Yau Talata ya Zama Dole ga Kowani Kabilar Igbo ya Zauna a Gida – IPOB

 

IPOB ta umurci yan jihohin kudu da su zauna a gida yau Talata.

Wannan sanarwar tasu ta zo ne ganin cewa shugaban su Nnamdi Kanu ya bayyana a kotu yau.

Kungiyar tace dole kowani kabilar Igbo ya nuna wa Shugaban nasu goyan baya.

Tsagerun kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra (IPOB) ta umurci yan jihohin Igbo da kada su sake su fito yau Talata.

Mai magana da yawun kungiyar, Emma Powerful, yace sun dauki matakin ne ganin cewa shugaban su Nnamdi Kanu ya bayyana a kotu yau Talata kamar yadda Jaridar Nation ta ruwaito.

zaman gida da suka kakaba wa mutane na ranar Litinin har yanzu ya sanya bankuna, kasuwanni, shaguna da sauran wasu harkoki na yau da kullum a Jihar Anambara da ma wasu jihohin a tasgu.

Fararen hula a Anambara basa iya fitowa su je Ofisoshinsu saboda barazana da yan kungiyar suke wa rayuwarsu.

A wani jawabi da kungiyar (IPOB) ta saki ranar Litinin, tace:

” Mun riga a da mun bayyana cewa duk ranar da Shugaban mu Nnamdi Kanu zai bayyana a kotu to dole kowa ya nuna mishi goyon baya.

“Saboda haka, yau Talata ya zama dole ga kowani kabilar Igbo ya zauna a gida.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here