An Kama ‘Yan Majalisar Dokokin Amurka 17 Kan Adawa da Soke ‘Yancin Zubar da Ciki

 

Akalla ‘yan majalisar dokokin Amurka 17 ne aka kama a birnin Washington DC, saboda zanga-zangar adawa da soke ‘yancin zubar da ciki.

Cikin ‘yan majalisar da aka kama sun hadar da Alexandria Ocasio-Cortez, da Rashida Tlaib da Ilhan Omar

An ga ‘yan majalisar na rera wakokin da ke cewa ”A bar mu, mu sakata, mu wala” tare da toshe wasu titunan birnin kafin ‘yan-sanda su yi awon-gaba da su .

A kwanakin baya ne dai Kotun Kolin Amurka ta haramta dokar ‘yancin zubar da ciki a fadin kasar.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here