Shugaba Buhari Archives - Arewa Agenda Hausa

Ba a Taba Shugaban Kasa Mara Sanin Makamashin Aiki ba Kamar Buhari – Sanata Hanga
Ba a Taba Shugaban Kasa Mara Sanin Makamashin Aiki ba Kamar Buhari – Sanata Hanga

Shugaba Muhammadu Buhari bai tabuka komai ba kuma bai san makamashin aiki ba kwata-kwata a cewar Sanata Rufai Hanga.

Hanga ya ce bayan kammala wa’adinsa, Shugaba Buhari zai koma gida a Daura ya rika barci hankali kwance domin bai ma san abin da ke faruwa a kasa ba.

Tsohon shugaban na CPC ya ce ba a taba ‘lalataccen’ shugaban kasa irin Buhari ba duk da cewa shi ya na yi wa kansa kirari cewa ya fi dukkan sauran shugabannin Najeriya.

Sanata Rufa’i Hanga, shugaban tsohuwar jam’iyyar CPC na farko, kuma zababben sanata na mazabar Kano Central a karkashin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya gaza.

Yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Daily Politics da Legit.ng Hausa ta yi ido hudu da bidiyon, Hanga ya ce idan Buhari ya kammala mulki zai koma Daura ya yi kwanciyarsa lafiya kalau domin bai san abin da ke faruwa ba.

Buhari ya gaza, ba a taba shugaban kasa mara sanin makamashin aiki kamansa ba, Rufai Hanga

Da ya ke amsa tambaya kan abin da ya ke ganin Buhari zai koma da shi Daura bayan wa’adinsa ya cika, shin zai yi barci hankali kwance, Hanya ya ce:

“Eh, tabbas zai yi barcinsa lafiya saboda bai san abin da ke faruwa ba. Bai san makamashin aiki ba, bai san makamashin aiki ba kuma gaskiya ne.

“Idan mutum zai gaza irin yadda ya yi, ya mayar da kasar inda ta ke a yanzu amma ya cigaba da bugun kirji yana cewa shine shugaba mafi kwazo da aka taba yi a tarihin Najeriya. Abin da ya ke cewa kenan.”

A yayin da ya ke kwatanta Shugaba Buhari da sauran shugabannin Najeriya, Sanata Hanga ya ce Buhari bai tabuka komai ba kuma ya gaza.

Kalamansa:

“Ba abin da ya tabuka, ga gaza baki daya.”

The post Ba a Taba Shugaban Kasa Mara Sanin Makamashin Aiki ba Kamar Buhari – Sanata Hanga appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Sauya Naira: APC ta Goyi Bayan Gwamnoni, ta Bukaci Buhari ya Mutunta Doka
Sauya Naira: APC ta Goyi Bayan Gwamnoni, ta Bukaci Buhari ya Mutunta Doka

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sake kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tsoma baki cikin manufofin tsuke bakin aljihu da ke kawo wa mutane wahala.

Shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu, a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kusan sa’o’i 2 na ganawar sirri da gwamnonin APC, ya ce jam’iyyar za ta tabbatar da hukuncin da kotun koli ta yanke wanda ke rike da ka’idar doka ta tsofaffin takardun kudi.

Adamu ya ce, ya kamata babban bankin Najeriya (CBN) da babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) su mutunta doka ta hanyar tabbatar da hukuncin da kotun koli ta yanke kan musayar kudade.

Ya ce “Mun bukaci babban mai shari’a na tarayya da gwamnan babban bankin Najeriya CBN da su mutunta umarnin kotun koli na wucin gadi wanda har yanzu ake ci gaba da aiki. Cewa taron yana kira ga mai girma shugaban kasa da ya sa baki wajen warware matsalolin da ke jawo wa al’umma wannan babbar matsala da tattalin arziki.”

A halin da ake ciki kuma, a cikin sa’o’i na ganawar sirrin, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya mamaye sakatariyar jam’iyyar.

An boye bayanan zuwan sa gidan Buhari domin ya ki yin jawabi ga manema labarai.

Taron ya samu halartar gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai; Mohammed Bello of Niger, Abdulahi Sule of Nasarawa, Yahaya Bello of Kogi state, Inuwa Yahaya of Gombe state, Bello Matawalle of Zamfara , Mai Mala Buni of Yobe, Abubakar Badaru of Jigawa , Biodun Oyebanji of Ekiti, Simone Lalong of Plateau, Atiku Bagudu na jihar Kebbi, Babajide Sanwolu na jihar Legas, da mataimakan gwamnonin jihar Imo, Placid Njoku, da Mohammed Manir Yakubu na jihar Katsina.

