Godswill Akpabio Archives - Arewa Agenda Hausa

Majalisar Dokokin Najeriya za ta Katse Hutunta Don Tattauna Muhimman Batutuwan ƙasar
Majalisar Dokokin Najeriya za ta Katse Hutunta Don Tattauna Muhimman Batutuwan ƙasar

Majalisar wakilan Najeriya za ta katse hutunta na shekara domin yin wani zama a ranar Laraba da nufin tattauna muhimman batutuwan da suka buƙaci majalisar ta yi magana a kan su.

Bayanin hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa daga magatakarda na majalisar Yahaya Danzaria.

Taron zai ƙunshi tattaunawa da matasa ƴan Najeriya a wani taro da kakakin majalisar Tajuddeen Abbas zai karɓi baƙunci.

Taron zai haɗa da shugabannin matasa da ɗalibai daga manyan makarantu da ƙwararru matasa da kuma wakilai daga ƙungiyoyin matasa da ƙungiyoyin farar hula.

An tsara taron domin bai wa matasa ƴan Najeriya damar bayyana damuwarsu su kuma bayyana ra’ayoyinsu sannan su tattauna da jagororin majalisa kan matsalolin da suka shafi rayuwarsu da kuma gobensu.

Majalisar wakilan ta soma hutu ne ranar Talatar da ta gabata inda ta shirya dawowa ranar 17 ga watan Satumba.

Shi ma shugaban majalisar dattijai, Sanata Godswill kpabio ya kira taron gaggawa don tattauna al’amuran ƙasar, kamar yadda sanarwa daga magatakardan majalisar, Chinedu Akubueze ta bayyana.

Sai dai sanarwar ba ta yi cikakken bayani ba game da abin da taron zai mayar da hankali a kai.

Za a yi taron ranar Laraba, 31 ga watan Yuli, kwana ɗaya kafin gagarumar zanga-zangar da aka shirya yi a faɗin Najeriya.

The post Majalisar Dokokin Najeriya za ta Katse Hutunta Don Tattauna Muhimman Batutuwan ƙasar appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Akpabio ya Buƙaci Gwamnatin Tarayya ta Soke Wasu Ma’aikatun Gwamnati
Akpabio ya Buƙaci Gwamnatin Tarayya ta Soke Wasu Ma’aikatun Gwamnati

Shugaban Majalisar dattawan Najeriya Sanata Godswill Akpabio ya buƙaci gwamnatin tarayyata ta soke wasu ma’aikatun gwamnati, sannan ta yi garambawul a wasu, ta yadda za a samu ingantuwar aiki.

Yayin da yake jawabi jim-kadan kafin shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin 2024 a zauren majalisar, Sanata Akpabio ya ce hakan zai tabbatar da an gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.

Shugaban Majalisar dattawan ya shawarci gwamnati ta duba hanyoyin rage basukan da ta gada daga tsahuwar gwamnati.

Sanata Akpabio ya kuma bayyana cewa majalisa za ta bai wa ɓangaren zartarwa haɗin kai domin aiwatar da kasafin kuɗin yadda ya dace.

The post Akpabio ya Buƙaci Gwamnatin Tarayya ta Soke Wasu Ma’aikatun Gwamnati appeared first on Arewa Agenda Hausa.

An Samu Takaddama a Majalisar Dattawan Najeriya Kan Nada Sabbin Shugabannin Marasa Rinjaye
An Samu Takaddama a Majalisar Dattawan Najeriya Kan Nada Sabbin Shugabannin Marasa Rinjaye

An samu takaddama a majalisar dattijan Najeriya ranar Talata, bayan sanar da nadin shugabanni a bangaren marasa rinjaye da Shugaba Majalisar Godswill Akpabio ya yi.

Kujerar shugaban marasa rinjaye da ta mai tsawatarwa a bangaren marasa rinjaye sun kasance babu kowa tun bayan da kotun daukaka kara ta soke zaben Sanata Simon Davou Mwadkwon na PDP da Darlington Nwokocha na LP.

Kotu ta soke zaben sanata Simon Mwadkwon inda ta ba da umarnin sake gudanar da zabe.

Tun a makon jiya ne sanatocin jam’iyyar PDP suka gudanar da wani taron gaggawa kan batun maye guraben shugabannin marasa rinjaye.

Jaridar Punch ta ambato Sanata Garba Maidoki wanda ya yi jawabi ga manema labarai bayan taron, na cewa ‘yan majalisa bangaren adawa sun amince sun amince da fitar da sabon shugaban marasa rinjaye daga arewa ta tsakiya.

Don haka, yayin zaman majalisar na Talata, Godswill Akpabio ya sanar da Abba Moro na PDP a matsayin shugaban marasa rinjaye, yayin da Osita Ngwu shi ma daga PDP zai kasance mai tsawatarwa a bangaren marasa rinjaye.

