Mambila Archives - Arewa Agenda Hausa

Tun 2017 Aka Ware wa Aikin Mambila Kudi Amma ba Abin da Aka yi – Sanata Suswam
Tun 2017 Aka Ware wa Aikin Mambila Kudi Amma ba Abin da Aka yi – Sanata Suswam

Kwamitin lura da harkokin wuta na Majalisar Dattawan Najeriya ya bayyana aikin gina madatsar ruwa ta samar da wutar lantarki na Mambila a matsayin fata kawai duk da biliyoyin naira da aka kashewa aikin.

Ministan wutar lantarki Injiniya Abubakar D. Aliyu shi ne ya bayyana haka duk da dimbin kudin da ake ware wa aikin a kasafin kudi na shekaera-shekara da ya kai biliyoyin naira.

Jaridar DailyTrust ta ruwaito ministan na fadar hakan ne yayin da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon-kasa, EFCC, ke gudanar da bincike kan aikin.

Batun ya taso ne yayin zaman kare kasafin kudi na 2023 ranar Talata tare da Ministan wutar lantarki da sauran hukumomi da ke karkashin ma’aikatar.

Shugaban kwamitin Sanata Gabriel Suswam (PDP, Benue), ya ce abin takaici ne duk da dimbin kudin da aka yi ta ware wa aikin wanda tun shekara 30 baya aka tsara shi, ba abin da aka yi a aikin.

Sanatan ya ce tun 2017, ake ware wa aikin na Mambila kudi amma ba abin da aka yi duk da matsin lambar da Majalisun Dokoki da kuma ‘yan Najeriya suke yi.

Aikin madatsar ruwan wanda zai samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 3,050, idan aka kammala shi zai kasance mafi girma a Najeriya sannan kuma daya daga cikin mafiya girma a Afirka.

The post Tun 2017 Aka Ware wa Aikin Mambila Kudi Amma ba Abin da Aka yi – Sanata Suswam appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Sanata Teslim Folarin ya yi Karin Bayani Kan Aikin Wutar Lantarkin Mambila
Sanata Teslim Folarin ya yi Karin Bayani Kan Aikin Wutar Lantarkin Mambila

Teslim Folarin ya yi bayanin abin da ya jawo bata lokaci a kwangilar Mambila.

‘Dan majalisar yana sa rai nan da karshen shekara ‘yan kwangila su soma aiki.

Folarin ya bayyana cewa duk an shawo kan wasu matsaloli da ake fama da su.

Abuja – A ranar Litinin, 27 ga watan Satumba, 2021, majalisar dattawan Najeriya tace shari’a a kotu suka hana a iya fara aikin wutar lantarkin Mambila.

Jaridar Daily Trust ta rahoto ‘yan majalisar dattawan kasar suna cewa an magance duk wasu kalubale da suka jawo aka gaza fara yin wannan kwangila.

Majalisar dattawan tace ana sa ran ‘yan kwangila su isa yankin, su fara aiki kafin karshen shekara.

Teslim Folarin ya karbi rahoton kwamiti

Shugaban kwamitin da ya shafi irin wadannan ayyukan a majalisar, Sanata Teslim Folarin, ya yi wannan bayani da yake karbar wani rahoton aikin kwangilar.

Teslim Folarin yace an gamu da cikas ne saboda sai da hukumar da ke kula da cigaban yankin Arewa maso gabashin Najeriya ya sake duba wannan aikin.

‘Dan majalisar yace NEDC ta kawo takardun aikin da TWG suka yi a kan yadda za a yi kwangilar.

Kamar yadda jaridar ta Daily Trust ta rahoto, Folarin yace an gabatar da wadannan takardun a gaban majalisar tarayya domin a dauki matakin da ya dace.

“Bayan nan majalisar tarayyan da kwamitin TWS sun kafa wani karamin kwamiti da zai kula da harkar kudi a karkashin jagorancin shugaban bankin NEXIM.”

“A shekarar nan aka kaddamar da kwamitin, kuma aka ce ya gabatar da rahoto a makonni shida.”

