An Ceto Mutane 10 da Gini ya Rufta da su a Legas
An ceto mutum 10 da ransu bayan wani ginin bene ya rufta da su jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya
Lamarin ya faru ne a kan titin Old Ojo Road kusa da tashar motar Alakija da ke kan babbar hanyar Legas zuwa Badagry, inda rahotanni suka ce har yanzu ana ci gaba da bincike domin gano ko akwai wasu da suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan ginin.
Read Also:
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar kashe gobara ta jihar Legas ta ce ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:37 na safe, inda ta tura jami’anta zuwa wurin da lamarin ya faru.
Babbar daraktar hukumar a jihar Legas, Margaret Adeseye, ta tabbatar da cewa an ciro mutum 10 da rai daga cikin ɓaraguzan ginin.
“Waɗanda aka ceto sun samu raunuka daban-daban, kuma an miƙa su ga likitoci domin duba lafiyarsu,” in ji ta.
Ta ƙara da cewa ana ci gaba da aikin ceto yayin da jami’ai ke binciken wurin domin gano ko akwai wasu da suka rage a ƙarƙashin ginin.
Hukumomi sun ce har yanzu ba a gano musabbabin ruftawar ginin ba, amma za a fara bincike da zarar an kammala aikin ceto






