Matsalolin Arewa da ya Kamata a Duba- Abdulwahab Said Ahmad

Idan Kayiwa Najeriya Kallon Tsanaki za kaga cewa Arewa da ‘Yan Arewa sune suka hana Kasar Cigaba.

idan da za’a cire Arewa da kasha mamaki badan komai ba Sai don irin son kai, da bakin ciki da kuma rusa duk wani dan arewan da yayi shura.

Babu wani dan Siyasa Guda Daya a Arewacin Najeriya da zai magana kashi 70% na alummar yankin su saurare shi.

Babu wani malamin addini da zai magana a Arewa kashi 30% na yankin su saurare shi. Ballantana ace ma ga dattijan Arewa.

Idan kaga dan Jarida yana gaggawar buga labarai to Matsala ce a afku a Arewa.

Dan Arewa ne yake bin diddigin danuwanshi domin yasamo abun fada marar kyau akanshi ya bata shi.

Duba kaga irin gudun mowar da BUA DA Dangote suka bayar lokacin Corona amma har yanzu babu wata kungiya a Arewa data iya karramasu Sai ma zagi dake biyo wa baya.

Sai Dan kudu yayi batanci ko kazafi akan wani shahararren a Arewa amma Sai kaga Yan Arewa suna taya shi.

Duk matsalar dake Arewa an taba yinta a Kudu amma basu bari tayi tsamari ba sukai maganinta, amma munafinci ya hanamu.

A Arewa ne da adawa ke murna idan an kai hari ko an sace wasu domin yasamu abun gorantawa Mai mulki.

Bazaka taba ganin Yan adawa sun yi taron FADAKARWA kan Halin tsaro ba, Sai dai a koma gefe ana karawa wutar iskar gas.

Mai kudin Arewa ne yake ba talakan Arewa kudi yaje ya sato masa talakan Arewa ya Boye masa shi, Ayi cinikin fansa abawa maikudin 1m shikuma ya Bashi 30000.

Boko Haram Arewa, Garkuwa da Mutane Arewa, Rikicin Addini Arewa, Daba Arewa, Bangar Siyasa Arewa…

Allah ka sauwake Mana.
#kano #arewapopularschallenge #arewapeople #insecurechallenge

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here