2015:Buhari ya Dauki Alwashin Tabbatar da Tsaro da Kare Rayuka
Ayyukan ta’addanci na kungiyar Boko Haram sun fara bayyana ne tun cikin shekarar 2009 a jihar Borno.
Har yanzu, bayan fiye da shekaru 10, kungiyar Boko Haram ba ta daina kai hare-hare tare da kami’an tsaro da fararen hula ba.
Buhari ya samu nasarar lashe zaben shekarar 2015 bisa tsammanin da jama’a a ke yi a kan cewa zai kawo karshen matsalar.
A yayin da jama’a a Najeriya, musamman mazauna yankin arewa, ke juyayin kisan manoma 43 da mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago a jihar Borno, Legit.ng ta yi waiwaye adon tafiya a kan wani tsohon faifan bidiyo.
Read Also:
Matsalar Boko ta dade ta na ci wa gwamnatin Najeriya tuwo a kwarya, kusan duk wani yunkuri na kawo karshen matsalar ya ci tura.
Gaza kawo karshen matsalar Boko Haram na daga cikin dalilan da suka jawo faduwar gwamnatin PDP a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan.
A lokacin da ya ke yakin neman zabe, shugaba Buhari ya sha daukan alkawarin cewa zai tabbatar da tsaro tare da kare dukkan ‘yan kasa daga wata barazanar tsaro.
A wata hira da aka yi da shi, wacce Channels TV ta nada kafin zaben shekarar 2015, shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ce ta ke daukan nauyin Boko Haram tunda ta gaza kawo karshen kungiyar.
“gwamnatin tarayya ce, da kanta, babbar mai daukar nauyin Boko Haram, saboda tana da dukkan ikon dakatar da mulkin mulikiyya da duk wani rikicin na siyasa,” kamar yadda Buhari ya bayyana a cikin bidiyon.