The post Sauya Naira: APC ta Goyi Bayan Gwamnoni, ta Bukaci Buhari ya Mutunta Doka appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Shugaba Buhari ya Nemi Hadaddiyar Daular Larabawa(UAE) ta ‘Dage Dokar Hana Bai wa ‘Yan Najeria Biza
Shugaba Buhari ya Nemi Hadaddiyar Daular Larabawa(UAE) ta ‘Dage Dokar Hana Bai wa ‘Yan Najeria Biza

Shugaba Muhammadu Buhari ya sa baki a dambarwar diflomasiyya da ke tsakanin Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), wadda ta kai ga kasar ta Gabas ta Tsakiya ta dakatar da bai wa ‘yan Najeriya takardar izinin shiga cikinta, wato biza.

A watan Oktoba na shekarar da ta wuce ne 2022 hukumomin Daular suka dauki matakin dakatar da bai wa ‘yan Najeriya, sai wadanda suke da fasfo na manya wato na diflomasiyya kawai.

Duk da cewa hukumomin kasar ta Larabawa ba su bayyana dalilinsu na daukar matakin ba, wasu na danganta shi ga rashin da’a da bin doka da oda da wasu ‘yan Najeriyar da ke zaune ko aiki a can suke yi.

A wata tattaunawa ta waya da Shugaba Buhari ya yi ranar Litinin da takwaransa na Daular Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, wanda kuma shi ne Sarkin Abu Dhabi ya yi maganar neman dage dakatarwar.

Tattaunawar da Shugaba Buharin ya yi da Sheikh Al Nathan na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin shugaban na Najeriya Mallam Garba Shehu, ya fitar yau Talata.

The post Shugaba Buhari ya Nemi Hadaddiyar Daular Larabawa(UAE) ta ‘Dage Dokar Hana Bai wa ‘Yan Najeria Biza appeared first on Arewa Agenda Hausa.

‘Yan Siyasa da ke Shirin Yin Magudi a Zaben 2023 za su sha Mamaki – Igini
‘Yan Siyasa da ke Shirin Yin Magudi a Zaben 2023 za su sha Mamaki –  Igini

Mike Igini, tsohon kwamishinan INEC a jihar Akwa Ibom ya ce yan siyasa da ke shirin yin magudi a zaben 2023 za su sha mamaki.

Igini ya ce hukumar zaben ta samu damar bullo da sabbin na’urori da dabaru don dakile kafafen da yan siyasa ke amfani da su wurin magudi.

Ya ce an samu damar yin wannan canje-canjen ne saboda rattaba hannu kan sabuwar dokar zabe da Shugaba Buhari ya yi a watan Fabrairun wannan shekarar.

Akwa Ibom – Tsohon kwamishinan hukumar zabe INEC, a Jihar Akwa Ibom, Mike Igini, a jiya ya ce yan siyasa da ke fatan za su yi magudi za su sha mamaki a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Igini, wanda ya yi magana a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels ya ce matakan da INEC ta dauka sakamakon amincewa da sabuwar dokar zabe zai bawa masu shirin yin magudi mamaki.

Ya ce zaben 2023 zai kafa tarihi a zabukan Najeriya saboda INEC da bullo da sabbin kayan aiki da mutane ba su sani ba.

A cewarsa:

“Mutane nawa suka sani cewa INEC na bibiya yayin zabe kuma a halin yanzu da muke magana bayan rattaba hannu kan dokar zabe a ranar 25 ga watan Fabrairun wannan shekarar, a ranar 26 INEC ta tafi ofis ta yi canje-canje don dacewa da dokar zaben na yanzu. Yan siyasa da dama za su sha mamaki a 2023.”

An canja sashi na 40 na dokar zaben 2002 da masu magudi ke fakewa da shi, Igini

Igini ya ce an sauya sashi na 40 na dokar zaben 2002 da sashi na 49 da suka ce idan mai jami’in zabe ya gamsu da mai zabe yana iya barin shi ya kada kuri’a, ana amfani da wannan wurin magudi.

Ya ce:

“Sashi na 47 ta bawa INEC damar amfani da na’urar card reader da wasu fasahar da za su tantance mai zabe wanda a baya babu su.

“Yau, mutane su sani idan ka tafi rumfar zabe, babu maganar incident fom, babu maganar zabe na manuwal amma yanzu akwai sabon tsari na ‘bimodal’.”

Wadanda suka tara katin zabe da yawa ba su iya amfani da shi ba

Igini ya kuma cea sashi na 47 ne dalilin da yasa mutanen da suka tara katin zabe na sata ba za su iya amfani da su ba, suna ta zubarwa.

Ya ce:

“Suna zubar da PVC don saboda sashi na 47 ya magance sashi na 49 da ake amfani da shi a baya ana magudi. Karkashin sabon tsarin, duk wadanda suka boye katin PVC na INEC ba za su iya amfani da shi ba.”

