Gwamnan Kano ya Kafa Kwamitin Yaƙi da Miyagun ƙwayoyi a Faɗin Jihar

 

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa wani kwamiti na musamman domin yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da safarar su a jihar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta ce an ɗauki matakin ne domin magance matsalar da ke addabar yawancin matasa a jihar.

Daga cikin ayyukan da kwamitin zai fi maida hankali su ne gano manyan wuraren da ake hada-hadar miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar, domin kai samame da kama waɗanda ake zargi.

Sanarwar ta ce an kuma ɗora wa kwamitin alhakin tattara bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro, gano hanyoyin safarar miyagun ƙwayoyi da kuma ƙarfafa wa al’umma yadda za su riƙa kai rahoton ayyukan da ake zargi na da alaƙa da miyagun ƙwayoyi ko ɓata gari.

Bugu da ƙari, kwamitin zai yi aiki tare da ɓangaren shari’a domin gaggauta yin shari’o’in da suka shafi miyagun ƙwayoyi da yanke hukunci.

Tsohon shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar, Muhuyi Magaji Rimingado ne zai shugabanci kwamitin.

Akwai kuma wakilai daga hukumomin tsaro irinsu NDLEA, DSS, ƴan sanda, NSCDC, Kwastam da kuma wakilai daga ma’aikatun gwamnati da sarakuna da malamai da ƙungiyoyin farar hula.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here