Dakarun Sojoji Sun Hallaka Hatsabibin ‘Dan Ta’adda, Junaidu Fasagora da Mayakansa

 

Kasurgumin dan ta’adda a jihar Zamfara ya gamu da ajalinsa bayan dakarun sojoji sun hallaka shi da nayaƙansa.

Rundunar sojojin ta bayyana nasarar da ta samu inda ta murjushe hatsabibin dan ta’addan, Junaidu Fasagora da mayakansa.

Sojojin sun sanar da wannan nasara a yammacin yau Laraba 27 ga watan Maris a shafin X da aka fi sani da Twitter.

Jihar Zamfara – Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar murƙushe hatsabibin dan ta’adda a jihar Zamfara.

Rundunar ta ce ta yi ajalin kasurgumin dan ta’addan mai suna Junaidu Fasagora da sauran na hannun damansa.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa sa rundunar ta fitar a shafinta na X a yammacin yau Laraba 27 fa watan Maris.

Dakarun sojojin sun samu nasarar murƙushe Junaidu da sauran mayakansa ne a yankin karamar hukumar Tsare da ke jihar.

Sojojin suka ce Fasagora da mayakansa sun addabi yankin Arewa maso Yamma da ayyukan ta’addanci.

Ta ce yin ajalin wadannan miyagu babbar nasara ce ganin yadda suka yi sanadin rayukan al’umma da asarar dukiyoyi.

Karin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here