Babu Wanda Zai Shigo da Haramtatun Kaya Sai Mun Gane – Ministan Harkokin Cikin-Gida
Gwamnatin Najeriya ta ce bude iyakoki ba zai bada damar shigo da shinkafa ba.
Rauf Aregbesola yace sam ba za a bari a shigo da kayan waje da aka haramta ba.
Ministan yace an kafa na’urar MINARS a kan iyakokin tudu saboda fasa-kauri.
Ministan harkokin cikin-gida, Rauf Aregbesola, yace duk da bude iyakokin tudu da aka fara yi, babu maganar shigo da shinkafa daga ketare.
Jaridar Punch, ta rahoto Ministan yana wannan bayani a ranar Asabar lokacin da ya gana da ‘yan jarida.
Read Also:
Rauf Aregbesola da ya ke magana a garin Ilesa, ya ce akwai fasahohin da za su sa a gano shinkafa duk yadda aka yi kokarin shigo da ita a boye.
“Mun kawo wata fasaha wanda ake kira MINDARS, a iyakoki hudu da mu ka bude. MIDARS zai yi wa duk wanda ya shigo cikin Najeriya rajista.”
ace: “Idan MINDARS ta yi wa mutum rajista, har abada an san da zaman shi, don haka babu wanda ya isa ya shigo Najeriya ba tare da an gane ba.”
Mai girma Ministan ya bayyana cewa an bude iyakokin tudun ne domin mutane su shigo cikin kasar, sannan a rika cinikin kayan Afrika ta yamma.
“Kayan da mu ka hana shigo da su sune na waje. Ana cin shinkafar waje ne a Najeriya da kasar Afrika ta yamma kawai..” Ministan ya yi karin-haske.
“Bude iyakokin bai bada damar shigo da kayan da aka haramta ba, irinsu tsuntsaye, shinkafa da kwayoyi, makamai, makudan kudi ba.” Inji Aregbesola.