Fim din Ali Nuhu, “Bana Bakwai” Ya Sauya Akalar Fina Finan Kannywood
Musa Sani Aliyu
AREWA AGENDA HAUSA – Shekara ta 2020 tazo da abubuwa dayawa marasa dadi ta fuskoki da dama, kama daga annobar cututtuka zuwa ga durkushewar kasuwanci, dama al’amura bila adadin.
Masana’antar fina finai  itama lamarin abun ya shafeta haikan. Muna daf da fita daga cikin shekarar, tsulum! sai ga kayatattun fina finai masu kayatarwa kamar Bana Bakwai na fitar burgu. Fim din Bana Bakwai wanda FKD production ce ta kawo wa masu kallo, fim ne wanda yasha bambam da fina finan masana’antar ta Kannywood da aka saba gani.
Yayin shirya fim din Bana Bakwai
Abubakar Bashir Maishadda, Nazifi Asnanic, Khalid Yusuf Kherlydo su suka dauki nauyin fim din, sai kuma Ali Nuhu ya yi labarin tare da bada umarni.
Bana Bakwai fim ne da akai duba na tsanaki, kazalika akai la’akari tare da zakulo al’amuran da suke damun Najeriya, kama daga   matsalar rashin aikin yi da matsalolin dayake haifarwa, cin zarafin yara, cin hanci tsakankanin jami’an tsaro da ‘yan siyasa, dasauran su, musamman a yankin Arewa.
“Fim din kusan awa biyu, a iya cewa yayi nuni ga ‘yar manuniyar haska hasken fitilar yadda hobbasar matasa ke shafar cigaban kasa,ta hanya mai kyau ko akasin haka. “Inji Daya daga cikin masu sharhin fim din.
Manyan jarumai kwararu kamar su, Saddiq Sani Saddiq, Nafisa Abdullahi, Lawan Ahmad, Abdul M Shareef, Ramadan Booth, Shuaibu Lawan, Tijjani Asase, Hajara Usman, Falalu Dorayi, su suka fito a ciki.
“Kwararren” mai bada umarni, Ali Nuhu ya fito a  bayyane ya jaddadawa duniya bajintar sa da kwarewar sa a fagen kirkira, da karbar yanayin sauyi na cigaban fikira a muhallinta, cikin  wani salo da usulubin rashin gazawar sassarfar nishandartar da masoyan sa ta kowane janabi, a duniyar shirya fina finan Kannywood.
Jarumai suna taka rawar gani a fim din
Ali Nuhu ya bayyana  cewar ya zama wajibi a irin martarbar sa a matsayin mai shirya fina finai yabada gudunmuwa ga al’umma ta hanyar yin fina finai wanda ake akwai nishadi a ciki, amma tsarme a ciki da ilimantarwa ba zallan nishadi ba kawai. “Na karanci ‘Transmedia Story Telling’ a Jami’ar Kudancin Kalifoniya dake Amurka, na fahimci fina finan mu na da nakasun fito da abubuwan dake shafar al’umma na yau da gobe bisa zamantakewar su ta yau da gobe. Tun daga wannnan lokaci na daukarwa kaina cewa zan cigaba da yin Fina finai da zasu dinga nuni ga wani madubi zuwa ga al’umma, fim dina na baya ‘ Karki Manta Dani’ nayi shi akan matsala da illar  shan miyagun kwayoyi, sannan nayi wannan akan matsalar harkar daba da sauran su,” Ali Nuhu yake fada cike da farin ciki, yayin da yake zantawa da Arewa Agenda a yayin kallon tsokaci da aka shiryawa ‘yan jarida,wannan shine yin hakan na farko a masana’antar.
Bana Bakwai nagartacce kana kayataccen fim ne da ya nuna dabia irin ta alakar dan’adam da wasu laifuka a rayuwar mu, tare da aibunsu,ya bude labulen nishadantarwa a lokaci guda gami da iliminatarwa, fim din ya zama kamar wata manhajar wayar dakai hakika. “Abunda ya kayatar dani  Fim dinnan shine yadda akai  nuni da cewar masu shirya fina finai yanzu a masana’antar suna chanja layi daga zallar fina finan soyayya da aka fiya yi zuwa yin fina finan da suke da ma’ana sosai kuma suke kara wayar da kan masu kallo.” A cewar Baba Lawal, daya cikin daga wanda suka halarci taron sharhi kan Fim din.
In akai duba zuwa  sauran fina finai na baya a masana’antar, shakka babu za a aminta cewar akwai sauye sauye da cigaba masu yawa da aka samu musamman a bangaren Kyamara, haske da sauransu. Kalamai da maganganu sun dace da yanayin da akai fim din.