Shugaban majalisar ya ce sabbin shugabannin marasa rinjayen sun samu rinjayen goyon bayan takwarorinsu.

Da yake gabatar da wnai kudurin jan hankali, Sanata Okechukwu Ezea na jam’iyyar LP ya nuna rashin amincewa da rashin shigar da jam’iyyarsa a shugabancin marasa rinjaye, inda ya bayyana lamarin a matsayin rashin adalci ga jam’iyyun marasa rinjaye.

Ana cikin hargitsi ne, sai Sanata Tony Nwoyi na LP ya zargi Godswill Akpabio da nada wa jam’iyyun adawa shugabanci.

The post An Samu Takaddama a Majalisar Dattawan Najeriya Kan Nada Sabbin Shugabannin Marasa Rinjaye appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Sanata Ifeanyi Ubah ya Sauya sheƙa Zuwa Jam’iyyar APC
Sanata Ifeanyi Ubah ya Sauya sheƙa Zuwa Jam’iyyar APC

Sanata Ifeanyi Ubah ya sauya sheƙa daga jam’iyyar YPP ya koma jam’iyyar APC mai mulki ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba, 2023.

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ne ya tabbatar da haka a wasiƙar da ya karanta yayin zamana majalisar.

A wasiƙar, Sanatan ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne saboda rikicin cikin gidan YPP da ya ƙi ci kuma ya ƙi cinyewa.

FCT Abuja – Sanata mai wakiltar mazaɓar Anambra ta kudu a majalisar dattawa, Sanata Ifeanyi Ubah, ya canza sheƙa daga Young Progressives Party (YPP) zuwa APC.

Daily Trust ta tattaro cewa hakan na ƙunshe ne a wata wasiƙa da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta a zauren majalisar ranar Alhamis.

Sanata Ubah ya yi bayani a cikin wasiƙar da Akpabio ya karanta cewa ya yanke shawarar barin jam’iyyar YPP ne sakamakon gaza shawo kan rigingimun cikin gida.

Sai dai Sanatan bai bayyana ainihin rikicin cikin gidan da yake nufi ba, wanda a cewarsa, shi ne dailin barin jam’iyyar YPP, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Wasiƙar ta kara da bayanin cewa Sanata Ubah ya koma APC ne da amincewar mutanen mazabarsa.

Ana ganin wannan sauya sheƙa ta ƙara ɗaga jam’iyyar APC, musamman a irin wannan lokacin da jam’iyyar ke kokarin ganin ta yaɗu a shiyyar Kudu maso Gabas.

Taƙaitaccen tarihin siyasar Sanata Ubah

A shekarar 2014, Ubah ya sha ƙashi a zaben gwamnan jihar Anambara karkashin inuwar jam’iyyar Labour Party.

Haka nan kuma INEC ta ayyana Ubah a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan Anambra ta kudu karkashin inuwar jam’iyyar YPP a ranar 24 ga watan Fabrairu, 2019.

A babban zaɓen da ya biyo bayan wannan, wanda aka yi a watan Fabrairu, 2023, Hukumar zaɓe ta sake ayyana Ubah, ɗan shekara 52 a matsayin wanda ya ci zaɓen Anambra ta kudu a karo na biyu.

The post Sanata Ifeanyi Ubah ya Sauya sheƙa Zuwa Jam’iyyar APC appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Yana da Kyau a Wasu Lokutan Maza su Riƙa bai wa Mata Jan Ragamar Siyasar ƙasar nan – Godswill Akpabio
Yana da Kyau a Wasu Lokutan Maza su Riƙa bai wa Mata Jan Ragamar Siyasar ƙasar nan – Godswill Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ce akwai bukatar mata su rike madafun iko.

Ya ce ya kamata maza su riƙa komawa gefe domin bai wa mata damar ɗarewa kujerun siyasa.

Ya bayyana cewa adadin mata da ake da su a kujerun shugabanci ya yi kaɗan a halin da ake ciki.

FCT, Abuja – Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya ce yana da kyau a wasu lokutan maza su riƙa bai wa mata jan ragamar siyasar ƙasar nan.

Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Abuja, a wajen wani taro na ƙasa da ƙasa kan rawar da mata ke takawa a shugabanci.

Cibiyar Nazarin Dokoki da Dimokuradiyya ta ƙasa (NILDS) ce ta shirya taron kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Akpabio ya ce akwai bukatar mata a siyasa

Akpabio ya bayyana cewa yana matuƙar sha’awar ganin mata riƙe da kujerun shugabanci na siyasa a Najeriya.

Sai dai yanayin siyasar da ake ciki a yanzu, ba su cika samun kujerun shugabancin ba sai dai a ba su muƙamai a gwamnati.