“Wannan kwamiti ne aka ba nauyin tsara yadda za a samu kudin yin kwangilar, ana lissafin Naira biiliyan 1.7, wanda shi ne 30% na kudin kwangilar, $5.7bn.”

“Ba ni da wani haufi cewa duk an shawo kan wadannan da ma wasu abubuwan, kuma nayi imani za a samu takarda a kan yadda za a iya aiwatar da aikin.”

The post Sanata Teslim Folarin ya yi Karin Bayani Kan Aikin Wutar Lantarkin Mambila appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Gwamnatin Shugaba Buhari ta Fitar da Hotunan Aikin Wutar Lantarki na Zungeru
Gwamnatin Shugaba Buhari ta Fitar da Hotunan Aikin Wutar Lantarki na Zungeru

Yayin da ake ci gaba da fuskantar karshen 2021, gwamnatin Buhari ta fitar da hotunan aikin wutan lantarki na Zungeru.

An watsa wasu hotuna a kafafen sada zumunta da ke nuni da aikin tashar wutan lantarkin ya jima da yin nisa.

Wannan na zuwa ne bayan da bincike ya nuna gwamnatin tarayya ba ta fara aikin komai na tashar wutan Mambila ba.

Abuja – Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fitar da wasu hotuna a wani bangare na nuna wa ‘yan Najeriya tana aikin tashar wutan lanatarki ta Zungeru dake jahar Neja.

A baya, gwamnatin Najeriya ta fara aikin tashar ne tun a shekarar 2013, inda ta nufi kammala aikin a shekarar 2018 wanda kuma hakan bai samu ba, wannan yasa a ka sake sanya watan Disambar 2021 a matsayin lokacin da za a kammala aikin, kamar yadda Wikipedia ta tattaro.

Legit.ng Hausa kafar yanar gizo ta Afrik 21 ta ce an ware makudan kudaden da suka kai dalolin Amurka biliyan 1.3 don wannan aiki.

A wasu hotuna da wani hadimin shugaba Buhari ta fannin yada labarai Bashir Ahmad, ya fitar ta shafinsa na Facebook yau Talata 28 ga watan Satumba, an ga wuraren da ake aikin, tare da nuna alamun lallai aikin ya yi nisa.

A rubutunsa, Bashir ya ce:

“Tashar Wutar Lantarki ta Zungeru ita ce tashar wutar lantarki mai karfin megawatt 700 (940,000 hp) da ake ginawa. Idan aka kammala ta, za ta zama tashar wutar lantarki ta biyu mafi girma a kasar, bayan Tashar Wutar Lantarki ta Kainji mai karfin megawatts 760 (1,020,000 hp).”

The post Gwamnatin Shugaba Buhari ta Fitar da Hotunan Aikin Wutar Lantarki na Zungeru appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Dalilin da Yasa Aikin Wutar Lantarkin Mambila Bai Tabbata ba – Garba Shehu
Dalilin da Yasa Aikin Wutar Lantarkin Mambila Bai Tabbata ba – Garba Shehu

Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da ya hana yin aikin wutar Mambila wanda shekaru 40 kenan da ake maganar sa.

Hadimin shugaban kasan Najeriya, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai.

A cewar Shehu, rigima ce ta barke tsakanin dan kwangilar da kuma gwamnati, hakan ya hana banki ba shi bashi.

FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta bayyana kwararan dalilan da suka janyo aikin wutar lantarki na Mambila da ke jahar Taraba ya kasa tabbata tsawon lokaci ba a kammala ba.

Kamar yadda BBC Hausa ta bayyana, har wakilin BBC da kansa ya je wurin da aka bayar don yin tashar wutar lantarkin amma ya ga ba a fara yin aikin ba.

Garba Shehu ya bayyana kwararan dalilan da suka dakatar da aikin

BBC ta samu nasarar tattaunawa da mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu inda ya bayyana dalilin da suka sa aikin bai tabbata ba.

A cewar Garba Shehu:

“Kudin da aka kididdiga za su isa a kammala aikin gabadaya sun kai sama da $4,000,000 wanda aka tsara cewa bashi za a amsa a wurin wani banki dake kasar China zai bayar.”

