Tsokaci ga Rubutun Fina-finan Kannywood – Sameen Y Sa’id 

 

-Marubatan Kannywood: gyara ko barna

-Me Yakamata a Rubutu:-

Ina Mafuta:

Gabatarwa: duk dacewa an dade ana rubatawa da haska fina-finan hausa iri-iri a masana’antar shirya fina-finan Hausa wacce akafi sani da “Kannywood”. Shin abin tambaya shine; fina-finan suna isar da sakon da ya kamata su isar? Kokuma anayinsu ne domin biyan bukatar marubucin ko me shiryawa batare da ya kalli tasirin da wannan shirin fim din yake dashi ba awajen me kallo. Duk cewa fim yana zama silar daukar wata dabi’a; me kyau ko mara kyau!

Kalubalen Masana’antar:

Duk da cewa masana’antar “Kannywood” masana’anta ce da take fama da karancin tsarin doka, da tsarin gudanarwa. Amman akwai yunkurin dokoki na hukumar tace fina-finan da dab’i ta jahar Kano wato “Kano State Censorship Board”, Amman dukda haka, kalubale kullum karuwa yake daga marubuta, masu shiryawa da sauransu.

Abinda Yakamata A Rubuta:

Shugaban Hukumar tace fina-finan jahar Kano, Malam Isma’il Na’abba Afakalla, ya jadaddawa gidan radiyon Freedom cewa sun hana haska fina-finan da suke nuna dabi’ar Daba da sauran haramtaciyar dabi’a. Ya kuma ce za su saka ido, su dauki mataki ga duk wanda ya sabawa dokar “Censorship Board.”

Saboda haka, akwai bukatar a maida hankali wajen haska fina-finan dasuke da mahimmanci, wadanda suke dauke da darasi, amfani ko kuma bunkasa al’adar Hausawa.

Misali, wani fim da ake haskawa “Aduniya” wanda a fahimta da nazari har yau banga wani alfanu Ko kuma gyara da yakawo a dabi’ar mutane ba. Sedai yana koyar da wata dabi’ar daban.

Misali, na taba gani acikin littafin mai nazari akan fina-finan hausa. Kuma daya daga cikin masu son ganin an samar da gyara a masana’antar wato Dr. Muhsin Ibrahim na Jami’ar Cologne, a littafinsa na “Kannywood: Unveiling The Overlooked Hausa Film Industry”, yayi tsokaci kan fina-finan da basu dauki salo na daidai ko burgewa ba. Ya bada misali da “Aduniya” wanda yanuna tundaga sunan fim din bai dace da abunda yake cikin fim din ba, abun nufi; ma’anar fim dai bata fito ba.

Ina Mafuta:

Yakamata marubuta da furodusoshi su san me yakamata su rubuta, kuma su haskawa duniya domin fim yana zama jigo kuma madubin canjin dabi’ar dayawa daga cikin wasu mutane. Sannan yana nunawa wasu al’ummar dasuke kalla cewa, wannan itace dabi’ar al’ummar dasuke cikin wannan fim din.

Sameen Y Saeed (Dr SYS)

Daya daga cikin marubuta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here