Kungiyoyin Arewa Sun Soki Majalisa Kan Dakatar da Abdul Ningi

 

Kungiyoyin da ke magana da masu rajin kare Arewacin Najeriya suna tare da Sanatan Bauchi ta tsakiya, Abdul Ningi.

An dakatar da ‘dan siyasar daga majalisar dattawa bayan ikirarin an yi cushen N3.7tr a cikin kasafin kudin shekarar 2024.

A dalilin dakatarwar, wadannan kungiyoyi suka soki majalisa, suka bukaci a gaggauta maido Sanata Ningi kujerarsa.

Abuja – Wata kungiya mai suna RAID da aka kafa domin cigaban Arewacin Najeriya ta bukaci majalisar dattawa ta dawo da Abdul Ningi.

A ranar Asabar, The Nation ta rahoto kungiyar RAID tana Allah wadai da yadda aka dakatar da Sanatan Bauchi ta tsakiya daga majalisa.

Arewa ta tsayawa Sanata Abdul Ningi

Kungiyar tana ganin cewa an takawa ‘dan majalisar burki ne saboda ya yi namijin kokari wajen bankado irin rashin gaskiyar da ake tafkawa.

RAID ta ce wannan mataki da aka dauka ya jawo an toshe bakin daya daga cikin manyan ‘yan siyasan da ke magana da yawun yankin Arewa.

Wannan matsaya ta fito daga bakin shugaban RAID, Balarabe Rufai a wani taron manema labarai da ya kira a Abuja a karshen makon nan.

Balarabe Rufai ya shaidawa jaridar The Guardian Abdul Ningi yana cigaba da samun goyon bayan al’umma musamman mutanen da ke Arewa.

“Yunkurin Sanata Ningi na haska rashin gaskiyar da aka lullube namijin kokari ne kuma abin da ake bukata.”

“Sai dai korarsa daga zauren majalisar dattawa bala’i ne, mun rasa daya daga cikin masu magana da yawunmu.”

– Balarabe Rufai

Matasan Bauchi suna tare da Sanata Ningi

Kungiyar gamayyar matasa ta Youth Coalition of Bauchi da ke Bauchi ta tsakiya sun bukaci a yi bincike a kan maganar da Ningi yake yi.

Wasu su na maganar zuwa kotu, suka ce idan Sanatan ya yi laifi, hukuncinsa bai wuce dakatarwar wata guda ba, akasin watannin uku.

Abdul Ningi: Dattawan Arewa sun soki Majalisa

Punch ta ce kungiyar ACF ta dattawan Arewa ta fitar da jawabi tana mai sukar yadda majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Abdul Ningi.

Sakataren yada labaran ACF, Farfesa Tukur-Baba ya fitar da jawabi, ya bukaci a yi bincike maimakon gaggawan dakatar da ‘dan majalisar.

Gwamnan Bauchi ya goyi bayan Sanata Ningi

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayyana matsayarsa kan Sanata Abdul Ningi idan za ku tuna da rahoton da muka fitar a baya.

Bala Mohammed ya ce ya ji takaici da aka dakatar da sanatan domin ya tsaya kan gaskiya, ya kuma sha alwashin magance matsalar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here