Shehu ya ce dan kwangilar ya kai karar gwamnatin Najeriya, hakan ya dakatar da aikin

Saidai kamar yadda BBC ta rawaito, Shehu ya ce wata rigima ce ta barke tsakanin gwamnatin Najeriya da dan kwangilar daga nan bankin ya dakatar da bayar da bashin.

Shehu ya bayyana cewa:

“Wani dan kasuwa Leno Adesanya ya yi ikirarin cewa gwamnati ta ba shi kwangilar kawo ma’aikatan da za su yi aikin tashar wutar Mambila.”

“Sai dai da aka bincika an gano cewa ba a gabatar da kwangilar zuwa ofishin tantance kwangiloli bai ba don amincewa da ita.”

“Sakamakon haka ne dan kwangilar ya maka gwamnatin Najeriya kara har wurin kwamitin daidaito na ‘yan kasuwa dake kasar Paris inda ya bukaci gwamnatin Najeriya ta biya shi $200,000,000 sannan ya saki kwangilar, sakamakon haka ya janyo China ta dakatar da bayar da bashin.”

Shehu ya ce aikin zai tabbata ne da zarar dan kwangilar ya janye karar da ya kai gwamnati.

The post Dalilin da Yasa Aikin Wutar Lantarkin Mambila Bai Tabbata ba – Garba Shehu appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Bincike ya Gano Cewa Har Yanzu ba a Soma Aikin Tashar Wutar Lantarkin Mambila ba
Bincike ya Gano Cewa Har Yanzu ba a Soma Aikin Tashar Wutar Lantarkin Mambila ba

Shekaru kusan 40 da bada kwangilar Mambila, har yanzu babu abin da aka tabuka.

Idan aikin ya kammala, Najeriya za ta samu karin karfin wuta na megawatt 3, 000.

A halin yanzu mutane miliyan 200 a kasar suna raba megawatt 5,000 zuwa 5400 ne.

Taraba – BBC Hausa ta gudanar da wani bincike na musamman a kan tashar wutar lantarkin Mambila inda ta gano cewa har yau ba a soma wannan aikin ba.

Shekara 39 kenan da gwamnatin shugaba Shehu Shagari ta bada kwangilar samar da wutar lantarki ta tashar Mambila, kawo yanzu babu labarin wannan aiki.

A shekarar 1982 aka tsara cewa tashar za ta samar da megawatt 2600 na karfin wuta idan an gama aikin.

Amma da ‘dan jaridar BBC ya ziyarci tashar, sai ya gano cewa ba a fara yin aikin ba. ‘Dan jaridar ya je har gangaren ruwa na Tambi wanda yana cikin tsarin tashar.

Duk da cewa mota ba ta iya zuwa wannan wuri, ‘dan jaridar ya hau babur, inda ya shafe sa’o’i biyar yana tafiya, daga baya sai ya karasa tashar lantarkin a kafa.

Shekara da shekaru babu labari

Shugabanni goma aka yi a Najeriya amma ba su iya cika alkawarin da aka yi ba. Shugabannin su ne; Shehu Shagari, Muhammadu Buhari da Ibrahim Babangida.

Sai Ernest Shonekan, Sani Abacha da Abdussalami Abubakar. Daga nan sai Olusegun Obasanjo, Ummaru ‘Yar’adua, Goodluck Jonathan sai Buhari (ya dawo).

Har yanzu aiki bai kankama ba?

Rahoton yace mafi yawan hotunan da ake gani a shafukan yanar gizo a kan wannan aiki, na bogi ne.

Mutane suna dauko hotunan takwarar tashar Mambila, madatsar ruwar Kashimbila (duk a jahar Taraba), suna yada wa da sunan tashar wutar lantarkin Mambila.

A wata hira da aka taba yi da Injiniya Saleh Mamman a lokacin yana Ministan wutar lantarkin Najeriya, yace batun wannan aikin tamkar tatsuniya ce kurum.

The post Bincike ya Gano Cewa Har Yanzu ba a Soma Aikin Tashar Wutar Lantarkin Mambila ba appeared first on Arewa Agenda Hausa.