Sanata Ifeanyi Ubah ya Sauya sheƙa Zuwa Jam’iyyar APC

 

Sanata Ifeanyi Ubah ya sauya sheƙa daga jam’iyyar YPP ya koma jam’iyyar APC mai mulki ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba, 2023.

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ne ya tabbatar da haka a wasiƙar da ya karanta yayin zamana majalisar.

A wasiƙar, Sanatan ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne saboda rikicin cikin gidan YPP da ya ƙi ci kuma ya ƙi cinyewa.

FCT Abuja – Sanata mai wakiltar mazaɓar Anambra ta kudu a majalisar dattawa, Sanata Ifeanyi Ubah, ya canza sheƙa daga Young Progressives Party (YPP) zuwa APC.

Daily Trust ta tattaro cewa hakan na ƙunshe ne a wata wasiƙa da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta a zauren majalisar ranar Alhamis.

Sanata Ubah ya yi bayani a cikin wasiƙar da Akpabio ya karanta cewa ya yanke shawarar barin jam’iyyar YPP ne sakamakon gaza shawo kan rigingimun cikin gida.

Sai dai Sanatan bai bayyana ainihin rikicin cikin gidan da yake nufi ba, wanda a cewarsa, shi ne dailin barin jam’iyyar YPP, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Wasiƙar ta kara da bayanin cewa Sanata Ubah ya koma APC ne da amincewar mutanen mazabarsa.

Ana ganin wannan sauya sheƙa ta ƙara ɗaga jam’iyyar APC, musamman a irin wannan lokacin da jam’iyyar ke kokarin ganin ta yaɗu a shiyyar Kudu maso Gabas.

Taƙaitaccen tarihin siyasar Sanata Ubah

A shekarar 2014, Ubah ya sha ƙashi a zaben gwamnan jihar Anambara karkashin inuwar jam’iyyar Labour Party.

Haka nan kuma INEC ta ayyana Ubah a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan Anambra ta kudu karkashin inuwar jam’iyyar YPP a ranar 24 ga watan Fabrairu, 2019.

A babban zaɓen da ya biyo bayan wannan, wanda aka yi a watan Fabrairu, 2023, Hukumar zaɓe ta sake ayyana Ubah, ɗan shekara 52 a matsayin wanda ya ci zaɓen Anambra ta kudu a karo na biyu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com