dangote Archives - Arewa Agenda Hausa

Dangote ya Buƙaci NNPCL da ƴan Kasuwa da su Daina Shigo da Mai Daga Waje
Dangote ya Buƙaci NNPCL da ƴan Kasuwa da su Daina Shigo da Mai Daga Waje

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce za a daina samun dogayen layuka a gidajen mai muddin dillalan mai suka fara sayen mai a matatarsa.

Dangote ya bayyana haka ne bayan wata ganawa da shugaba Bola Tinubu a yau Talata.

Hamshaƙin attajirin na Afrika ya kuma buƙaci babban kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL, da kuma ƴan kasuwa a faɗin ƙasar da su daina shigo da mai daga waje.

Ya ce matatarsa ita ce mafita ga batun dogayen layuka da ake samu a gidajen mai da ke faɗin ƙasar.

“Kiyasin da na yi ya nuna cewa fetur da za mu iya sha a kullu yaumin zai kai lita miliyan 30-32, za mu iya fara bayar da wannan ko a mako mai zuwa. Ba wani abun damuwa bane saboda muna da lita miliyan 500 a tankokinmu yanzu haka. Don haka ko ba a shigo da mai cikin ƙasa ba, za a iya amfani da man mu a faɗin ƙasar har na tsawon kwanaki 12,” in ji Dangote.

Hakan na zuwa ne ƙasa da wata ɗaya bayan da gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da tsarin sayar da ɗanyen man fetur a naira ga Dangote maimakon kuɗin dala.

Gwamnatin tarayya ta ce matakin zai daidaita farashin man fetur a ƙasar da kuma karfafa kuɗin naira ta hanyar rage buƙatar amfani da dala wajen hada-hadar ɗanyen man fetur.

The post Dangote ya Buƙaci NNPCL da ƴan Kasuwa da su Daina Shigo da Mai Daga Waje appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Lokaci ya yi da Gwamnatin Najeriya za ta Daina Biyan Tallafin Man Fetur – Dangote
Lokaci ya yi da Gwamnatin Najeriya za ta Daina Biyan Tallafin Man Fetur – Dangote

Shugaban matatar man fetur ta Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce lokaci ya yi da gwamnatin Najeriya za ta daina biyan kuɗin tallafin man fetur.

Dangote ya bayyana hakan ne a wata tattaunawarsa da Blomberg a ranar Litinin, inda ya ce biyan tallafin na sa gwamnatin “kashe kuɗaɗen da bai kamata ba,” wanda hakan ya sa akwai buƙatar a dakatar da shi, sannan ya ƙara da cewa ita kanta gwamnatin Najeriya ba za ta iya cigaba da biyan kuɗin tallafin ba.

“Ina tunanin lokaci ya yi da za a daina biyan kuɗin tallafin nan domin dukkan ƙasashe sun daina biya.

“Farashin man fetur ɗinmu kusan kashi 60 ne farashin ƙasashen da muke maƙwabtaka da su, kuma iyakokinmu babu cikakken tsaro. Don haka ba za a iya cigaba da kashe irin kuɗaɗen nan ba,” kamar yadda ya bayyana a tattaunawarsa da Bloomberg.

Dangote ya ƙara da cewa man fetur ɗin da matatarsa ke fitarwa zai taimaka wajen rage wa Naira nauyi.

Ya ce, “Batun tallafin fetur magana ce babba. Idan ka bayar da tallafi a kan wani abu, wasu sai su riƙa ƙara yawan abun domin su samu ƙarin kuɗaɗe sannan sai nauyin ya ƙare a kan gwamnati. Zai fi dacewa a daina biya baki ɗaya.

“Matatarmu za ta magance matsaloli da dama. Za ta bayyana asalin adadin man fetur da ake amfani da shi a Najeriya saboda babu wanda zai iya faɗa maka a yanzu adadin litar man fetur da ake amfani da shi. Wasu za su ce maka lita miliyan 60 a kullum, wasu suna cewa bai kai ba. Amma mu yanzu za mu iya kididdigewa. Sannan za mu saka na’urorin bibiyar motocinmu domin tabbatar da cewa a Najeriya suke sauke man.”

