Babban Bankin Najeriya (CBN) Archives - Arewa Agenda Hausa

Shugaba Tinubu ya Naɗa Olayemi Cardoso a Matsayin Sabon Gwamnan Babban Bankin Najeriya
Shugaba Tinubu ya Naɗa Olayemi Cardoso a Matsayin Sabon Gwamnan Babban Bankin Najeriya

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana sunan Dr. Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) na tsawon shekara biyar, da zarar Majalisar Dattijan ƙasar ta amince da shi.

Wannan bayani na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya fitar, yau Juma’a.

Bayanin ya ce shugaban ƙasar ya ɗauki matakin ne bisa dogaro da sashe na 8 (1) na dokar Babban Bankin Najeriya ta 2007, wadda ta bai wa shugaban ƙasar karfin ikon naɗa shugaba da mataimaka huɗu na Babban Bankin.

Sanarwar ta kuma bayyana sunayen wasu mutane huɗu da shugaban ya amince da su domin naɗawa a matsayin mataimakan gwamnan babban bankin na Najeriya.

Mataimakan su ne:

(1) Mrs. Emem Nnana Usoro

(2) Mr. Muhammad Sani Abdullahi Dattijo

(3) Mr. Philip Ikeazor

(4) Dr. Bala M. Bello

Shugaban ya buƙaci waɗanda aka naɗan su mayar da hankali wajen aiwatar da muhimman sauye-sauyen da aka ɓullo da su a bankin a ƙoƙarin gwamnatinsa na sake fasalin tattalin arziƙin ƙasar.

A watan Yunin wannan shekara ne shugaban ƙasar ya dakatar da gwamnan babban bankin ƙasar, Godwin Emefiele.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayyar ƙasar ta ce an dakatar da Emefiele ne ne domin gudanar da bincike da kuma kasancewa wani ɓangare na ƙoƙarin sauya fasalin harkokin kuɗi a ƙasar.

Kwanaki kaɗan bayan dakatar da shi ne rundunar tsaron ciki ta ƙasar, DSS ta tabbatar da kamawa tare da tsare tsohon gwamnan babban bankin.

DSS ɗin ta kuma gurfanar da Emefiele a gaban kotu bisa tuhumar sa da laifuka daban-daban.

The post Shugaba Tinubu ya Naɗa Olayemi Cardoso a Matsayin Sabon Gwamnan Babban Bankin Najeriya appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Babban Bankin Najeriya ya Gargaɗi Bankuna a Kan Hulɗar Kasuwanci da ƙasashen Kamaru,Vietnam da Croatia
Babban Bankin Najeriya ya Gargaɗi Bankuna a Kan Hulɗar Kasuwanci da ƙasashen Kamaru,Vietnam da Croatia

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bukaci bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi a ƙasar su ƙara sanya ido wajen harkokin kasuwanci da mutane daga ƙasashen Kamaru da Croatia da kuma Vietnam.

Matakin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan tsare-tsare da hada-hadar kuɗi Mista Chibuzo Efobi ya fitar a Abuja.

A cewar CBN, bankunan Najeriya da sauran cibiyoyin kudi na bukatar su yi hankali da yin hulɗar kasuwanci da waɗancan ƙasashe, saboda a baya-bayan nan, Hukumar sa ido kan ayyukan halatta kuɗin haram da kuɗaɗen aikata ta’addanci a duniya (FAFT) ta sanya su a jerin ƙasashen da ake sanya wa ido.

Sanarwar ta ce, “An janyo hankalin bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi ga sakamakon da hukumar FAFT ta gudanar daga ranar 21 – 23 ga watan Yuni, 2023 inda ta sanya Kamaru da Croatia da kuma Vietnam a cikin jerin ƙasashe da za a ƙara sa wa ido”

“Bugu da ƙari, Koriya ta Kudu da Iran da Myanmar sun ci gaba da kasancewa cikin jerin ƙasashen da ake sanya wa ido.”

