgumin dan damfara, Abbas Roman (Huspuppi) da ke barnarsa a duniya, lamarin ya kuma ba ‘yan Najeriya da dama mamaki.

A ci gaba da jin batutuwan neman mika shi waje, alkalin ya tsayar da ranar ne bayan sauraran hujjoji akan karar da bangarorin da abin ya shafa suka bijiro dasu, rahoton Punch.

Ba daidai bane mika Kyari kasar Amurka, inji Lauyansa

Kyari wanda wani babban Lauyan Najeriya (SAN), Nureni Jimoh ya wakilci bayanansa, ya roki kotun da ta ki amincewa da bukatar mika shi Amurka bisa hujjar cewa bai aikata laifin da zai sa gwamnatin tarayya ta kai shi kasar Amurka ba da sunan hukunta shi.

Kyari ya sanar da kotun cewa fiye da shekara guda kafin a kama shi, ya rubuta wa AGF Abubakar Malami da Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP), Usman Alkali Baba wasika, inda ya sanar da su cewa ya bude sahar sadarwa da wanda ake zargin dan damfara ne, Ramon Abass.

A cikin wasiku guda biyu da aka mika a gaban kotu, Kyari ya bayyana cewa, manufar alakarsu ba komai bane face a baiwa Hushpuppi kwarin gwiwa da kuma jawo shi zuwa Najeriya inda tuni rundunarsa ke shirye don kwamushe shi.

Ban da haka, ya sanar da kotun cewa hukumomin Amurka sun taba yaba masa bisa jajircewar da yake nunawa wajen yaki da ‘yan damfarar yanar gizo, kamar yadda Channels Tv ta rawaito.

Ya kuma shaida wa kotun cewa tuhumar da ake masa na damfara da gwamnatin Amurka ta yi, ba laifi ba ne a karkashin dokar mike mutum waje, don haka bai kamata kotu ta bari a yi amfani da wannan lamari don mika shi Amurka ba.

Lauyan gwamnatin tarayya, Pius Akuta ya bukaci kotun da ta yi watsi da hujjojin wanda ake kara. Ya ce gwamnatin Amurka ta cika sharuddan karbar Kyari bisa tuhumar da ake yi masa da kuma bukatar mika shi kasar domin fuskantar shari’a.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here