ALLAH ya yi wa Muhammad Sani Umar Kalgo Rasuwa

Manyan mutane da ma su fada a ji a jihar Kebbi sun halarci jana’izar Muhammad Sani Umar Kalgo.

Marigayi Kalgo ya rasu da safiyar ranar Talata bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

An yi sallar jana’izarsa a babban masallacin kasa da ke birnin tarayya, Abuja.

Tsohon mamba a majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Birnin Kebbi, Kalgo, da Bunza, Muhammad Sani Umar Kalgo, ya rasu yana da shekaru 70 a duniya bayan gajeriyar jinya.

An yi Sallar jana’izarsa a Babban Masallacin kasa da ke birnin tarayya, Abuja.

Marigayi Kalgo ya taba neman takarar kujerar gwamnan jihar Kebbi gabanin zaben shekarar 2015.

Manyan mutane da suka hada da tsofin gwamnoni, ministoci, da manyan ‘yan siyasa da masoya da magoya daga jihar Kebbi da fadin kasa.

Daga cikin manyan mutanen da suka halarci jana’izarsa akwai gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, Sanata Adama Aliero, tsohon ministan tsaro, Dakta Bello Halliru.

Tsohon ministan aiyuka na musamman, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), Honarabul Kabiru Tukura, Alhaji Suleiman Muhammad Argungu (Jarman Kabi) da sauransu.

An haifi marigayi a ranar 15 Na watan Mayu, shekarar 1950, a karamar hukumar Kalgo a jihar Kebbi.

Marigayin ya rayu da mace daya da ‘ya’ya biyar da suka hada da kwamishinan kasafi da tsarin tattalin arziki na jihar Kebbi, Dakta Abba Sani Kalgo.

VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here