Jarrabawar ‘Qualifying’ a Jihar Kano
Faduwar jarrabawar “Qualifying” da rashin biyawa dalibai kudin da zasu rubuta jarrabawar SSCE ba karamar barazana ga ilimi bace a jihar Kano. Wannan shi zai kara tabbatar da lalacewar ilimi a jihar. Kuma zai kara jawowa faduwar gwamnatin da suke burin kafawa karkashin ikon gwamnati mai mulki.
Read Also:
Ba’a taba kawo tsarin cewa sai mutum ya ci “9 credits” sannan gwamnati zata sahale masa rubuta jarrabawar SSCE ba, sai a wannan kadamin. Bisa al’ada, idan dalibi ya samu “5 credits” tare da ‘Mathematics’ da ‘English’, to gwamnati zata sahale masa ya rubuta jarrabawar SSCE (WAEC, NBAIS ko NECO), Amman yanxu sai aka ce; sai wanda yasamu “9 Credits” sannan gwamnati zata sahale wa rubuta SSCE din.
Jarrabawar SSCE ta dade tana zama haramiyar ‘ya’yan talakawa, dalibai da dama suna hakura da karatun gabadaya saboda rashin halin biyan jarrabawar SSCE din. Misali, a yanzu, dalibai suna biyan akalla 20,000 ga NECO, WAEC ko NBAIS ga duk dalibin da gwamnatin bata sahale masa ba.
A nawa fahimtar, a babu amfanin rubuta jarrabawar “Qualifying” gabadaya a jihar Kano. Indai irin wannan tsarin shi ne makomar daliban sakandiren gwamnati. Nasan ba kowa zai yarda da ra’ayina ba, saboda matsala ce ta wasu tsirari marasa karfi; idan mutum na da hali ma ko makarantar da akeyin Qualifying bazai kai ‘ya’yansa ba.
Comrade Sameen Y Saeed (Dr SYS)
27th May 2022