A watan Fabrairu, hukumar FAFT dai ta sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da za a sawa ido amma sanarwar baya-bayan nan daga Hukumar tattara bayanan sirri ta Najeriya ta ce yunkurin da ƙasar ta yi na ficewa daga cikin jerin ya tilastawa FATF rage wuraren da aka ga tana da rauni daga 84 zuwa 15.

The post Babban Bankin Najeriya ya Gargaɗi Bankuna a Kan Hulɗar Kasuwanci da ƙasashen Kamaru,Vietnam da Croatia appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Takardun ƙudi: Ban Umarci CBN ya ƙi bin Umarnin Kotu ba – Buhari
Takardun ƙudi: Ban Umarci CBN ya ƙi bin Umarnin Kotu ba – Buhari

Fadar shugaban Najeriya ta ce Babban Bankin ƙasar ba shi da wani dalili na ƙin bin umarnin Kotun Ƙoli kan sabbin takardun kuɗi don fakewa da sunan jiran umarni daga Shugaba Muhammadu Buhari.

Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan kafafen yaɗa labarai, Garba Shehu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa inda ya ce Shugaban ƙasar bai umarci atoni janar na ƙasa, Abubakar Malami da Gwamnan CBN, Godwin Emiefele su ƙi martaba umarnin kotu ba da ya shafi gwamnati da wasu ɓangarorin.

A ranar 3 ga watan Maris ne Kotun ƙolin ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsofaffin takardun ƙudi har zuwa 31 ga watan Disamban bana.

Umarnin kuma ya zo ne bayan da gwamnonin jihohi 16 suka ƙalubalanci matakin sauya fasalin kuɗin.

Jihohi 16 ƙarƙashin jagorancin Kaduna da Kogi da Zamfara sun buƙaci kotun ƙolin ta soke matakin gwamnatin bisa dalilan cewa hakan ya jefa ƴan Najeriya cikin ƙunci da wahala.

Kotun ta ƙara da cewa rashin martaba umarnin kotun na ranar 8 ga watan Fabrairu, alama ce ta mulkin kama-karya inda ta bayyana cewa shugaban ya saɓa wa Kundin tsarin mulkin ƙasa a yadda ya bai wa CBN umarnin sake fasalta kuɗin ƙasar.

Sanarwar dai ta ce Shugaban ƙasar babban mai mutunta dokoki ne kuma babu adalci a yadda ake yi sukar Shugaban da yi masa mummunan zato.

The post Takardun ƙudi: Ban Umarci CBN ya ƙi bin Umarnin Kotu ba – Buhari appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Zan Rufe duk Bankin da ya ƙi Karɓar Tsofaffin Takardun Kuɗi – Gwamnan Anambra
Zan Rufe duk Bankin da ya ƙi Karɓar Tsofaffin Takardun Kuɗi – Gwamnan  Anambra

Gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya Charles Soludo ya umarci mazauna jihar da su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun naira 200 da 500 da 1,000 tare da sababbin takardun kuɗin a ko’ina cikin jihar.

Cikin wata sanarwa ta musamman da Charles Soludo – wanda tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ne – ya fitar, ya ce babban bankin ƙasar ya umarci bankunan kasuwanci a ƙasar da su ci gaba da biyan masu ajiyar kuɗi a bankunan da tsofaffin takardun kuɗi.

Sannan kuma su ci gaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗin a duk lokacin da aka gabatar da su.

Gwamnan jihar ta Anambra ya ce ya tabbatar da sahihancin umarnin yayin wata hira da yayi da gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ta wayar tarho a ranar lahadi da daddare.

Soludo ya ce gwamnan CBN ya bayar da wannan umarnin ne yayin wani taro da babban bankin ya yi da bankunan ƙasar da aka yi a ranar Lahadi 12 ga watan Maris.

Gwamnan na Anambra ya kuma buƙaci al’ummar jihar da su kai ƙarar dukkan bankin da ya ƙi bin umarnin babban bankin na biya da karɓar tsofaffin takardun kuɗin.

Yana gargaɗin cewa gwamnatinsa za ta rufe duk bankin da ya bijire wa wannan umarnin.

A ranar 3 ga watan Maris ne kotun ƙolin Najeriya ya yanke hukuncin ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin ƙasar har zuwa 31 ga watan Disamban 2023.

