Ƴan Bindiga Sun Kashe Jami’an Ƴan sandan 2 a Jihar Kaduna
Rundunar ƴansandan jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce jami’anta sun ceto mutum tara da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Birnin Gwari.
Sai dai rundunar ƴansandan ta ce a yayin da jami’anta ke kan hanyar dawowa daga ceto mutanen, wasu ƴanbindigar sun yi musu kwanton ɓauna inda suka harbi jami’ai biyu waɗanda daga baisani suka rasu.
Read Also:
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 24 ga Yunin 2026 bayan samun sahihan bayanan sirri cewa kimanin ƴanbindiga kusan 15 ɗauke da makamai sun kai hari a ƙauyen Unguwan Sa’idu da ke kusa da Birnin Gwari, inda suka yi garkuwa da wasu mutane daga gonakinsu.
Sanarwar ta ce jami’ansu tare da haɗin gwiwar ƴan banga sun yi artabu da maharan, lamarin da ya tilasta wa ƴanbindigan tserewa cikin daji a kan babura bayan sun bar mutane 9 da suka yi garkuwa da su.






