Shugaba Buhari Ya Nada Dr Pokop Bupwatda a Matsayin Babban Daraktan Kula da Lafiya na Jami’ar Jos

 

Shugaban kasa Buhari ya nada Dr Pokop Bupwatda a matsayin CMD na asibitin koyarwa na jami’ar Jos

Nadin Bupwatda a matsayin babban daraktan JUTH ya fara aiki daga ranar 30 ga watan Agustan 2022, kamar yadda ma’aikatar kiwon lafiya ta sanar.

Mataimakin sashin labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta tarayya, Mista Ahmadu Chindaya, ya ce nadin na wa’adin shekaru hudu ne.

Abuja – Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Dr Pokop Bupwatda a matsayin babban daraktan kula da lafiya (CMD) na asibitin koyarwa na jami’ar Jos.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mista Ahmadu Chindaya, mataimakin sashin labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta tarayya ya saki a ranar Alhamis, 20 ga watan Oktoba.

Chindaya ya bayyana cewa nadin Bupwatda na kunshe a cikin wata wasika dauke da sa hannun ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, Daily Trust ta rahoto.

An tattaro cewa wasikar ya fara aiki ne daga ranar 30 ga watan Agustan 2022, kuma zai shafe tsawon shekaru hudu.

Da yake gabatar da wasikar ga Bupwatda, ministan ya bukace shi da ya jajirce don kawo ci gaba ga cibiyar don inganta tattalin arziki da kuma sauke nauyin da shugaban kasar ya daura masa.

Ehanire ya ce:

“Ma’aikatar lafiya ma’aikata ce mai muhimmanci ga fannin tattalin arziki, ka jajirce don inganta cibiyar lafiyar da ke karkashin kulawarka, ka dauki alhakin inganta tattalin arzikin da kuma yanayin asibitin koyarwar.”

Jawabin ya nakalto sabon CMD yana godiya ga shugaba Buhari kan ganin cancantarsa da ya yi sannan kuma ya bashi tabbacin cewa ba zai baiwa kasar kunya ba.

Ya dauki alkawarin aiki da duk masu ruwa da tsaki domin inganta asibitin, rahoton The Nation.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here