The post ‘Yan Siyasa da ke Shirin Yin Magudi a Zaben 2023 za su sha Mamaki – Igini appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Shugaba Buhari Ya Nada Dr Pokop Bupwatda a Matsayin Babban Daraktan Kula da Lafiya na Jami’ar Jos
Shugaba Buhari Ya Nada Dr Pokop Bupwatda a Matsayin Babban Daraktan Kula da Lafiya na Jami’ar Jos

Shugaban kasa Buhari ya nada Dr Pokop Bupwatda a matsayin CMD na asibitin koyarwa na jami’ar Jos

Nadin Bupwatda a matsayin babban daraktan JUTH ya fara aiki daga ranar 30 ga watan Agustan 2022, kamar yadda ma’aikatar kiwon lafiya ta sanar.

Mataimakin sashin labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta tarayya, Mista Ahmadu Chindaya, ya ce nadin na wa’adin shekaru hudu ne.

Abuja – Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Dr Pokop Bupwatda a matsayin babban daraktan kula da lafiya (CMD) na asibitin koyarwa na jami’ar Jos.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mista Ahmadu Chindaya, mataimakin sashin labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta tarayya ya saki a ranar Alhamis, 20 ga watan Oktoba.

Chindaya ya bayyana cewa nadin Bupwatda na kunshe a cikin wata wasika dauke da sa hannun ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, Daily Trust ta rahoto.

An tattaro cewa wasikar ya fara aiki ne daga ranar 30 ga watan Agustan 2022, kuma zai shafe tsawon shekaru hudu.

Da yake gabatar da wasikar ga Bupwatda, ministan ya bukace shi da ya jajirce don kawo ci gaba ga cibiyar don inganta tattalin arziki da kuma sauke nauyin da shugaban kasar ya daura masa.

Ehanire ya ce:

“Ma’aikatar lafiya ma’aikata ce mai muhimmanci ga fannin tattalin arziki, ka jajirce don inganta cibiyar lafiyar da ke karkashin kulawarka, ka dauki alhakin inganta tattalin arzikin da kuma yanayin asibitin koyarwar.”

Jawabin ya nakalto sabon CMD yana godiya ga shugaba Buhari kan ganin cancantarsa da ya yi sannan kuma ya bashi tabbacin cewa ba zai baiwa kasar kunya ba.

Ya dauki alkawarin aiki da duk masu ruwa da tsaki domin inganta asibitin, rahoton The Nation.

The post Shugaba Buhari Ya Nada Dr Pokop Bupwatda a Matsayin Babban Daraktan Kula da Lafiya na Jami’ar Jos appeared first on Arewa Agenda Hausa.

2023: APC ta Kaddamar da Sashen Mata na Tawagar Kamfen Din Tinubu/Shettima
2023: APC ta Kaddamar da Sashen Mata na Tawagar Kamfen Din Tinubu/Shettima

An kaddamar da sashen mata na tawagar kamfen din Tinubu na jam’iyyar APC gabanin zaben 2023 mai zuwa nan kusa.

A halin yanzu ne ake gudanar da kaddamarwar a Banquet Hall dake fadar shugaban kasa a Abuja, uma manyan jiga-jigan APC ne suka samu halarta, ciki har da shugaba Buhari.

Shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ma ya samu halarta, inji rahoton jaridar The Nation.

Sauran da suka halarci taron sun hada da:

1. Dan takarar shugaban kasna APC, Asiwaju Bola Tinubu

2. Mataimakin Tinubu, Sanata Kashim Shettima

3. Shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu

4. Uwar gidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari

5. Mata Tinubu, Sanata Remi Tinubi

6. Matar Shettima, Misis Nana Shettima

7. Shugaban gwamnonin APC, gwmna Simon Lalong.

8. Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo

9. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano

10. Ministar mata Pauline Tallen Shugaban mata ta APC na kasa, Beta Edu

Da sauran kusoshin jam’iyyar APC

Karin bayani na nan tafe…

The post 2023: APC ta Kaddamar da Sashen Mata na Tawagar Kamfen Din Tinubu/Shettima appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Shugaba Buhari ya Miƙa Saƙon Ta’aziyyarsa ga Iyalan Waɗanda Hatsarin Kwale-Kwale ya Rutsa da su a Anambra
Shugaba Buhari ya Miƙa Saƙon Ta’aziyyarsa ga Iyalan Waɗanda Hatsarin Kwale-Kwale ya Rutsa da su a Anambra

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin sake yin duba don inganta matakan kiyaye afkuwar haɗurra a tsarin sufurin ruwa na ƙasar, sakamakon hatsarin wani kwale-kwale da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane a jihar Anambra.

