Shugaban Kwamitin Rikon Kwarya na APC a Jahar Kano, Abdullahi Abbas ya ja Kunnen ‘Yan Jam’iyyar Kan Zaben 2023

Abdullahi Abbas, shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC na jahar Kano, ya bai wa ‘yan jam’iyyarsa shawara.

Ya shawarci ‘yan ga ni kashenin jam’iyyar da su kai wa duk wanda ya yi kokarin yin murdiyar zabe farmaki.

Ya sanar da hakan ne a ranar Juma’a a Kano yayin rantsar da ciyamomi 44 na kananun hukumomin jahar.

Abdullahi Abbas, shugaban kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar APC na jihar Kano, ya umarci duk masu kishin jam’iyyar da su kai wa duk wanda yayi yunkurin yin murdiyar zabe a jahar farmaki.

Abbas ya dade yana bai wa ‘yan jam’iyyar kwarin guiwa akan siyasa. Ya ja kunnen ‘yan jam’iyyar a wani taro da suka yi a watan Janairu, inda yace akwai mummunan mataki da jam’iyya za ta dauka akan duk wanda bai sake rijistar ba.

Shekarar da ta gabata, jam’iyyar ta shirya yin wani shiri na “violence for violence” akan zaben 2023, The Cable ta wallafa.

Ya yi wannan bayanin ne a taron da suka yi na rantsar da shugabannin kananun hukumomi 44 a jahar Kano, inda Abbas yace duk wanda yayi yunkurin magudin a zabe mai zuwa zai kwashi kashinsa a hannu.

“Na umarceku da ku ladabtar da duk wanda kuka gani yana kokarin satar akwatin zabe da sunan magudi. Babu abinda zai faru,” kamar yadda yace.

Ya bukaci duk wasu ‘yan jam’iyyar APC da suka halarci taron a Kano, da su shirya kare hakkin jam’iyyar idan zaben 2023 ya zo.

A jawabin gwamnan jahar Kano, Abdullahi Ganduje, ya shawarci sababbin shugabannin da aka zaba da su dage kuma su zage damtse wurin yin aiki tukuru da kuma hana da cin hanci a jahar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here