The post Lokaci ya yi da Gwamnatin Najeriya za ta Daina Biyan Tallafin Man Fetur – Dangote appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Nan ba da Jimawa ba Man Fetur ɗinmu zai Shiga Kasuwa – Dangote
Nan ba da Jimawa ba Man Fetur ɗinmu zai Shiga Kasuwa – Dangote

Mai kamfanin Matatar man fetur ta Dangote, Aliko Dangote ya sanar da cewa da

zarar kamfaninsa ya kammala wasu muhimman abubuwa da kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), man fetur ɗin kamfanin nasa zai shiga kasuwa.

Hamshakin ɗan kasuwar ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a ranar Talata, biyo bayan kaddamar da kason farko na man daga matatar kamfanin mai ganga 650,000 a kowace rana.

Dangote ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za su iya sa ran samun man fetur mai inganci da daɗewa

“Ba za ku ƙara fuskantar matsalolin da injinan motoci ke baku ba,” in ji Dangote.

“Man fetur ɗin mu zai yi daidai da na kowace ƙasa a duniya; babu wanda zai wuce mu ta fuskar inganci,” in ji shi.

Dangote ya jaddada fa’idar tattalin arzikin da ayyukan matatar kamfanin ke da su, inda ya bayyana cewa za ta taimaka wajen farfado da masana’antu a Najeriya tare da daidaita darajar naira da kuma taimakawa wajen rage hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa,” in ji shi.

Matatar mai ta Dangote da ke Legas ta dala biliyan 20, ta fara aiki a watan Disambar da ya gabata.

The post Nan ba da Jimawa ba Man Fetur ɗinmu zai Shiga Kasuwa – Dangote appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Dangote ya Halarci Taron Nadin Sarautar Matar Marigayi Abba Kyari
Dangote ya Halarci Taron Nadin Sarautar Matar Marigayi Abba Kyari

Alhaji Nubu Wabi III, Sarkin Jama’are ya nada matar marigayi Abba Kyari, Hajiya Hauwa Kulu a matsayin Gimbiyar Jama’are.

An yi bikin nadin sarautar a ranar Lahadi a fadar basaraken inda har biloniya Alhaji Aliko Dangote ya samu halarta.

Wabi ya kwatanta Hajiya Kulu da mace jaruma tagari mai kishin al’umma da don ganin cigaban Jama’are.

Bauchi – Sarkin Jama’are, Mai martaba Alhaji Nuhu Wabi III, ya nada matar marigayi tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abba Kyari, Hajiya Hauwa Kulu a matsayin gimbiyar farko ta Jama’are.

A bikin nadin sarautar da aka yi a fadarsa ranar Lahadi, sarkin ya kwatanta ta da diya tagari a Jama’are wacce ta yi matukar kokari wurin kawo cigaba ga dukkan masarautar.

Marigayi Kyari ‘dan asalin jihar Borno ne amma matarsa Hauwa Nee Gidado ta fito daga garin Jama’are dake karamar hukumar Jama’are ta jihar Bauchi.

“A al’adance Gimbiya ‘yar sarki ce kuma ita ce gadar dake tsakanin sarki da mata wadanda basu da damar shiga lamurran masarautar kai tsaye.

“Da wannan nadin, matan Jama’are a yanzu suna da wakiliya a majalisar zartarwa ta masarautar, za a ji muryoyinsu tangaran.

“Burina ya cika saboda ina da diyar masarautar a majalisar zartarwarta,” yace.

Wabi ya kwatanta Hauwa a matsayin mace jaruma wacce ta damu da damuwar jama’a tare da cigaba masarautar.

“Ta cancanci sarauta saboda ta mallaki dukkan dalilai uku da ya dace a karramata a Jama’are,”yace

Fitaccen bilonyan duniya, AlhajiAliko Dangote, ya samu damar halartar nadin sarautan. @arewafamilyweddings ne suka wallafa bidiyon.

The post Dangote ya Halarci Taron Nadin Sarautar Matar Marigayi Abba Kyari appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Dangote ya Hada N380.38bn a Cikin Watanni 3
Dangote ya Hada N380.38bn a Cikin Watanni 3

Tun daga watan Fabrairu, duniya ta shiga gunaguni game da mamayar Rasha a kasar Ukraine, lamarin da ya jefa miliyoyin ‘yan Ukraine cikin mawuyacin hali.

Sai dai bisa ga dukkan alamu ba ‘yan kasar Ukraine ne kadai ke kage ba, domin kuwa hudu daga cikin attajiran Rasha sun rasa mukaminsu a jerin attajirai, Aliko Dangote ya haura.

