Garkuwa da Makwabcinsa: ‘Yan sandan Jahar Katsina Sun Kama Matashin Gurgu

 

Rundunar ‘yan sandan jahar Katsina ta tabbatar da damke wani matashin gurgu mai shekaru 22 a duniya.

Ana zarginsa da yunkurin garkuwa da makwabcinsa inda ya bukaci a biya shi miliyan 2 ko ya sace shi.

Gurgu Haruna Buhari ya amsa laifinsa inda ya ce a duba nakasarsa a yi masa rangwame kuma ya yi nadama.

Kankia, Katsina – Rundunar ‘yan sandan jahar Katsina ta yi ram da wani matashin gurgu mai shekaru 22 mai suna Buhari Haruna daga karamar hukumar Kankia ta jahar.

Ana zargin gurgu Buhari Haruna da barazanar sace wani idan ba a biya shi kudi har naira miliyan biyu ba, LIB suka rawaito.

A yayin damke wanda ake zargin tare da nunawa manema labarai, kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah, ya ce an kama Haruna ne yayin da ya je karbar kudin fansan kuma yayi basaja kamar sunkin biredi a wurin da aka yi za a karba.

Isah ya ce, kamen Haruna ya bayyana cewa, hatta wadanda ba a tsammanin za su yi laifi a yanzu suna amfani da mummunar damar wurin satar jama’a.

A yayin jawabi ga manema labarai bayan kamensa, Haruna bai musanta laifin da ake zarginsa ba.

Ya ce ya kira mutumin da ke makwabcinsa ne tare da yi masa barazanar cewa in har bai biya kudi naira miliyan biyu ba, zai yi garkuwa da shi.

Ya ce ya yi nadamar abinda ya yi, duk da shi mai nakasa ne, ya na rokon yafiya kuma ‘yan sandan su yi masa rangwame, LIB ta rawaito

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here