Sanata Ndume ya Caccaki Hukumar Alhazai Kan Karin Kudin Hajjin 2024

Sanata Ali Ndume ya caccaki hukumar Alhazai kan karin kudin kujerar aikin hajjin shekarar 2024 da muke ciki.

Ndume ya ce karin kudin a wannan hali rashin adalci ne musamman ga wadanda wannan shi ne karon farkonsu.

Sanatan ya bukaci Shugaba Tinubu da ya dauki nauyin biyan sauran cikon kudin domin saukakawa maniyyatan.

FCT, Abuja – Mai tsawatarwa a Majalisar Dattawa, Ali Ndume ya soki karin kudin da hukumar Alhazai ta yi inda ya ce hakan rashin adalci ne da neman hana Musulmai gudanar da ibada.

Sanatan ya ce hakan zai dakile wasu da wannan shi ne karon farko da za su fara halartar kasa mai tsarki domin sauke farali.

“Karin kudin hajji rashin adalci ne” – Sanata

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba 27 ga watan Maris a Abuja, cewar Daily Trust.

Ya lissafo rukunan Musulunci guda biyar inda ya ce aikin hajji na daga cikin wanda ake bukatar Musulmi ya yi ko da sau daya ne a rayuwarsa idan ya samu dama.

Ya kara da cewa bai kamata a tilasta wadanda suka biya a farko karin kudin ba wanda bai wuce mako daya da za a rufe karban kudin ba.

Shawarar da Sanata Ndume ya ba Tinubu

“Karin kudin aikin hajji ‘yar bazata ga Musulmai wannan rashin adalci ne, babu yadda za a tilasta musu biyan kudin.”

“Akwai wadanda suka biya tun farko, idan har akwai wani karin kudi ko sauyi bai kamata a daura musu ba, ya kamata hukumar NAHCON ta dauki nauyi.”

“Ya kamata a dauki matakin gaggawa, ina kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya amince da biyan cikon kudin domin kawo karshen matsalar.”

– Ali Ndume

Sanatan ya kuma kirayi hukumomin Alhazai na jihohi da su tallafawa alhazan musamman wadanda zuwansu na farko kenan, cewar Vanguard.

NAHCON ta kara kudin kujerar hajji Wannan na zuwa ne bayan hukumar Alhazai ta kara kudin aikin hajjin inda ta bukaci maniyyata su kara biyan N1.9m.

Hukumar ta bayyana cewa tashin farashin dala shi ne ya tilasta karin kudin kujerar domin samun daidaito.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here