Kungiyoyin Direbobin Dakon Man Fetur na Shirin Shiga Yajin Aiki

 

An shiga fargabar yiwuwar wahalar man fetur a Najeriya sakamakon umarni da shugabannin kungiyar direbobin dakon man fetur na PTD da NUPENG suka bai wa mabobinsu na shiga yajin aiki.

Kungiyoyin sun yi barzanar soma yajin aiki ne saboda matsalolin rashin kyawun hanya da tsaronsu, da suka daura alhaki kan gwamnati.

Wannan umarni na kunshe a cikin wata sanarwa da suka fitar jiya Litinin bayan tattaunawar da suka yi a Enugu.

Sanarwar ta yi kira ga mambobin kungiyar su soma shirin kauracewa aiki daga 27 ga watan Satumbar 2021, a shirye-shirye tsunduma yajin-aikin daga 8 ga watan Oktobar 2021, muddin gwamnati ta gaggara biya musu bukatunsu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here