Mutane 5 Sun Rasa Rayukansu Yayin Zanga-Zanga a Chadi

 

Akalla mutum biyar ne suka mutu yayin zanga-zanga a Chadi, inda wasu ‘yan kasar ke bukatar Shugaba Mahamat Idris Deby ya sauka kamar yadda ya yi alkawari.

An gudanar da gangami a babban birnin kasar N’Djamena da wasu garuruwan.

Sai dai rahotanni sun ce ‘yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wurin tarwatsa masu boren.

An kuma samu rahotanni da ke cewa an cinnawa wani bangare na gidan sabon Firaiminista Saleh Kebzabo wuta.

Shugaba Mahamat Deby ya hau mulki ne watanni 18 bayan mutuwar mahaifinsa, kuma a wannan watan ne ya yi alkawarin sauka don a gudanar da zabe.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here