Gudumuwar da Aliko Dangote ya Bawa Makarantun Najeriya

 

Gudumuwar da Aliko Dangote ya ba Makarantu ya kai Naira Biliyan 10.

Attajirin ya kashewa irinsu ABU, BUK, da sauran Jami’o’i makudan kudi.

Duk Najeriya babu mai batar da kudi domin a habaka boko irin Dangote A lokacin da Dangote Academy ta ke shirin daukar sababbin dalibai da za su karanci ilmin fasaha, an bayyana adadin kudin da Aliko Dangote ya kashe a kan ilmi.

Kamar yadda kamfanin Dangote Group ta shaida wa jaridar Sun, bayan gwamnati, babu wani wanda yake kashe kudi a harkar ilmi a kasar nan irin Aliko Dangote. A cikin ‘yan kasuwa masu zaman kansu, Aliko Dangote bai da sa’a a kokarin farfado da ilmi.

Yara fiye da 1, 000 aka dauka a makarantar Dangote Academy, aka koyar da su ilmin fasaha, daga baya kuma aka ba su aiki a wasu kamfanonin Dangote da ake da su.

Shirin farko da kamfanin ya kawo shi ne makarantar horo da aka kafa jahar Kogi inda aka koyar da kwas a kan ilmin fasaha, da kuma koyar da kananun aikin kanikance.

Har ila yau Dangote Academy ta koyar da yara kwas a kan aikin hannu domin su yi riko da kansu.

Bayan horaswa da ake ba yara, kamfanin mai kudin na Afrika ya kashe kudi masu yawa wajen gyara makarantu, daga ciki ya yi wa jami’ar ABU Zaria ginin Naira Biliyan 1.2.

Sun ta ce, Dangote ya kuma dauki nauyin ginin makarantar koyon imin sana’a a jami’ar Bayero ta Kano, rahotanni sun nuna cewa wannan aiki shi ma ya ci Naira biliyan 1.2.

Jami’ar kimiyya da fasahar nan da ke Wudil, Kano, ta samu gudumuwar Naira miliyan 500 daga hannun Dangote, an yi amfani da kudin wajen gina dakuna da aikin lantarki.

Shugaban na Dangote Group ya dauki dawainiyar aikin N300m a jami’ar Ibadan, N120m a makarantar Nawair-ud-deen. Sannan ya ba jami’o’in UNN da Katsina N168m.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here