Wasu jihohin kasar ne dai suka shigar da ƙara a gaban kotun, suna neman a ɗage wa’adin da CBN ya sanya na daina amfani tsofaffin kuɗin.

The post Zan Rufe duk Bankin da ya ƙi Karɓar Tsofaffin Takardun Kuɗi – Gwamnan  Anambra appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Tsofaffin Takardun Kuɗi: Kotun ƙoli ta ce a Ci gaba da Amfani da N200, N500 da N1000
Tsofaffin Takardun Kuɗi: Kotun ƙoli ta ce a Ci gaba da Amfani da N200, N500 da N1000

Kotun ƙolin Najeriya ta yanke hukuncin cewa za a ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗin ƙasar har zuwa 31 ga watan Disamban 2023.

A lokacin da ta yanke hukuncin, kotun ta ce ba a sanar da al’umma da wuri ba, kamar yadda dokar Babban Bankin Najeriya ta tanada kafin shugaban ƙasa ya bayar da umarnin sake fasalin kuɗin da kuma janye tsofaffi daga hannun al’umma.

Saboda haka kotun ta ce umurnin ba ya kan doka, sannan aiwatar da shi haramun ne.

Tawagar masu yanke hukuncin bakwai ne suka yi zaman kotun ƙolin kuma suka amince a ci gaba da amfani da N1000 da N500 da kuma N200 a matsayin kuɗin ƙasa har sai nan da ranar 31 ga watan Disambar wannan shekarar.

Kotun ta kuma soke matakin Gwamnatin Tarayya na sake fasalin naira, tana cewa matakin ya ci karo da kundin tsarin mulki na 1999.

Tun da fari gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara ne suka shigar da gwamnati ƙara, kuma ƙarar da suka shigar aka yi amfani da ita a matsayin hujja wajen yanke wannan hukunci.

A watan jiya kuma wasu gwamnoni suka ƙara bin bayansu wajen shigar da ƙarar, abin da ya janyo kotun ƙolin ta dakatar da wa’adin na wucin gadi da aka sanya na daina amfani da tsofaffin kuɗin.

A hukuncin da ya yanke a ranar Juma’a mai shari’a Emmanuel Agim, ya ce sahalewar da Shugaba Buhari ya yi wa CBN na janyo takardun tsofaffin kuɗi ba daidai ba ne.

“Duba da bayanan da aka gabatar, Na fuskani ba a bai wa al’umma wani wa’adi ba na azo a gani ba, kamar yadda sashe na 20 na dokar CBN ta 2007 ya bayyana, gabanin shugaban ƙasa ya bayar da umarnin sake fasalin naira da janye tsofaffin takardun. A don haka, yanzu umarnin da shugaba ya bayar ba daidai ba ne kuma aiwatar da sauyin shi ma ba ya kan daidai.” Kamar yadda ya yi bayani.

A baya bayan nan ne Shugaba Buhari ya bai wa CBN umarnin sake fito da tsohuwar takardar kuɗi ta N200 domin ci gaba da amfani da ita har zuwa ranar 10 ga watan Afirilu, domin sassauta halin da ‘yan ƙasar suka tsinci kansu na rashin samun sabbin takardun naira.

The post Tsofaffin Takardun Kuɗi: Kotun ƙoli ta ce a Ci gaba da Amfani da N200, N500 da N1000 appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Sauya Naira: APC ta Goyi Bayan Gwamnoni, ta Bukaci Buhari ya Mutunta Doka
Sauya Naira: APC ta Goyi Bayan Gwamnoni, ta Bukaci Buhari ya Mutunta Doka

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sake kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tsoma baki cikin manufofin tsuke bakin aljihu da ke kawo wa mutane wahala.

Shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu, a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kusan sa’o’i 2 na ganawar sirri da gwamnonin APC, ya ce jam’iyyar za ta tabbatar da hukuncin da kotun koli ta yanke wanda ke rike da ka’idar doka ta tsofaffin takardun kudi.

Adamu ya ce, ya kamata babban bankin Najeriya (CBN) da babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) su mutunta doka ta hanyar tabbatar da hukuncin da kotun koli ta yanke kan musayar kudade.

