Saudiyya za ta Kera Tare da Fitar da Motoci Masu Amfani da Wutar Lantarki Sama da 150,000

 

Ministan Sadarwa da Fasahar Bayanai na Saudiyya, Injiniya Abdullah Al-Swaha ya ce kasar za ta kera tare da fitar da motoci masu amfani da wutar lantarki sama da 150,000 a 2026.Babban kamfanin kera motoci masu amfani da lantarki na Amurka Lucid Motors Company na son ya rika samar da motocin 150,000 a Saudiyyar a duk shekara, daga shekara ta 2027, kamar yadda ministan ya bayyana jiya Laraba.Tun da farko shugaban kamfanin Peter Rawlinson ya ce nan da wani dan lokaci suke son fara aikin kafa masana’antar a Saudi Arabia.

Ya ce, “Muna son fara kera motocin a 2025 kuma za mu kara yawansu a 2026 da 2027 mu kai motoci 150,000 a duk shekara” Ministan zuba jari na Saudi Arabia, Khalid Al-Falih ya ce kamfanin ya fara gina ma’aikatarsa a kasar a watan Mayu na wannan shekara.

Ma’aikatar za ta kasance daya daga ciki guda uku na kamfanin mai cibiya a California, wanda Saudiyya za ta mallaki kashi 61 na hannun jarinsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here