2023: Ubangiji ne Kawai Zai Iya Cewa ga Shugaban Kasar Najeriya – Rotimi Ameachi
An yi wa Ministan sufurin kasa, Rotimi Ameachi, tambaya kan siyasar 2023.
Rotimi Ameachi yace bai san wanda zai zama shugaban Najeriya na gaba ba.
Jigon na APC ya ce aikin da ke gabansa shi ne sauke nauyin kujerar Minista.
Ministan sufurin na kasa, Rotimi Chibukwe Amaechi, ya yi watsi da rade-radin da ake yi na cewa ana masa hangen zama shugaban Najeriya a 2023.
An yi hira da mai girma Ministan a gidan talabijin na Channels TV, inda ya bayyana cewa Ubangiji ne kadai ya san wanda zai zama shugaban Najeriya.
A cewar tsohon gwamnan kuma jagoran jam’iyyar APC a yau, aikin da ke gabansa shi ne sauke nauyin kujerar Minista ba harin takarar shugaban kasa ba.
Read Also:
“Har yanzu ni Ministan sufuri ne, kuma Ubangiji ne kawai zai iya cewa ga shugaban kasar Najeriya a 2023.”
Rotimi Amaechi ya yi gwamna sau biyu a jihar Ribas, kuma ya taba rike shugaban majalisar dokoki na Ribas, ya rike mukaman ne tsakanin 1999 da 2015.
Ko da yanzu akwai sauran lokaci mai tsawo kafin zaben 2023, mutane su na cigaba da tattauna yadda siyasar kasar za ta kasance a zaben mai zuwa.
A daidai lokacin da wa su ke ganin cewa ya kamata mulki ya koma yankin Kudancin kasar, akwai ‘yan siyasan Arewa da ake zargin su na harin takara.
Daga cikin wadanda ake zargin za su nemi kujerar shugaban kasa a 2023 akwai:
Atiku Abubakar
Bola Ahmed Tinubu
Rotimi Amaechi
Kayode Fayemi
Rabiu Musa Kwankwaso
Aminu Waziri Tambuwal
Donald Duke Owelle
Rochas Okorocha
Ahmed Sani Yarima
Yahaya Bello
David Umahi Bala