Dalilin da Yasa Aikin Wutar Lantarkin Mambila Bai Tabbata ba – Garba Shehu

 

Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da ya hana yin aikin wutar Mambila wanda shekaru 40 kenan da ake maganar sa.

Hadimin shugaban kasan Najeriya, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai.

A cewar Shehu, rigima ce ta barke tsakanin dan kwangilar da kuma gwamnati, hakan ya hana banki ba shi bashi.

FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta bayyana kwararan dalilan da suka janyo aikin wutar lantarki na Mambila da ke jahar Taraba ya kasa tabbata tsawon lokaci ba a kammala ba.

Kamar yadda BBC Hausa ta bayyana, har wakilin BBC da kansa ya je wurin da aka bayar don yin tashar wutar lantarkin amma ya ga ba a fara yin aikin ba.

Garba Shehu ya bayyana kwararan dalilan da suka dakatar da aikin

BBC ta samu nasarar tattaunawa da mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu inda ya bayyana dalilin da suka sa aikin bai tabbata ba.

A cewar Garba Shehu:

“Kudin da aka kididdiga za su isa a kammala aikin gabadaya sun kai sama da $4,000,000 wanda aka tsara cewa bashi za a amsa a wurin wani banki dake kasar China zai bayar.”

Shehu ya ce dan kwangilar ya kai karar gwamnatin Najeriya, hakan ya dakatar da aikin

Saidai kamar yadda BBC ta rawaito, Shehu ya ce wata rigima ce ta barke tsakanin gwamnatin Najeriya da dan kwangilar daga nan bankin ya dakatar da bayar da bashin.

Shehu ya bayyana cewa:

“Wani dan kasuwa Leno Adesanya ya yi ikirarin cewa gwamnati ta ba shi kwangilar kawo ma’aikatan da za su yi aikin tashar wutar Mambila.”

“Sai dai da aka bincika an gano cewa ba a gabatar da kwangilar zuwa ofishin tantance kwangiloli bai ba don amincewa da ita.”

“Sakamakon haka ne dan kwangilar ya maka gwamnatin Najeriya kara har wurin kwamitin daidaito na ‘yan kasuwa dake kasar Paris inda ya bukaci gwamnatin Najeriya ta biya shi $200,000,000 sannan ya saki kwangilar, sakamakon haka ya janyo China ta dakatar da bayar da bashin.”

Shehu ya ce aikin zai tabbata ne da zarar dan kwangilar ya janye karar da ya kai gwamnati.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here