Cikin Ruwa da Iska: Dalibi Mai Kwazon Zuwa Makaranta ya Samu Tallafi Daga Mutumin Kirki

 

Wani dalibin mai kwazon zuwa makaranta ya sami tallafi daga wasu mutanen kirki a jahar Kano.

A kwanakin baya hoton dalibin ya shahara a kafar Facebook, inda mutane da dama suka nuna son taimaka masa.

A halin yanzu, wani mutum ya yi alkawarin gwangwaje dalibin da kyautuka masu daraja don bashi kwarin gwiwa.

Wani dalibin da labarin jarumtarsa ya yadu a kafafen sada zunumta cikin makwannin nan da suka gabata ya sami tallafin wani mutumin kirki; Ibrahim Sanyi-Sanyi inda da ya ba shi gudummawa ta kudade masu tsoka.

A wani rubutu da Ibrahim ya buga a ranar Asabar, 18 ga Satumba, ya bayyana cewa an gano dalibin mai suna Mallam M. bayan bin diddiginsa, wanda ke zuwa makaranta a kan keke duk tsananin ruwa duk tsananin iska.

Zan ba shi N100,000

Sanyi-Sanyi ya bayyana cewa dalibin yana sakandare ajin SS1 a Makarantar Sakandaren Larabci ta Gwamnati da ke Kura kuma yana tahowa ne daga kauyensu zuwa makaranta kowace rana.

Saboda haka, ya kara da cewa zai ba da gudummawar N100,000, jakar makaranta, da sauran kayan makaranta ga dalibin.

Sanyi-sanyi ya kuma yi kira ga wasu da ke da sha’awar ba da gudummawa ga dalibin da cewa kofa a bude take.

Martanin jama’a kan wannan aiki na Ibrahim Sany-sanyi

Mutane da yawa a kafar Facebook sun yi martani kan wannan kyakkyawan aiki, duba kaga martaninsu.

Salisu Ibrahim Sheriff ya ce:

“Masha Allah. Zan aiko nawa gudummawa ta akwatin sakonk. Allah ya amfanar dashi akan karatunsa. Amin.”

Hussaini Najiddah Umar ya yi martani da cewa:

“Masha Allah abinda Ibrahim yayi abu ne mai kyau. Allah Ya saka masa da alheri. Ina ba da shawarar masu so su taimaka su fara taimakawa yara a unguwanninsu domin akwai irin wadannan yaran da suke kokari wajen neman ilimi, kuma suna bukatar taimakon. Allah ya ba da ikon taimakawa.”

Lawal Umar Faruk yace:

“Oga Sanyi-Sanyi, kai abin koyi ne ga da yawanmu. Allah ya albarkace ka, dukiyar ka da dangin ka. Allah Ya karbi duk abin da kake yi na Ibadat.”

MB Mahmoud yace:

“Wato Sanyi-Sanyi kai ma Allah Ya sanyaya ma.”

Abdulrazak Ibrahim yace:

“Abin mamaki Na halarci wannan makarantar na tsawon shekaru 3. Ta ina zan aiko da gudummawata?”

Hussaini Ubali yace:

“Ikon kafafen sada zumunta kenan, Allah ya saka muku da mafificin alkhairi Mallam.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here