Ƴan Sanda Sun Dakile Yunkurin Garkuwa a Katsina, Sun Ceto Ma’aurata

 

Rundunar ƴansandan jihar Katsina ta ce ta dakile wani yunkurin garkuwa da mutane, inda suka ceto mutane da lamarin ya so ya ritsa da su.

Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴansandan jihar, ASP Abubakar Sadiq ya fitar ranar Laraba, ta ce sun samu nasarar ce bayan samun wani rahoto da dare a ranar Litinin cewa wasu da ake zargi ƴan bindiga rike da muggam makamai sun kai hari kauyen Hayin-Dam da ke karamar hukumar Kankara.

Ya ƙara da cewa yayin harin, ƴan bindigar sun shiga gidan wani mutum mai suna Kabir Magaji, mai shekara 35, ind suka yi yunkurin garkuwa da shi tare da matarsa.

“Bayan samun rahoton abin da ke faruwa, nan take muka haɗa jami’ai zuwa wurin, suka yi artabu da ƴan bindigar,” in ji sanarwar.

ASP Sadiq ya ce daga bisani ne suka samu nasarar kuɓutar da waɗanda aka yi niyyar garkuwa da su waɗanda suka kasance ma’aurata ba tare da wani rauni ba.

Sai dai ya ce ƴan bindigar sun samu damar tserewa kuma ana ci gaba da farautarsu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here