Dangote, wanda a farkon 2022 ke cikin mutane 100 mafi arziki da ke raye a duniya, ya tsallake matsayi 21 kuma a yanzu ya zama na 79 a duniya.

Attajirin da ya fi kowa kudi a Nahiyar Afrika, Aliko Dangote, yanzu ya fi kusan dukkan attajiran kasar Rasha, banda hudu daga cikinsu.

A cewar jadawalin Bloomberg Billionaires Index, bakar fatar da ya fi kowa kudi a duniya a yanzu yana da kimanin dala biliyan 20 bayan da ya samu sama da dala miliyan 915 (N380.38bn) cikin watanni uku kacal.

Sabon kari na arzikin da ya samu na nuni da cewa Aliko Dangote ya zama attajiri na 79 a raye a duniya.

Shigar Dangote 2022

Dangote dai bai shiga 2022 da kafar dama, domin kuwa ya yi asarar dala miliyan 244 a rana guda bayan kare 2021 a wani matsayi mai inganci.

Dan kasuwan ya fado zuwa na 100 a jerin masu kudin duniya, inda ya mallaki dala biliyan 19.1 kacal.

Sai dai kuma labarin ya sauya sosai bayan ‘yan makonni kadan, kamar yadda a karshen watan Janairun 2022 ya nuna, Dangote ya hau matsayi na 91 a jerin attajiran duniya da zunzurutun kud akalla dala biliyan 19.5.

Haka dai ya ci gaba da habaka a Fabrairu 2022 kuma ya kare watan da zunzurutun dukiyar da ta kai dala biliyan 20.0 yayin da kuma ya yi tsalle ya zuwa matsayi na 84.

A baya-bayan nan a cikin Maris ya hau daya daga cikin mafi girman matakin da ya taba kasancewa.

Rushewar arzikin attajiran Rasha ya taimaka wa habakar Dangote

Faduwar hamshakan attajiran kasar Rasha ne ya kuma taimaka wa Dangote wajen samun nasarar tsallaka matakai a jerin attajiran duniya.

Lokacin da aka shiga 2022, akwai wasu hamshakan attajiran Rasha bakwai da suka dara Dangote arziki.

Sun hada da:

1. Leonid Mikelson

2. Vladimir Potanin

3. Alexei Mordashov

4. Vladimir Lisin

5. Vagit Alekperov

6. Gennady Timchenko

7. Alisher Usmanov

Ya zuwa karshen Maris 2022, Dangote yanzu ya fi dukkan hamshakan attajiran na kasar Rasha arziki idan aka cire Vladimir Potanin, Leonid Mikhelson, Alexey Mordashov da Vladimir Lisin.

The post Dangote ya Hada N380.38bn a Cikin Watanni 3 appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Hukumar Kwastam ta Kama Motar Dangote Makare da Shinkafar Waje 250
Hukumar Kwastam ta Kama Motar Dangote Makare da Shinkafar Waje 250

Hukumar kwastam a Najeriya ta yi nasarar cafke wata motar Dangote makare da shinkafar waje.

Hukumar ta bayyana kame motar dauke da buhuna 250 na haramtacciyar shinkafar ta kasar waje.

Hakazalika a wani yankin hukumar ta kame wasu haramtattun kayayakin da suka hada da fatan jaki, ganyen wiwi da sauransu.

Legas – Kwantrolla Janar na Kwastam, Team A Unit, Mohammed Yusuf, ya ce jami’an hukumar sun kwace wata motar babban Dangote makare da buhun shinkafa na kasar waje 250 da aka haramta shigo da su.

Yusuf ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Ikeja, Legas, yayin taron manema labarai inda ya bada jawabin ayyukan da suka yi cikin makonni hudu a sassa daban-daban, The Punch ta ruwaito.

Ya bayyana cewa a cikin kayan da aka kwace akwai kwantena ta katako mai tsawon kafa 20; buhunan shinkafa masu nauyin 50kg guda 1000; taya na gwanjo guda 3,143; kunshin tufafin gwanjo 320; Buhun fatar jaki 44 da ganyen wiwi kilogiram 137.3.

