2023: Sanata Abu Ibrahim ya Nuna Goyan Banyansa Akan Bola Tinubu a Matsayin Shugaban Kasa
Wani tsohon sanatan jahar Katsina ya bayyana ra’ayinsa game da bai wa Bola Tinubu shugabanci a 2023.
Sanatan ya bayyana cewa, a karkashin mulkin Bola Tinubu ne kadai Najeriya za ta zauna lafiya.
Hakazalika wani jigo a gwamnatin jahar Neja shima ya goyi bayan maganar tsohon sanatan.
Wani tsohon mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijai kuma jigo a jam’iyyar APC, Sanata Abu Ibrahim, ya ce Najeriya za ta zauna lafiya a karkashin Asiwaju Bola Tinubu, idan aka zabe shi a matsayin Shugaban kasa a zaben 2023.
Tsohon sanatan dan asalin jahar Katsina yayi wannan maganan ne a karshen mako a Abuja yayin kaddamar da kungiyar nuna goyon bayan Bola Tinubu (BTSO), The Nation ta ruwaito.
Ya nuna goyon baya ga masu tallata shugabancin Bola Tinubu a 2023, yana mai cewa ya san Shugaban na APC na Kasa sama da shekaru 20.
Ibrahim ya bayyana Asiwaju Tinubu a matsayin dan Najeriyar da ke da manufa kuma babban jagora wanda ke da sha’awar gano kwarewa da kwazon matasa masu tasowa ya jagorance su zuwa mukamai.
Read Also:
“Na san Asiwaju Tinubu sosai. Mun kasance abokai fiye da shekaru 20. Shi mutum ne mai himma da kwazo. Shi ne mai gina hadin kai kuma ginshikin hadin kan Najeriya. Ina ganin Najeriya za ta zauna lafiya a hannunsa.”
Har ila yau, Sakataren Gwamnatin Jahar Neja (SSG), Farfesa Mohammed Kuta Yahaya, ya jinjina wa Shugaban Jam’iyyar ta APC na kasa saboda kwarewa a jagoranci. Ya lura cewa tsohon gwamnan na Legas ya jagoranci ‘yan Najeriya da yawa a mukamai daban-daban na shugabanci a fadin kasar.
Yahaya, wanda shi ne Shugaban bikin rantsarwar, ya jaddada cewa babu wani shugaba a Najeriya da ya ke da kwazo kamar na Asiwaju Tinubu.
“Shin akwai wani dan Najeriya a fagen siyasa ko kuma harkar kasuwanci da ya jagoranci shugabanni masu tasowa kamar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu? Yahaya ya ce “Ya kamata mu kirkiro wani Bola Ahmed Tinubu a kowane shiyya na shiyyoyi shida na siyasar kasar nan, kuma za ku ga ba za a samu talauci da rashawa a Najeriya ba.”
Mai gabatar da taron kuma Kodinetan kungiyar na BTSO, Abubakar Kuso ya ce takarar kujerar Shugaban kasa a zaben 2023 na bukatar mutum mai hangen nesa kamar Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa wato Tinubu. “Ni saurayi ne kuma mai matukar karfafa ra’ayin ‘Ba a kankanta a shugabanci.
Amma Najeriya na bukatar shugaba kamar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Muna bukatar shi ya jagoranci matasa masu tasowa don ya ba mu damar karbar ragamar shugabancin kasar, ” in ji Kuso.