Ya ce “Mun bukaci babban mai shari’a na tarayya da gwamnan babban bankin Najeriya CBN da su mutunta umarnin kotun koli na wucin gadi wanda har yanzu ake ci gaba da aiki. Cewa taron yana kira ga mai girma shugaban kasa da ya sa baki wajen warware matsalolin da ke jawo wa al’umma wannan babbar matsala da tattalin arziki.”

A halin da ake ciki kuma, a cikin sa’o’i na ganawar sirrin, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya mamaye sakatariyar jam’iyyar.

An boye bayanan zuwan sa gidan Buhari domin ya ki yin jawabi ga manema labarai.

Taron ya samu halartar gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai; Mohammed Bello of Niger, Abdulahi Sule of Nasarawa, Yahaya Bello of Kogi state, Inuwa Yahaya of Gombe state, Bello Matawalle of Zamfara , Mai Mala Buni of Yobe, Abubakar Badaru of Jigawa , Biodun Oyebanji of Ekiti, Simone Lalong of Plateau, Atiku Bagudu na jihar Kebbi, Babajide Sanwolu na jihar Legas, da mataimakan gwamnonin jihar Imo, Placid Njoku, da Mohammed Manir Yakubu na jihar Katsina.

The post Sauya Naira: APC ta Goyi Bayan Gwamnoni, ta Bukaci Buhari ya Mutunta Doka appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Babban Bankin Najeriya ya Musanta Rahotan da ke Cewa ya Umarci Bankuna su Ci gaba da Karɓar Tsofaffin Kuɗi
Babban Bankin Najeriya ya Musanta  Rahotan da ke Cewa ya Umarci Bankuna su Ci gaba da Karɓar Tsofaffin  Kuɗi

Babban Bankin Najeriya ya janye batun ci gaba da karɓar takardun kuɗi na N1,000 da 500, bayan a baya ya tabbatar wa BBC cewa ya umurci bankuna su ci gaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗin.

Tun farko, Babban Bankin na Najeriya ta bakin daraktansa na yaɗa labaru, Osita Nwanisobi ya tabbatar wa BBC cewar ya bai wa bankuna umurnin ci gaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗi na 1,000 da kuma 500.

Sai daga baya bankin ya fitar da wani takarda ɗauke da sa hannun daraktar yaɗa labarun na CBN inda yake musanta hakan.

Bayan da BBC ta sake kiran sa domin tantance bayanin, Mr Nwanisobi ya ce bai da abin da zai fada baya ga wannan sanarwa da ya fitar daga baya.

The post Babban Bankin Najeriya ya Musanta  Rahotan da ke Cewa ya Umarci Bankuna su Ci gaba da Karɓar Tsofaffin  Kuɗi appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Gwamnan Bankin Najeriya ya Umarci Bankunan Kasar da su Fara Karbar Tsofaffin N1000 da N500
Gwamnan Bankin Najeriya ya Umarci Bankunan Kasar da su Fara Karbar Tsofaffin N1000 da N500

Gwamnan bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ya umurci dukkan bankunan Najeriya su fara karban tsaffin kudaden N1000 da N500 daga hannun jama’a yanzu.

Gwamnan ya bayyana cewa ya canza shawarar cewa kowa ya kai CBN kadai, rahoton Vanguard.

Amma dai bankin yace sharadin shine mutum N500,000 kadai zai iya kaiwa bankunan.

Duk kudin da ya wuce N500,000 mutum ya kai bankin CBN, riwayar TheCable.

Diraktan Sadarwa na bankin, Osita Nwanisobi, ya tabbatar da labarin inda ya bayyana cewa:

“Kawai na masu N500,000 da abinda yayi kasa ne.”

Saurari karin bayani….

The post Gwamnan Bankin Najeriya ya Umarci Bankunan Kasar da su Fara Karbar Tsofaffin N1000 da N500 appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Babban Bankin Najeriya ya yi Gargaɗi Kan Yin liƙi da Kudi a Lokacin Biki
Babban Bankin Najeriya ya yi Gargaɗi Kan Yin liƙi da Kudi a Lokacin Biki

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya jaddada gargaɗinsa ga jama’a a kan yin liƙi da takardar kuɗin ƙasar ta Naira a lokacin biki.