Ali Nuhu tare da abokan aiki yayin da yake ba da Umarnin fim din
“A banganren shiga da yanayi na kayan da aka saka a fim din, hakika zan iya cewa anyi kokari matuka, domin ‘yan daba sun Yi kama da Yan daba, ‘yan siyasa anyi musu kwalliyar da ta dace dasu suma kwarai da gaske. Zaren labarin shima yayi dai dai gwargwado, duba ga yadda aka tabo abubuwa da halayen  da muka tsinci kanmu yanzu a ciki. Fim din sakon shi bayyananne ne ta yadda kowane mai hankali zai gane ina fim din ya dosa. Hakika fim din yana dauke da sinadarin rike dan kallo da saka shi a tafkin zakuwar cigaba da son ganin mai ke faruwa, misali son sanin waye ya kashe wani dan siyasa a farkon fim din, sannan mene karshen kaddarar ‘yan kungiyar ‘Bana Bakwai’.” Inji Baba Lawal.
A faifai fim din ya bayyana yadda Jami’an tsaro ke cin amanar kasa,ta hanyar karbar cin hanci( musamman ‘yansanda kamar yadda aka nuna a Fim din) amma tare da haka ana samun nagari daga ciki wanda suke kokarin yin gaskiya a kowane hali. Fim din ya sake bayyana karara yadda tsagin ‘yan jarida suke taka irin rawar su, ta hanyar zama masu saka ido akan al’amuran al’umma domin zama tsani ko wata gada tsakanin su da hukumomi, da tasirin yadda aikin su ke bankado ashsha domin daukar matakan da suka dace ga masu laifi.
Har ila yau yayi nuni da yadda iyaye ya kamata su dinga mu’amalar data dace da ‘ya yan su, rashin hakan na turo ya zuwa kwazazzabon aikata laifuka marasa kyawu, daka iya shafar al’umma ta hanya mara kyau.
Fim din yayi nuni da yadda sha’anin almajiranci yake, ya kuma haska wasu boyayyun abubuwan dake zama sabubban  jawo rashin lumana a tsakanin al’umma wanda suka hadar da rashin aikin yi, kyarar yara ga ‘yaya saboda rashin abun yi, illar duhun jahilci da kuma rashin wadataccen ilimi.
Akwai wasu ‘yan kura kurai da ba a rasa ba wanda muka ganosu a cikin wannan Fim, misali akwai sin din da aka nuna wata matashiya dauke da shudin kaya a inda take fayyacewa Lalla wasu bayanan sirri akan kungiyar Bana Bakwai, kuma ba a nuna wata alaka tsakanin su da Lallan ba, a cikin Fim din ba a nuna inda suke da alaka ba. Akan wannan, Ali Nuhu yace wannan ba wani bakon abu bane a Fim.
“In ka yi kallo na tsanake, mun nuna alakar su. Kuma gaskiya a Fim akwai abun da muke cewa ‘Limitation of Subject’ ma’ana  baza kaita nuna yadda akai komai da komai da haduwar kowa da kowa a cikin Fim ba, wannan zai ja dogon lokaci Fim din ya kare ba a ma isar da sakon da ake so a isar ba.” Ali Nuhu ya fada yayin da yake karin haske.
Wani kuskure da muka kara cin karo dashi ya hadar da wani sin inda aka caka wa wani mutum wuka aka kuma harbeshi, lokacin da yansanda suka halarci wurin da akai kisan, wukar da akai kisan da ita bamu ga jini a jiki ba, kuma ya kamata ace an nuna yadda yadda ya kamata ayi da salon zamani na DNA,wato sanin tambarin yatsu ko wani abu makamancin haka.
“Wajibi ne asamu kura kurai da nakasu, amma muna kokari mu yi amfani da abubuwan da muke dasu a kasa domin inganta aiki, kuma zamu cigaba da wannan kokari,bazamu gaza ba.” Ali Nuhu ya tabbatar.
Yayin tambihi kan ko Fim din zai iya fuskantar kalubale duba ga yadda an fito da hakikanin gaskiyar yadda abubuwa suke tafiya musamman a siyasance a kasar nan, Ali Nuhu ya bayyana babu wata gargada domin Fim din anbi dukkan ka’dojin da suka dace a hukumance.
“Koda mutum yaga wani abu da yai kama da wani abu da yake yi, to arashi ne, kuma dafatan zai dauki darasin da ake fata na a gyara”. Ali Nuhu ya jaddada.
Fim din yana dauke da kwararrun jarumai a ciki, Sarki Ali Nuhu ya nuna bajinta haikan da kwarewa. Film din Bana Bakwai zai fita  Sinima rannan 25 ga watan December 2020.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here