“Ina farin cikin bayyana cewa cikin makonni hudu, tawaga ta Strike Force Team A, ta karbi N648,300,986 a matsayin haraji. Ta kuma kwace kaya da kudin harajinsu ya kai N373,629,700.

“Ina son in jadada cewa ba mu daukan aiki da wasa musamman aiki mai muhimmanci irin wannan. Masu fasakwabri da ke tunanin za su yi amfani da wannan damar su yi mummunan aikinsu za su sha mamaki,” in ji shi.

Mai magana da yawun sashin, Peter Duniya, ya tabbatar da cewa an kama motar kamfanin Dangote dauke da haramtatun kayan.

“Motar kamfanin Dangote na daya daga cikin kayayyakin da muka kama,” ya kara.

The post Hukumar Kwastam ta Kama Motar Dangote Makare da Shinkafar Waje 250 appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Matsalolin Arewa da ya Kamata a Duba – Abdulwahab Said Ahmad
Matsalolin Arewa da ya Kamata a Duba- Abdulwahab Said Ahmad

Idan Kayiwa Najeriya Kallon Tsanaki za kaga cewa Arewa da ‘Yan Arewa sune suka hana Kasar Cigaba.

idan da za’a cire Arewa da kasha mamaki badan komai ba Sai don irin son kai, da bakin ciki da kuma rusa duk wani dan arewan da yayi shura.

Babu wani dan Siyasa Guda Daya a Arewacin Najeriya da zai magana kashi 70% na alummar yankin su saurare shi.

Babu wani malamin addini da zai magana a Arewa kashi 30% na yankin su saurare shi. Ballantana ace ma ga dattijan Arewa.

Idan kaga dan Jarida yana gaggawar buga labarai to Matsala ce a afku a Arewa.

Dan Arewa ne yake bin diddigin danuwanshi domin yasamo abun fada marar kyau akanshi ya bata shi.

Duba kaga irin gudun mowar da BUA DA Dangote suka bayar lokacin Corona amma har yanzu babu wata kungiya a Arewa data iya karramasu Sai ma zagi dake biyo wa baya.

Sai Dan kudu yayi batanci ko kazafi akan wani shahararren a Arewa amma Sai kaga Yan Arewa suna taya shi.

Duk matsalar dake Arewa an taba yinta a Kudu amma basu bari tayi tsamari ba sukai maganinta, amma munafinci ya hanamu.

A Arewa ne da adawa ke murna idan an kai hari ko an sace wasu domin yasamu abun gorantawa Mai mulki.

Bazaka taba ganin Yan adawa sun yi taron FADAKARWA kan Halin tsaro ba, Sai dai a koma gefe ana karawa wutar iskar gas.

Mai kudin Arewa ne yake ba talakan Arewa kudi yaje ya sato masa talakan Arewa ya Boye masa shi, Ayi cinikin fansa abawa maikudin 1m shikuma ya Bashi 30000.

Boko Haram Arewa, Garkuwa da Mutane Arewa, Rikicin Addini Arewa, Daba Arewa, Bangar Siyasa Arewa…

Allah ka sauwake Mana.

#kano #arewapopularschallenge #arewapeople #insecurechallenge

The post Matsalolin Arewa da ya Kamata a Duba – Abdulwahab Said Ahmad appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Kamfanin Takin Dangote ya Gina Makaranta Kyauta a Jahar Legas
Kamfanin Takin Dangote ya Gina Makaranta Kyauta a Jahar Legas

Kamfanin takin zamani na Dangote ya gina katafaren makaranta a jihar Legas.

Mutanen Ijebu-Lekki sun nuna farin cikinsu da jin dadi dangane da aikin da kamfanin ya yi musu.

Kamfanin ya jaddada cewa yana daga cikin aikinsu wanzar da ilimi tsakanin al’ummar kasar baki daya.

Kamfanin takin zamani na Dangote ya gina katafariyar dakin karatun zamani da miliyoyin naira na zamani tare da mika shi ga hukumar kula da ilimin bai-daya ta jihar Legas, Jaridar The Punch ta ruwaito.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Lahadi ta ce, gudummawar makarantar na da nufin samar wa al’ummar Abejoye da ke yankin Ibeju-Lekki na Legas ingantaccen ilimi ta hanyar samar da kayayyakin koyarwa da kuma yanayi mai kyau.

