Gwamna Dapo Abiodun ya Rage Kaso 50 Cikin 100 na Farashin Shikafa

 

Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya rage kaso 50 cikin 100 a farashin shinkafa domin ragewa al’ummar jihar wahalhalun tsadar rayuwa.

Ya ce gwamnatinsa za ta sayar da buhunan shinkafa a rabin farashin kasuwa kuma za ta fara daga kan ma’aikatan gwamnati.

Abiodun ya yi wannan furuci ne a wurin taron buɗa baki da ya shiryawa malamai a gidan gwamnati da ke Abeokuta.

Jihar Ogun – Gwamnan jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun, ya ce nan ba da jimawa ba gwamnatinsa za ta fara siyar da shinkafa ga al’ummar jihar a kan farashi mai rangwamen 50%.

Gwamna Abiodun ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne domun rage wa mazauna Ogun raɗaɗin tsadar rayuwar da ake ciki a ƙasar nan, Channels tv ta ruwaito.

Ya ce gwamnatin za ta fara daga ma’aikata, inda ya ƙara da cewa burinsa kowa ya koma siyan kayan abinci kamar da kafin hauhawar farashi.

Ya yi wannan jawabi ne a lokacin buda baki na musamman da aka shirya wa kungiyar Limamai da Alfas ta jihar a fadar gwamnati da ke Abeokuta ranar Talata.

Meyasa gwamnan ya rage kaso 50%?

“Mun yanke shawarar fara sayar da shinkafa kuma za mu rage kashi 50% daga ainihin farashin da ake sayarwa. Za mu fara da ma’aikata, duk ma’aikatan gwamnati za su sayi shinkafa a rabin farashinta.

“Abin da muke ƙoƙarin yi shi ne sake mayar da al’umma matsayinsu na kafin hauhawar farashi, wannan ƙarfin da suke da shi na iya ɗaukar ɗawainiyar kansu muke son dawo masu da shi.”

– Dapo Abiodun.

Gwamnan ya bayyana cewa an kafa kwamitin da zai kula da yadda za a sayar da kayayyakin ga mazauna jihar, a cewar TVC News.

Abiodun ya kara da cewa sayar da shinkafara da rangwamen kashi 50% na farashinta zai baiwa gwamnatinsa damar ci gaba da siyo wasu domin sayar wa jama’a.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here