Jerin Kasuwannin da za a Samu Kayan Abincin Cikin Rahusa a Legas

 

Yayin da ake fama da tsadar kayan abinci a jihar Legas, gwamnatin jihar ta bude kasuwanni da za a siyar da kaya mai sauki.

Gwamnatin ta shirya bude kasuwannin ne a yau Laraba 17 ga watan Maris domin samun saukin siyan kayan abincin.

Wannan na zuwa ne bayan daukar matakin rage farashin kayan abincin da kaso 25 da gwamnan jihar ya yi.

Jihar Legas – Gwamnatin jihar Legas ta shirya bude kasuwanni da al’ummar jihar za su samu kayan abinci kan farashin mai sauki.

A yau Lahadi 17 ga watan Maris gwamnatin ta shirya bude kasuwanni da za a samu farashin cikin sauki da kaso 25.

Kayan abincin da za a samu sauki a Legas

Kwamishinan yada labaran jihar, Gbenga Omotosho shi ya tabbatar da haka inda ya ce Gwamna Babajide Sanwo-Olu ne ya ba da umarnin.

Omotosho ya lissafi kayan abincin da ragin ya shafa kamar haka, wake da shinkafa da garri da tumatar da tattase da kwai da biredi da sauransu.

Har ila yau, ya ce an dauki matakai domin tabbatar da cewa an siyar da kayan abinci yadda ya dace ba tare da matsala ba.

Ya kara da cewa za a siyar da kilo 5 na shinkafa a farashin N5,325 yayin kilo daya kuma N1, 065, cewar Punch.

Sai kuma kilo biyar na wake kan farashin N6,225 yayin da kilo daya kuma zai kama N1,245.

Jerin kasuwannin da za a samu kayan abincin cikin rahusa:

1. Karamar hukumar Eti Osa – Makarantar Ikota, Lekki -Epe Expressway, Ikota.

2. Karamar hukumar Eti-Osa ta Gabas – kasuwar Admiralty Lekki Phase 1.

3. Karamar hukumar Ikoyi Obalende – Old Nursing Ground, 1-9 hanyar Awolowo, Ikoyi, cewar TheCable.

4. Ƙaramar hukumar Victoria Island – makarantar Victory Island Snr.

5. Karamar hukumar Lagos Island – makarantar Elegbata.

6. Karamar hukumar Lagos Island ta Gabas – makarantar Lafiaji.

Sauran kasuwannin da za a samu kayan

1. Karamar hukumar Ikorodu – makarantar Grammer ta Ikorodu, cewar The Nation.

2. Ƙaramar hukumar Igbogbo/Bayeku – makaranta Islamiyya ta Zumuratu.

3. Karamar Hukumar Ijede – makarantar Luwasa.

4. Karamar hukumar ljede Ikorodu ta Arewa.

5. Karamar hukumar Odogunyan Ikorodu ta Yamma – makarantar Cherubim and Seraphim.

6. Karamar hukumar Imota – makarantar karamar hukuma.

7. Ƙaramar hukumar Imota Kosofe – makarantar St Emmanuel.

8. Karamar hukumar Ogudu Ikosi Isheri – makarantar Ikosi.

9. Karamar hukumar Ketu Agboyi Ketu – makarantar Comprehensive a Agboyi Ketu.

Sai kuma sauran kasuwanni da za a samu kayayyakin cikin sauki da dama da ke birnin Ikeja da Epe da kuma Badagry a jihar Legas.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here