A cewar manajan kamfanin takin, ajujuwan da aka gina a matsayin wani bangare na kokarin daukar nauyin jama’a na kamfanin, za su yi aiki ne a madadin Makarantar Firamare ta Abejoye.

Makarantar tana daga cikin yankin kasuwanci na kyauta da aka ware wa DFL, amma an komar da ita zuwa ga al’ummar Abejoye, yanzu haka ta kunshi dakunan ma’aikata, ofishin shugaban malamai, wuraren bayan gida, injin samar da wutar lantarki da kuma rijiyar burtsatse.

Da yake jawabi a bikin mika kayan a Legas, Babban Daraktan Zartarwa, Strategy Capital Projects da Portfolio Development, Dangote Industries Limited, Devakumar Edwin, ya yi alkawarin kamfanin zai yi sadaukarwa domin samar da ingantaccen ilimi a kasar nan baki daya.

A cewarsa, Tallafin Dangote na ci gaban ilimi ya shafi taimaka wa al’ummomin da ke karbar bakunci don samar da ingantaccen ilimi mai inganci wanda daga karshe zai isa ga dukkan mutane.

Ya ce, “Mu a matsayinmu na kamfani mun yi imanin cewa ilimi fasfo ne na nan gaba kuma cewa saka hannun jari a cikin ilimi shine mafi kyawu kuma muna da muradin haɓakawa, ilimantarwa da kuma ƙarfafawa matasa.

“Muna cimma wadannan manufofi ne ta hanyoyi daban-daban kamar bayar da tallafin karatu ga dalibai 50 da aka zaba a tsakanin al’ummomin da ke karbar bakuncinmu, tare da horar da matasa 200 kan sana’o’in hannu da dama.”

Edwin ya kara da cewa kamfanin ya fara shirye-shirye daban-daban da nufin bunkasa kananan hukumomi a tsakanin al’ummomin da suke karbar bakuncinsu don basu damar gudanar da ayyukansu na ci gaban kansu.

Shugaban zartarwa na LASUBEB, Wahab Alawiye-King, wanda Daraktan sashin aiyuka, Ebaide Omokore ya wakilta a taron, ya yaba wa kamfanin takin zamani na Dangote saboda samar da kayayyakin aiki don inganta ilimi.

Ya lura cewa hukumar tana kuma gudanar da ayyukan inganta kayayyakin more rayuwa da gyara a sassa da dama na jihar, musamman a tsakanin al’ummomin da ke da wahalar shiga.

Shima da yake magana a wurin taron, Shugaban Karamar Hukumar Lekki Local Council Development Area, na Jihar Legas, Ogidan Olaitan, ya yaba wa kamfanin bisa wannan karamcin, yana mai cewa kamfanin zamani na Dangote ya tabbatar da cewa kamfani ne mai kula da zamantakewar al’umma, wanda ke da sha’awar kamfanin a zuciyarsa.

The post Kamfanin Takin Dangote ya Gina Makaranta Kyauta a Jahar Legas appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Gwamnan Jahar Nasarawa ya Fadi Dalilin Zuwansa Amurka
Gwamnan Jahar Nasarawa ya Fadi Dalilin Zuwansa Amurka

Gwamnan Jahar Nasarawa Injiniya Abdullahi Abdullahi ya bayyana cewa ziyarar sa Amurka bata da alaka da duba lafiya..

Ya shaida cewa ya dauki hutun karshen shekara kamar yadda ya saba kuma ya tafi hutawa tare da iyalan sa a Houston da ke Texas.

Ya kuma kara da cewa yayi amfani da damar wajen yin gwajin lafiya kamar yadda ya saba tun kafin zaman sa gwamna amma lafiyar ƙalau.

Gwamnan Jahar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya karyata jita jitar da ke cewa ya tafi Amurka ne don duba lafiyarsa, ya kuma bayyana cewa yaje Amurka don ziyartar yayan sa yayin da ya ke hutun karshen shekara.

Gwamnan ya yi ikirarin ne lokacin da ya bayyana a hirar gidan talabijin na Channels, kamar yadda kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Sule, wanda ake ganin ya wofantar da asibitocin jihar don tafiya duba lafiya zuwa Amurka, ya bayyana cewa yana daukar hutun shekara a watan Disamba kuma yayi amfani da wannan damar don ziyartar iyalan sa a Houston, Texas.

