Shugaba Buhari ya Nemi Hadaddiyar Daular Larabawa(UAE) ta ‘Dage Dokar Hana Bai wa ‘Yan Najeria Biza

 

Shugaba Muhammadu Buhari ya sa baki a dambarwar diflomasiyya da ke tsakanin Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), wadda ta kai ga kasar ta Gabas ta Tsakiya ta dakatar da bai wa ‘yan Najeriya takardar izinin shiga cikinta, wato biza.

A watan Oktoba na shekarar da ta wuce ne 2022 hukumomin Daular suka dauki matakin dakatar da bai wa ‘yan Najeriya, sai wadanda suke da fasfo na manya wato na diflomasiyya kawai.

Duk da cewa hukumomin kasar ta Larabawa ba su bayyana dalilinsu na daukar matakin ba, wasu na danganta shi ga rashin da’a da bin doka da oda da wasu ‘yan Najeriyar da ke zaune ko aiki a can suke yi.

A wata tattaunawa ta waya da Shugaba Buhari ya yi ranar Litinin da takwaransa na Daular Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, wanda kuma shi ne Sarkin Abu Dhabi ya yi maganar neman dage dakatarwar.

Tattaunawar da Shugaba Buharin ya yi da Sheikh Al Nathan na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin shugaban na Najeriya Mallam Garba Shehu, ya fitar yau Talata.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here