Ƙarancin Man Fetur ya Jawo Zanga-Zanga a Sri Lanka

Masu zanga-zanga sun toshe hanyoyi a wasu sassan Colombo babban birnin Sri Lanka bayan gidajen mai da dama sun rasa mai.

Hakan ya jawo cikas matuƙa ga motocin haya inda tuni wasu daga cikin bas-bas ɗin ƙasar suka daina aiki sakamakon ƙarancin mai.

Firaiministan ƙasar Ranil Wickremesinghe a ranar Talata ya bayyana cewa cikin watanni huɗu masu zuwa, ƙasar za ta iya samar da kashi 50 cikin 100 na makamashin da ta saba samarwa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here