Gwamnatin Shugaba Buhari ta Fitar da Hotunan Aikin Wutar Lantarki na Zungeru

 

Yayin da ake ci gaba da fuskantar karshen 2021, gwamnatin Buhari ta fitar da hotunan aikin wutan lantarki na Zungeru.

An watsa wasu hotuna a kafafen sada zumunta da ke nuni da aikin tashar wutan lantarkin ya jima da yin nisa.

Wannan na zuwa ne bayan da bincike ya nuna gwamnatin tarayya ba ta fara aikin komai na tashar wutan Mambila ba.

Abuja – Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fitar da wasu hotuna a wani bangare na nuna wa ‘yan Najeriya tana aikin tashar wutan lanatarki ta Zungeru dake jahar Neja.

A baya, gwamnatin Najeriya ta fara aikin tashar ne tun a shekarar 2013, inda ta nufi kammala aikin a shekarar 2018 wanda kuma hakan bai samu ba, wannan yasa a ka sake sanya watan Disambar 2021 a matsayin lokacin da za a kammala aikin, kamar yadda Wikipedia ta tattaro.

Legit.ng Hausa kafar yanar gizo ta Afrik 21 ta ce an ware makudan kudaden da suka kai dalolin Amurka biliyan 1.3 don wannan aiki.

A wasu hotuna da wani hadimin shugaba Buhari ta fannin yada labarai Bashir Ahmad, ya fitar ta shafinsa na Facebook yau Talata 28 ga watan Satumba, an ga wuraren da ake aikin, tare da nuna alamun lallai aikin ya yi nisa.

A rubutunsa, Bashir ya ce:

“Tashar Wutar Lantarki ta Zungeru ita ce tashar wutar lantarki mai karfin megawatt 700 (940,000 hp) da ake ginawa. Idan aka kammala ta, za ta zama tashar wutar lantarki ta biyu mafi girma a kasar, bayan Tashar Wutar Lantarki ta Kainji mai karfin megawatts 760 (1,020,000 hp).”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here