Jaruma Rahama Sadau Zata Fito A Fim Din Indiya

 

Daga Musa Sani Aliyu

Fitacciyar jarumar nan wato Rahama Sadau, wadda sunanta ya zagaya kowane lungu da sako na masana’antar shirya fina finai ta Kannywood har ma da Nollywood.

ba shakka labarin da muka samu daga’ Labaran Kannywood Twitter’ in ya rikide ya zama hakika, to babu digon shakka bare jirwayen tantamar cewar jaruma Rahama Sadau itace farkon wadda zata fara taka rawa a masana’antun Fina finai guda uku reras kuma jeras a sashen yammacin afrika baki daya, Kwarai kuwa!

Kai tsaye wannan yana da nasaba da hango jarumar da mukayi a kasar Indiya tare da fitacce,kwararre kana hazikin mai bada umarni na masana’antar shirya Fina finai ta indiya tsagin ‘Bollywood’ mai suna Faruk Kabir.

An hango fasihiyar jarumar ne suna tattaunawa da daraktan akan teburin cin abinci
‘Dining table’ cikin wani yanayi na musayar maganganu masu matukar fa’ida, ana karfafa zaton cewar suna zantawa ne kan fitowar jarumar a fina finan Indiya. Kasantuwar kasancewar hakan ka iya zamowa karo na farko da masana’antar ta ‘Bollywood’ zasu hadu da masana’antar ta ‘Kannywood’ domin yin fim.

Faruk Kabir fitaccen mai bada umarni ne na fina finan indiya, ya fara aiki a masana’antar tun a shekarar alif ta 2000 wato shekara ashirin da daya da suka wuce,
Faruk Kabir shine mataimakin mai bada umarni a finai finai irinsu ‘Phir Bhi Dil Hai Hindustani’ wanda jarumi Shah Rukh Khan da jaruma Juhi Chawla suka fito a ciki, ‘Asoka’ na Jarumi Shah Rukh Khan da Kareena Kapoor Khan, da Fim din ‘Pyar Ishq Aur Mohabbat’ na jarumi Arjun Rampal.

Kazalika shi yabada umarnin fina finai irin su ‘The Awakening’ wanda jarumi Ajay Devgn ya fito a ciki da ‘Khuda Hafiz’ da sauran su.

Rahama Sadau jaruma ‘yar shekara ashirin da bakwai, haifaffiyar Jahar kaduna ce ,dake arewacin Najeriya, ta fara fitowa a Fina Finai a shekara ta 2013 da Fim dinta na farko mai suna ‘Gani ga Wane’ tare da jarumi Ali Nuhu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here