A sanarwar da hukumar bankin ta fitar ta Twitter ta ce, saɓa wa dokar bankin ta 2007 laifi ne da zai sa a ci tarar mutum naira dubu 50 ko kuma ɗaurin gidan yari da bai wuce wata shida ba ko kuma duka biyu.

Wasu ‘yan Najeriya suna da al’adar yin abubuwa kamar su kek da takardar kuɗin ƙasar ta Naira domin aika wa ‘yan uwa da masoya a lokacin bikin ranar haihuwa ko kuma wani biki na aure da makamantansu.

Haka kuma sukan yi liƙi da takardar ta Naira a lokacin bukukuwa.

Laifukan da bankin ya zayyana da ake yi da takardar kuɗin sun haɗa da, liƙi da sayarwa da cukuikuyewa da rubutu ko zane ko tattaka su ko rawa a kansu da sauransu.

Babban Bankin na Najeriya ya fitar da wannan gargaɗi ne a daidai lokacin da takardar kuɗin ke ƙaranci sakamakon canjin takardar naira ta 200 da 500 da kuma 1,000 da bankin ya yi.

The post Babban Bankin Najeriya ya yi Gargaɗi Kan Yin liƙi da Kudi a Lokacin Biki appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Babu Bukatar Dage Wa’adin 10 ga Watan Fabrairu na Daina Amfani da Tsoffin Kudi – Emefiele
Babu Bukatar Dage Wa’adin 10 ga Watan Fabrairu na Daina Amfani da Tsoffin Kudi – Emefiele

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya ce babu gudu babu ja da baya a wa’adin 10 ga watan Fabrairu na daina amfani da tsoffin kudi.

Emefiele ya ce za a fara kama yan POS da ke chajin kudi fiye da N200 yayin cire kudi a wajensu.

Ya ce lallai idan aka aiwatar da wannan manufar yadda ya kamata, hauhawan farashin kayayyaki zai sauka da kaso 4.

Abuja – Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya bayyana cewa babu bukatar dage wa’adin 10 ga watan Fabrairu na daina amfani da tsoffin kudi.

Mun dai ji cewa kotun koli ta yake hukuncin wucin gadi inda ta dakatar da gwamnatin tarayya da CBN daga aiwatar da wa’adin na daina amfani da tsoffin Naira.

Sai dai kuma, Emefiele yayin ziyarar da ya kai ma’aikatar harkokin waje don tattauna manufar kudin kasar, ya ce dage wa’adin bai da amfani, rahoton The Nation.

Ya ce:

“Lamarin ya fara daidaita tun bayan da aka fara biyan kudi a kan kanta don kari a kan cire kudi ta ATM.

“Saboda haka, babu bukatar duba yiwuwar dage wa’adin na 10 ga watan Fabrairu.”

Gwamnan babban bankin ya kuma bayyana cewa za a kama masu POS da ke chajin fiye da N200 wajen cire kudi kuma za a kai su gidan yari idan aka kama su.

Daily Trust ta kuma nakalto Emefiele yana cewa:

“Wasu daga cikin shugabanninmu suna siyan sabbin kudi suna boyewa saboda wasu dalilai kuka ni ba za zurfafa kan wannan batun ba.”

Manufar CBN zai rage yawan hauhawan farashin kayayyaki, Emefiele

Har ila yau, gwamnan CBN din ya ce babban bankin kasar na sane da mawuyacin halin da yan Najeriya ke ciki, yana mai cewa aiwatar da manufar na iya zabtare kaso 4 na adadin hauhawan farashin kayayyaki.

Ya kuma yi bayanin cewa yawan kudaden da ke zagawa yanzu haka ya kai kimanin naira biliyan 700.

The post Babu Bukatar Dage Wa’adin 10 ga Watan Fabrairu na Daina Amfani da Tsoffin Kudi – Emefiele appeared first on Arewa Agenda Hausa.