Shugaban ya ce adadin matan da yanzu haka ke a Majalisar Dattawan Najeriya sun yi kaɗan, inda yake ganin ya kyautu a ce sun wuce hakan.

Ya ƙara da cewa a bisa wannan dalilin ne yake ganin ya kamata maza su riƙa komawa gefe a wasu lokutan domin bai wa mata damar samun kujerun siyasa.

Akpabio ya nemi a yaƙi wariyar jinsi

Akpabio ya kuma bayyana cewa akwai buƙatar a yaƙi wariyar jinsin da ake nunawa mata a cikin al’umma musamman yayin neman shugabanci.

Ya ce wannan wani abu ne da Cibiyar Nazarin Dokokin ya kamata ta yi da haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyin na kare haƙƙin mata kamar yadda The Punch ta wallafa.

Ya kuma ƙara da cewa akwai buƙatar a sauya yadda al’amura ke tafiya tun a baya da kuma yadda suke a yanzu, ta hanyar ƙarfafawa mata gwiwar su shiga siyasa.

The post Yana da Kyau a Wasu Lokutan Maza su Riƙa bai wa Mata Jan Ragamar Siyasar ƙasar nan – Godswill Akpabio appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Jam’iyyar APC ta yi Watsi da Jagororin Majalisa da Aka Sanar
Jam’iyyar APC ta yi Watsi da Jagororin Majalisa da Aka Sanar

Ga dukkan alamu sabon rikici na shirin ɓarkewa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a ƙasar nan.

Hakan na zuwa ne bayan shugabannin majalisa ta 10 sun sanar da sunayen jagororin majalisar ba tare da sanin uwar jam’iyya ba.

Jam’iyyar a nata ɓangaren ta yi fatali da sunayen ƴan majalisar da aka sanar inda tace ba haka tsarin fitar da su yake ba

FCT, Abuja – Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta nesanta kanta daga jagororin majalisa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da kakakin da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas suka sanar.

Shugabannin majalisar dai sun sanar da sabbin jagororin majalisar ne a zaman da aka gudanar ranar Talata, 4 ga watan Yuli.

Amma da yake jawabi ga gwamnonin jam’iyyar, Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar na ƙasa, ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta da hannu a cikin sunayen ƴan majalisar da aka sanar, cewar rahoton Daily Trust.

Adamu ya ce shi ma sai dai ya ji raɗe-raɗi na yawo a kafafen watsa labarai cewa an naɗa jagororin majalisar.

Adamu bai san da cewa za a sanar da sunayen jagororin majalisar ba

Shugaban jam’iyyar ya ce duk da ya karɓi baƙuncin shugabannin majalisar lokacin da suka kai masa ziyara barka da Sallah a ƙarshen mako, bai san cewa za a sanar da sunayen jagororin majalisar ba.

A kalamansa:

“Amma yanzu kawai na ke ji a matsayin jita-jita a kafafen watsa labarai cewa an fitar da wasu sanarwoyi a majalisar dattawa da ta wakilai.”

“Hedikwatar jam’iyyar APC ta ƙasa da kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) bai fitar da wannan bayanin ba ko sanar da zaɓin jagororin ba.”

“Sannan har sai mun tattauna a tsakaninmu mun fitar sannan mu tura musu a rubuce wanda hakan shi ne abinda aka saba yi, ba mu da niyyar kaucewa daga wannan tsarin.”

“Domin haka kowace irin sanarwa da shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa, kakakin majalisar wakilai ko mataimakinsa suka yi, ba daga gare mu bane.”

The post Jam’iyyar APC ta yi Watsi da Jagororin Majalisa da Aka Sanar appeared first on Arewa Agenda Hausa.

2023: Kotu ta Umarci INEC da ta Wallafa Sunan Akpobio a Matsayin ‘Dan Takarar Sanata na APC
2023: Kotu ta Umarci INEC da ta Wallafa Sunan Akpobio a Matsayin ‘Dan Takarar Sanata na APC

FCT Abuja – Wata babban kotun tarayya da ke Abuja ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta amince kuma ta wallafa sunan Godswill Akpabio a matsayin dan takarar sanata na jam’iyyar APC mai wakiltar Akwai Ibom ta Arewa/Yamma a zaben 2023.

Mai shari’a Emeka Nwite, a cikin hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis, ya ce INEC ta saɓa doka da ta ƙi karbar sunan Akpabio ta kuma wallafa duk da cewa jam’iyyar APC ta aika da sunan a matsayin dan takararta, The Nation ta rahoto.

Dakaci karin bayani …

The post 2023: Kotu ta Umarci INEC da ta Wallafa Sunan Akpobio a Matsayin ‘Dan Takarar Sanata na APC appeared first on Arewa Agenda Hausa.