Gwamnan ya kara da cewa yayin da ya ke hutu a Amurka, inda ya dauki tsawon lokaci, ya yi amfani da damar don duba lafiyarsa.

“Ziyara ta nan bata da alaka da lafiya. Nazo ne hutun karshen shekara. Kamar yadda na saba, ana duba lafiyata tun lokacin ina babban daraktan kamfanonin Dangote.

“Ba abin da ke damuna, lafiya ta ƙalau. Na kammala gwajin lafiya kamar yadda na saba, hakori, ido da komai kuma komai lafiya ƙalau,” ya yi karin bayani.

The post Gwamnan Jahar Nasarawa ya Fadi Dalilin Zuwansa Amurka appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Gwamati ta Ware Kamfanin Dangote Daga Dokar Rufe Iyakokin Kasa
Gwamati ta Ware Kamfanin Dangote Daga Dokar Rufe Iyakokin Kasa

Gwamnatin tarayya ta yarje gami da sahalewa kamfanin siminti na Dangote ya cigaba da fitar da kayayyakinsa zuwa makwabtan ƙasashe duk da dokar rufe iyakokinta.

Tuni mutane suka fara sa ran cewa gwamnati za ta buɗe iyakar gabaɗaya don cigaba da gudanar harkokin kasuwanci tunda an fara buɗewa shafaffu da mai irinsu Ɗangote.

Tun a a watan Agusta na shekarar 2019 gwamnatin tarayya ta rufe iyakokinta don bunƙasa harkokin kasuwanci da noma a cikin gida Gwamnatin Najeriya ta ƙyale kamfanin siminti na Dangote da yaci gaba da shige da ficensa akan iyakokin ƙasarta, a cewar jaridar Bloomberg.

Hakan ya zo duk da umarnin gwamnatin tarayya tayi na rufe iyakokin ƙasa sama da shekara guda.

Wannan yunƙuri ya janyo sa rai a zukatan ƴan Najeriya wai ko wataƙila gwamnatin tarayya na shirin buɗe iyakokin ƙasar don cigaba da kasuwanci da maƙwabtan ƙasashe bayan shafe sama da shekara guda a rufe.

Gwamnatin Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ta sahalewa babban mai sarrafa kaya na Afirka, Dangote, da ya cigaba da kai kayansa ƙasar Togo da Niger a watanni huɗun ƙarshen shekarar nan.

Wannan shine karo na farko a watanni goma, Michel Purchersos, shugaban kamfanin reshen jihar Legas, ya fada a wata hirarsa da masu ruwa da tsaki a kan hannun jari a Legas ya ce; “fitar da kayan ya kasance ne sakamakon sahalewar da gwamnati ta yi” a cewarsa.

Ana ganin ware kamfanin siminti na Dangote a matsayin laushi da gwamnatin ta yi akan matsayarta na rufe iyakoki da ya fara tun a watan Agusta na shekarar 2019.

Kamar kuma hakan zai baiwa kasuwanci cigaba da wanzuwa akan iyakokin ƙasar nan.

Gwamnatin Najeriya ta rufe iyakokinta da ƙashen da suka haɗar da; Benin da Nijar don kawo ƙarshen fasaƙwauri da bunƙasa harkokin kasuwanci cikin gida.

Dukda rufe iyakokin ya tilasta jama’a cin kayayyakin gona da aka sarrafa a gida Najeriya kamar shinkafa da sauransu.

Sai dai kuma hakan ya ƙuntatawa kamfanonin yammacin Afirka wanda suka dogara da Najeriya a kasuwancinsu na aƙalla mutane miliyan ɗari biyu ₦200m.

Dangote ya na fitar da kaya “amma a ƙayyade”, sai dai akwai tsarin haɓaka kasuwancinsa ta hanyar amfani da mashigar teku acewar Puchercos.

Tsarin da kamfanin dake jihar Legas ke yi don ganin ta siyo hannayen jari ya samu jinkiri sakamakon tasgaro da tangarɗa irin ta kasuwa wanda hakan ya shafi darajar hannayen jarin,G uillaume Moye, mai aiki a matsayin babban shugaban kasuwanci shine ya faɗi hakan a wannan kiran tattaunawar haɗakar.

The post Gwamati ta Ware Kamfanin Dangote Daga Dokar Rufe Iyakokin Kasa appeared first on Arewa Agenda Hausa.