Kisan Sojoji 17: Shugaba Tinubu ya ba da Sabon Umarni ga Dattawa da Sarakunan Okuama

 

A yau Laraba 27 ga watan Maris aka binne sojojin da suka mutu yayin harin kwantan bauna a jihar Delta.

Shugaba Bola Tinubu ya samu halartar bikin inda ya nuna alhini kan mutuwar sojojin tare da karrama su.

Tinubu ya umarci dattawan yankin da kuma sarakuna da su tabbatar sun zakulo matasan da hadin kan jami’an tsaro.

FCT, Abuja – Shugaban kasa, Bola Tinubu ya ba dattawan kauyen Okuama a jihar Delta umarni da su zakulo wadanda ake zargi da kisan. Tinubu ya bayyana haka ne a yau Laraba 27 ga watan Maris yayin da ya halarci jana’izar sojoji 17 da suka mutu a jihar Delta.

Tinubu ya karrama sojojin da lambar yabo

Shugaban ya kuma bukaci sarakunan gargajiya a kauyen da su ba da hadin kai wurin tabbatar da an cafke wadanda suka aikata ta’asar.

Ya kuma bayyana cewa an karrama dukkan sojojin da suka rasa rayukansu a yayin harin da lambar yabo mai daraja ta kasa, cewar Daily Trust.

Wannan na zuwa ne bayan kisan sojoji 17 a kauyen Okuama da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu da ke jihar Delta.

Sojojin sun gamu da ajalinsu ne yayin wasu bata gari suka far musu bayan sun isa yankin domin kwantar da tarzoma, cewar Channels TV.

Umarnin da Tinubu ya ba dattawan

“Dukkansu mun karrama su da lambar yabo, ina sake tabbatar wa wadanda suka aikata hakan za su fuskanci hukunci.”

“Dole za mu zakulo su kuma sojojin da suka mutu za a yi musu adalci ransu ba zai tafi a banza ba.”

“Dattawa da kuma sarakunan Okuama dole su taimaki jami’an tsaro wurin zakulo wadanda suka aikata wannan ta’asar.”

– Bola Tinubu

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here