An samu rahotanni masu cin karo da juna kan ainihin yawan waɗanda abin ya rutsa da su a jihar da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Amma wata sanarwa da mai taimaka wa Buhari kan yada labarai ta ce, ana jiran bayanai har yanzu, sai dai hukumimin agaji sun tabbatar d acewa “yawan waɗanda suka mutu ya kai 76.”

Yawancin waɗanda suka rasun dai mata ne da yara da suke ƙoƙarin tsere wa yankinsu da ambaliyar ruwa ta mamaye.

Rahotanni sun ce jirgin wanda ke ɗauke da mutum fiye da 80 ya yi hatsarin ne a yankin Ogbaru a ranar Juma’a.

Jami’ai sun ɗora alhakin jawo hatsarin kan injin jirgin da suka ce ya lalace, sannan kuma jirgin ya yi karo da wata gada.

Shugaba Buhari ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda abin ya rutsa da su, yana mai bayyana hatsarin a matsayin mummuna, sannan ya ƙara da cewa dole ne hukumomi su yi duk abin da ya dace don gano waɗanda har yanzu ba a gansu ba.

Kazalika shugaban ya bai wa hukumomin gwamnati umarnin sake yin nazari kan tsarin tabbatar da tsaro a sufurin jiragen ruwa da kwale-kwale don kare afkuwar irin hakan a gaba.

Ana yawan samun hatsarin kwale-kwale a Najeriya – inda a mafi yawan lokuta ake ɗora alhakin hakan kan ɗaukar mutanen da suka fi ƙarfin jirgin da sauran matsaloli.

The post Shugaba Buhari ya Miƙa Saƙon Ta’aziyyarsa ga Iyalan Waɗanda Hatsarin Kwale-Kwale ya Rutsa da su a Anambra appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Shugaba Buhari Zai Gabatar da Kasafin Kudin 2023 ga ‘Yan Majalisar Tarayya
Shugaba Buhari Zai Gabatar da Kasafin Kudin 2023 ga ‘Yan Majalisar Tarayya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatarwa ‘yan majalisar tarayyar kasar nan kasafin kudin shekarar 2023.

Kamar yadda shugaba majalisar dattawa, Ahmed Lawan ya sanar, hakan zata faru ne a ranar Juma’a wurin karfe 10 na safe.

Shugaba Buhari zai mika kasafin N19.76 tiriliyan ga ‘yan majalisar a zauren wucin-gadi na majalisar wakilan Najeriya.

Abuja – Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudi N19.76 tiriliyan na shekarar 2023 ga majalisar tarayyar kasar nan a ranar Juma’a.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a zaman majalisar na ranar Talata, yace shugaban kasar zai yi wannan gabatarwan da karfe 10 na safe a zauren majalisar wakilai na wucin-gadi.

Karin bayani na nan tafe…

The post Shugaba Buhari Zai Gabatar da Kasafin Kudin 2023 ga ‘Yan Majalisar Tarayya appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Shugaba Buhari ya Taya Mai Jiran Gadon Saurautar Saudiyya, Yarima Bin Salman Murnar Zama Firaiminista
Shugaba Buhari ya Taya Mai Jiran Gadon Saurautar Saudiyya, Yarima Bin Salman Murnar Zama Firaiminista

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Yarima Mohammed Bin Salman, mai jiran gadon sarautar Saudiyya, murnar zama firaiministan kasar.

Shugaban ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana d yawunsa, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Laraba.

“Shugaba Buhari ya ce gwamnati da al’ummar Najeriya suna sa ran kara aiki tare da shi domin kyautata dangantakar da ke tsakaninsu,” in ji sanarwar.

Kazalika shugaban Najeriya ya yi addu’a ga Sarki Salman Bin Abdulaziz domin samun karin lafiya.

The post Shugaba Buhari ya Taya Mai Jiran Gadon Saurautar Saudiyya, Yarima Bin Salman Murnar Zama Firaiminista appeared first on Arewa Agenda Hausa.

Shugaba Buhari ya Kai Ziyara Jihar Imo
Shugaba Buhari ya Kai Ziyara Jihar Imo

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Jihar Imo domin kaddamar da wasu ayyukan raya kasa.

Ayyukan da shugaban zai kaddamar sun hada da na hanyoyin mota kamar ta Orlu zuwa Okigwe da kuma ta Orlu zuwa Owerri.

Gwamnan Jihar Hope Uzodinma ne ya tarbi shugaban a filin jirgin saman birnin Owerri.

The post Shugaba Buhari ya Kai Ziyara Jihar Imo appeared first on Arewa Agenda Hausa.