Me Akpabio ya ce kan Rashin Tsaro?
FCT, Abuja – Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi magana kan karuwar matsalar rashin tsaro.
Akpabio ya yi zargin cewa karuwar rashin tsaro da ake samu a faɗin Najeriya kwanan nan yana da nasaba da siyasa da kuma babban zaɓen 2027 mai zuwa.
Jaridar Vanguard ta ce Akpabio ya bayyana haka ne a ranar Talata, 14 ga watan Afirilun 2026 yayin jawabin taya murna a wajen kaddamar da babban ofishin hukumar tara kudaden shiga ta ƙasa (NRS).
Me Akpabio ya ce kan rashin tsaro?
Ya bayyana cewa wasu ’yan siyasa ne ke ɗaukar nauyin tashe-tashen hankula domin dakile damar sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu.
“Kuna ganin rashin tsaro a yau, har ma ƙaruwa yake yi saboda zaɓe na gabatowa. Da zaran an gama zaɓe, a cikin makonni biyu na farko ba za ku sake jin ƙarar bam ko guda ɗaya ba.”
“Domin mutane ne ke ɗaukar nauyin hakan don shagaltar da ku; ba su san abin da za su yi ba, sai su ce wannan mutumin (Tinubu) yana da ƙwarewa sosai a fannoni da dama.”
– Godswill Akpabio Akpabio ya yi maganar farin jinin Tinubu
Read Also:
Ya yi nuni da abin da ya kira ƙaruwar goyon baya na siyasa da shugaban ƙasar ke samu, inda ya nuna cewa gwamnoni da dama sun dawo ƙarƙashin inuwar Tinubu tun bayan 2023, jaridar Daily Trust ta dauko rahoton.
“Gwamnoni suna son sa ne saboda yana kula da jihohinsu sosai. Ya shigo da gwamnoni 18, amma a yau yana da kusan gwamnoni 32 a ƙarƙashinsa cikin 36. Don haka, a ina muke?”
– Godswill Akpabio Shugaban majalisa ya soki ‘yan adawa
Ya kuma yi magana game da takaddamar da ta shafi wani shafin X da ake zargin shugaban hukumar INEC, Joash Amupitan, ne ke amfani da shi, inda ya yi watsi da zargin nuna son kai a harkar zaɓe.
“Yaya za ku ci zaɓe alhalin ba ku da tsari? Babu wata jam’iyyar siyasa da take zaune lafiya a ƙasar nan. Sai su sauya sheka su koma suna sukar mutanen da za su gudanar da zabe.”
“Sai suka fito da wani saƙon X inda shugaban INEC ya ce, ‘Nasara tana nan tabbas,’ amma bai ce nasarar ta APC ce ko ta PDP ba.”
– Godswill Akpabio
Wannan bayani na Akpabio na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar fargaba kan tsaro a faɗin ƙasar, biyo bayan jerin tashe-tashen hankula da suka faru a kwanakin nan.













