Jami’an Haraji a Indiya Sun Kai Samame a ofishohin BBC da ke Kasar

 

Jami’an haraji a Indiya sun kai samame a ofishohin BBC da ke Delhi da Mumbai inda suka ce sun zo domin tantance takardu harajin ma’aikata.

Sun hana ma’aikata fita daga wurin aikinsu kuma rahotani sun ce sun kwace wayoyi.

BBC ta ce tana bayar da cikakken hadin kai ga mahukuntan kasar.

Samamen na zuwa makonni kadan bayan da BBC ta yadda wani shiri a kan rawar da firaministan Indiya Narendra Modi ya taka a tashin hankali mai nasaba da addini da ya faru shekaru ashirin da suka gabata.

Sai dai Sakatare Janar na jam’iyyar hammaya ta Congress ya ce mahukunatan Indiya sun rasa na yi ne shi ya sa suka kai samamen.

A dayan bangaren kakakin jam’iyyar BJP mai mulki ya bayyana BBC a matsayin kungiyar da ta fi aikata rashawa a duniya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here