‘Yan Siyasa da ke Shirin Yin Magudi a Zaben 2023 za su sha Mamaki –  Igini

 

Mike Igini, tsohon kwamishinan INEC a jihar Akwa Ibom ya ce yan siyasa da ke shirin yin magudi a zaben 2023 za su sha mamaki.

Igini ya ce hukumar zaben ta samu damar bullo da sabbin na’urori da dabaru don dakile kafafen da yan siyasa ke amfani da su wurin magudi.

Ya ce an samu damar yin wannan canje-canjen ne saboda rattaba hannu kan sabuwar dokar zabe da Shugaba Buhari ya yi a watan Fabrairun wannan shekarar.

Akwa Ibom – Tsohon kwamishinan hukumar zabe INEC, a Jihar Akwa Ibom, Mike Igini, a jiya ya ce yan siyasa da ke fatan za su yi magudi za su sha mamaki a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Igini, wanda ya yi magana a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels ya ce matakan da INEC ta dauka sakamakon amincewa da sabuwar dokar zabe zai bawa masu shirin yin magudi mamaki.

Ya ce zaben 2023 zai kafa tarihi a zabukan Najeriya saboda INEC da bullo da sabbin kayan aiki da mutane ba su sani ba.

A cewarsa:

“Mutane nawa suka sani cewa INEC na bibiya yayin zabe kuma a halin yanzu da muke magana bayan rattaba hannu kan dokar zabe a ranar 25 ga watan Fabrairun wannan shekarar, a ranar 26 INEC ta tafi ofis ta yi canje-canje don dacewa da dokar zaben na yanzu. Yan siyasa da dama za su sha mamaki a 2023.”

An canja sashi na 40 na dokar zaben 2002 da masu magudi ke fakewa da shi, Igini

Igini ya ce an sauya sashi na 40 na dokar zaben 2002 da sashi na 49 da suka ce idan mai jami’in zabe ya gamsu da mai zabe yana iya barin shi ya kada kuri’a, ana amfani da wannan wurin magudi.

Ya ce:

“Sashi na 47 ta bawa INEC damar amfani da na’urar card reader da wasu fasahar da za su tantance mai zabe wanda a baya babu su.

“Yau, mutane su sani idan ka tafi rumfar zabe, babu maganar incident fom, babu maganar zabe na manuwal amma yanzu akwai sabon tsari na ‘bimodal’.”

Wadanda suka tara katin zabe da yawa ba su iya amfani da shi ba

Igini ya kuma cea sashi na 47 ne dalilin da yasa mutanen da suka tara katin zabe na sata ba za su iya amfani da su ba, suna ta zubarwa.

Ya ce:

“Suna zubar da PVC don saboda sashi na 47 ya magance sashi na 49 da ake amfani da shi a baya ana magudi. Karkashin sabon tsarin, duk wadanda suka boye katin PVC na INEC ba za su iya amfani da shi ba.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here